‘Yan bindiga sun saki wani bidiyon mutanen mutanen da suka sace a wani masallaci a Jihar Neja.
Bidiyon ya bayyana kwanaki biyu bayan da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da sama da masallata 600 yayin sallar Juma’a a wani masallaci da ke ƙauyen Dekera a Jihar Neja.
Mazauna yankin sun ce ‘yan bindigar sun kai hare-hare a lokaci guda kan wasu al’ummomi tare da yin awon gaba da mutane da dama.
A cikin bidiyon, wanda ya yaɗu a Facebook da WhatsApp, an ga wasu yara suna kuka yayin da wasu mahara ɗauke da makamai a kewaye da su.
Ɗaya daga cikin ‘yan bindigar, wanda ke magana da harshen Hausa, ya yi magana kai tsaye da iyalan waɗanda aka sace, inda ya buƙaci su yi ƙoƙarin gano ‘yan uwansu da ke cikin waɗanda suke tsare da su.
“Ga mutanenku nan,” in ji ɗan bindigar.
Lamarin na zuwa ne yayin da Nijeriya ke shirin gudanar da babban zaɓen shekarar 2027.














