Gwamnatin Jihar Kaduna ta fara rabon takin zamani kyauta ga ƙananan manoma 150,000 a faɗin jihar, a wani mataki da ta ce zai taimaka wajen ƙara yawan amfanin gona, inganta rayuwar manoma da kuma ƙarfafa samar da isasshen abinci.
An gudanar da rabon takin ne ta cibiyoyin karɓar taki guda 69 da aka kafa a faɗin ƙananan hukumomi 23 na jihar, inda kowace ƙaramar hukuma ke da cibiyoyi uku.
Da yake duba yadda ake rabon takin a cibiyar karɓar taki ta Gadan Gayan da ke ƙaramar hukumar Igabi, Kwamishinan aikin gona na jihar, Malam Murtala Dabo, ya ce an riga an kai takin zuwa rumbunan ajiya daban-daban a faɗin jihar.
Ya ce an kuma tura jami’an tsaro da na fasahar sadarwa domin tabbatar da cewa rabon takin ya kasance cikin gaskiya, adalci da sahihanci.
A cewarsa, kowane manomin da aka tantance zai samu buhunan taki guda biyu ta hanyar amfani da tsarin zamani na tantance masu cin gajiyar shirin.
“Za a tura wa kowanne wanda aka tantance saƙo da zai sanar da shi, inda zai karɓi buhunan taki guda biyu da gwamna ya samar domin daminar shekarar 2026.
“Za a tantance takardar karɓarsa, sannan a ɗauki bayanansa da hotonsa kafin a miƙa masa takin,” in ji shi.
Kwamishinan ya gargaɗi waɗanda suka amfana da shirin da su yi amfani da takin kai tsaye a gonakinsu, yana mai jan kunnen da su guji karkatar da shi ko sayar da shi.
Ya ce takin ba na sayarwa ba ne, kuma duk wanda aka kama yana sayar da shi zai fuskanci hukunci.
Shi ma kwamishinan yaɗa labarai da al’adu na jihar, Malam Ahmed Maiyaki, ya bayyana cewa rabon takin na daga cikin matakan da Gwamna Uba Sani ke ɗauka wajen ƙara zuba jari a ɓangaren aikin gona.
Ɗaya daga cikin manoman da suka amfana da shirin daga Dandami, Unguwar Birnin Yero da ke ƙaramar hukumar Igabi, AbdulHamid Muhammad, ya yaba wa gwamnatin jihar bisa tallafin.













