Yau Litinin, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin, Lin Jian, ya gudanar da taron manema labarai na yau da kullum. A gun taron, wani dan jarida ya yi tambaya game da barazanar da sakataren baitul-malin Amurka ya yi na sanya takunkumi ga kasashen dake kasuwanci ko mu’ammala da Iran.
Game da hakan, Lin Jian ya ce, takunkumi da matsin lamba ba za su taimaka wajen magance matsala ba, sai dai su kara tayar da hankali, kuma ba su dace da muradun bangarorin biyu ba. Ya ce Sin za ta sa ido sosai kan abubuwan da suke faruwa kuma ta dauki matakan da suka dace don kare halaltattun hakkoki da muradunta.
Dangane da batancin da wasu jami’an Amurka suka yi wa kamfanonin fasahar zamani na Sin a shafukan sada zumunta kwanan nan, Lin Jian ya bayyana cewa kalaman sun gurbata gaskiya, kuma sun nuna cin zarafi a fannin fasaha da kuma kawo barazana.
Game da ziyarar ministan harkokin wajen Sin a Indonesia da halartar taro na farko game da tsarin tattaunawa bisa manyan tsare-tsare tsakanin Sin da Indonesia, Lin Jian ya ce, a matsayinsu na manyan kasashe masu tasowa, karfafa hadin gwiwarsu bisa tsare-tsare, yana da ma’ana mai muhimmanci da zurfi da ta wuce bangarorin biyu.
Bugu da kari, ma’aikatar harkokin wajen Sin ta fitar da sanarwa cewa za a gudanar da taron wakilai na musamman karo na 25 kan batun iyakokin kasashen Sin da Indiya a birnin Beijing a ranar 25 ga wata.(Safiyah Ma)














