Dakarun Sojojin ‘Operation Fansan Yamma’ (OPFY) sun dakile yunƙurin yin garkuwa da mutane sau biyu a jere a wurare daban-daban a Jihar Zamfara, tare da ceto mutane 10.
Jami’in Yaɗa Labarai na Rundunar OPFY, Sashi na Biyu, Laftanar Kanal Aliyu Danja, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa a ranar Litinin.
Danja ya ce a ranar 27 ga Satumba, dakarun da ke aiki a Ƙaramar Hukumar Maru sun samu bayanan cewa ‘yan ta’adda sun yi garkuwa da wasu mazauna ƙauyen Kade Daba da ke gundumar Kanoma.
Ya ce dakarun sun gaggauta isa yankin tare da fafatawa da ‘yan ta’addan, inda suka ceto mutane huɗu.
A wani lamari na daban da ya faru a wannan rana, Danja ya ce dakarun da ke gudanar da sintiri a kan hanyar Tsafe zuwa Funtua a Ƙaramar Hukumar Tsafe sun ji karar harbe-harbe.
A cewarsa, dakarun sun nufi wurin inda suka tarar da ‘yan ta’addan na ja da baya ta wani tudu da ke kusa da yankin.
Ya ce dakarun sun kai musu farmaki, lamarin da ya tilasta wa ‘yan ta’addan tserewa daga yankin.
Danja ya ce kafin isowar dakarun, ‘yan ta’addan sun ƙona wata motar Sharon yayin da suke ƙoƙarin yin garkuwa da mutanen da ke cikinta.
Ya ce mutanen da ke cikin motar sun samu damar tserewa kafin wutar ta cinye motar gaba ɗaya.
Ya ƙara da cewa dakarun sun kuma ceto mutane shida da ke cikin wata mota da ta ƙwace bayan jin karar harbe-harben.














