ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Sojoji Sun Ceto Mutum 10 A Sakkwato, Kebbi Da Zamfara

by Sadiq
3 weeks ago

Sojojin rundunar haɗin gwiwa ta Operation FANSAN YAMMA sun ceto mutane 10 a wasu hare-hare daban-daban da suka gudanar a jihohin Sakkwato, Kebbi da Zamfara.

Rundunar sojin ta ce an gudanar da ayyukan ne tsakanin ranar 18 zuwa 19 ga watan Agustan 2026.

A Jihar Sakkwato, sojoji sun fafata da ‘yan ta’adda da suka yi musu kwanton ɓauna a ƙaramar hukumar Isa.

ADVERTISEMENT

An ceto mutane biyar tare da sada su da iyalansu.

Haka kuma, an ƙwato babura biyu da ‘yan ta’addan suka bari yayin da suke tserewa.

LABARAI MASU NASABA

’Yan Takarar ADC A Arewa Maso Yamma Sun Yi Alƙawarin Biyan N110,000 A Matsayin Mafi Ƙarancin Albashi

Hormuz: Iran Ta Kai Muggan Hare-hare Kan Sansanin Amurka A Jordan

A Jihar Kebbi, sojoji sun ceto mutane uku da aka yi garkuwa da su a ƙaramar hukumar Danko Wasagu.

A Jihar Zamfara kuma, sojoji sun kai ɗauki bayan samun rahoton ayyukan ‘yan ta’adda a ƙaramar hukumar Tsafe.

Hakan ya tilasta wa ‘yan ta’addan tserewa tare da barin mutane biyu da suka sace.

Mutanen biyu sun samu raunukan harbin bindiga, inda aka garzaya da su asibiti domin samun kulawar gaggawa.

Rundunar sojin ta ce ana ci gaba da ƙoƙarin gano ‘yan ta’addan da suka tsere, tare da roƙon jama’a su riƙa bai wa jami’an tsaro sahihan bayanai domin taimaka wa ayyukan tsaro.

MASU ALAKA

’Yan Takarar ADC A Arewa Maso Yamma Sun Yi Alƙawarin Biyan N110,000 A Matsayin Mafi Ƙarancin Albashi
Manyan Labarai

’Yan Takarar ADC A Arewa Maso Yamma Sun Yi Alƙawarin Biyan N110,000 A Matsayin Mafi Ƙarancin Albashi

September 9, 2026
Iran Ta Musanta Ikirarin Trump Tare Da Zafafa Hare-hare Kan Isra’ila
Manyan Labarai

Hormuz: Iran Ta Kai Muggan Hare-hare Kan Sansanin Amurka A Jordan

September 9, 2026
Sojoji
Manyan Labarai

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Next Post
Ba Mu Taba Biyan Kudin Fansa Ba Kuma Ba Za Mu Biya Ba – Kwamishinan Katsina

Ba Mu Taba Biyan Kudin Fansa Ba Kuma Ba Za Mu Biya Ba – Kwamishinan Katsina

LABARAI MASU NASABA

’Yan Takarar ADC A Arewa Maso Yamma Sun Yi Alƙawarin Biyan N110,000 A Matsayin Mafi Ƙarancin Albashi

’Yan Takarar ADC A Arewa Maso Yamma Sun Yi Alƙawarin Biyan N110,000 A Matsayin Mafi Ƙarancin Albashi

September 9, 2026
Yadda Jami’an ‘Yansanda Suka Yi Garkuwa Da Wani Mazaunin Abuja, Sun Kwashe Fiye Da Naira Miliyan 20 A Asusunsa

Na Sayar Da ’Ya’yana, Na Sace Wasu 19 – Wata Da Ake Zargi Da Safarar Yara

September 9, 2026
Iran Ta Musanta Ikirarin Trump Tare Da Zafafa Hare-hare Kan Isra’ila

Hormuz: Iran Ta Kai Muggan Hare-hare Kan Sansanin Amurka A Jordan

September 9, 2026
ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

September 9, 2026
Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.