Firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya ce a shirye kasarsa take ta hada hannu da MDD wajen shawo kan tarin kalubalen da duniya ke fuskanta.
Li Keqiang ya bayyana haka ne jiya Juma’a, lokacin da yake ganawa da shugaban babban zauren MDD na 77, Csaba Korosi.
A cewar firaministan, a shirye Sin take ta hada hannu da dukkan bangarori wajen daukaka muradu da ka’idojin MDD, da dokokin da harkokin kasa da kasa, da inganta dunkulewar tattalin arzikin duniya da huldar bangarori daban-daban da tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya.
Har ila yau, ya ce a matsayinta na daya daga cikin mambobin da suka kafa MDD kuma mambar dindindin a kwamitin sulhu na majalisar, kasar Sin za ta ci gaba da bayar da goyon baya da shiga ana damuwa da ita cikin ayyukan majalisar da karfafa hadin gwiwa a bangarori kamar na ci gaba mai dorewa da sauyin yanayi da albarkatun ruwa da yi wa MDD garambawul.
Da yake jawabi, Csaba Korosi ya ce, MDD na fatan zurfafa abota da karfafa hadin gwiwa da Sin domin hada hannu wajen shawo kan matsalolin siyasa da tattalin arziki da muhalli da jin kai da duniya ke fama da su, tare kuma da cimma ci gaba mai dorewa da inganta samun sauye-sauye bisa dabaru na kimiyyance. (Mai fassarawa: Fa’iza Mustapha)