A yau Jumma’a, ma’aikatar tsaron kasa ta Sin ta bukaci Japan da ta yi waiwaye kan zaluncinta na yaki a lokacin yakin duniya, tare da dakatar da abin da aka kira da ayyuka masu hadari na sake farfado da karfin soji, gabanin cika shekaru 81 da sanar da mika wuyan Japan ba tare da gindaya wani sharadi ba a yakin duniya na biyu.
Mai magana da yawun ma’aikatar tsaron, Chen Xi, ya bayyana hakan yayin da aka nemi ya yi tsokaci kan bukatar Japan ta ware kasafin kudin tsaron kasa mai tsoka a shekarar 2027. Bukatar da aka tsara gabatarwa, ta kai kimanin tiriliyan 8.9 na kudin kasar Yen (watau kusan dala biliyan 55.9), adadin da zai sake kafa sabon tarihi a matsayin mafi yawan kudin da aka taba warewa.
Chen ya bayyana cewa, hakika Japan ta gaza koyon darasi daga tarihi bayan cinta da yaki da aka yi a yakin duniya na biyu. Kuma ta jima tana barin gungun masu ra’ayin rikau dinta suna kokarin boye gaskiya ko musanta miyagun laifukanta na kai hare-haren zalunci, tare da neman duk wata hanya ta keta kundin tsarin mulkinta na son zaman lafiya da kuma manufar mayar da hankali ga kare kai kawai. Sannan ta yi kokarin kalubalantar tsarin duniya da aka kafa bayan yakin. Sakamakon haka, Japan ta zama barazana ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin. (Abdulrazaq Yahuza Jere)













