Dakarun rundunar haɗin gwiwa ta Operation Fansan Yamma sun samu nasarar ceto mutum 14 da aka yi garkuwa da su, tare da cafke wasu mutum uku da ake zargi da kai wa ƴan ta’adda kayan aiki da maƙudan kuɗaɗe a Jihar Katsina.
Jami’in yaɗa labarai na rundunar, Laftanar Kanar Aliyu Danja, ne ya bayyana hakan a ranar Asabar, inda ya ce mutanen da aka ceto sun haɗa da maza 12 da mata biyu, waɗanda aka sace daga ƙauyukan Anguwan Miko da Tafoki da ke Ƙaramar Hukumar Faskari.
Danja ya bayyana cewa a ranar 24 ga Satumba, 2026, dakarun shashi na 2 sun tare wasu mutum uku a kan babur a yankin Faskari, inda binciken farko ya nuna cewa suna ɗauke da kuɗi naira miliyan 2.7 da ake zargin na fansa ne, tare da wayoyin salula guda uku da nufin miƙa su ga wani babban ɗan ta’adda.
Haka kuma, a ranar 25 ga Satumba, dakarun sun yi kwanton-ɓauna bayan samun sahihan bayanan sirri kan motsin ƴan bindiga a yankin na Faskari, inda suka buɗe musu wuta tare da tilasta musu tserewa, sannan aka ƙwace bindiga ƙirar AK-47 guda ɗaya, alburusai 30, da kuma babur guda ɗaya.
A wannan rana ce kuma dakarun da ke aikin sintiri suka yi nasarar kuɓutar da mutum 14 ɗin, yayin da sanarwar ta tabbatar da cewa waɗanda ake zargin da kayayyakin da aka ƙwace na can a hannun rundunar sojin domin ci gaba da gudanar da bincike mai zurfi.














