ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Monday, November 2, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Sojoji Sun Kuɓutar Da Mutane 11 Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Kebbi

by Abubakar Sulaiman
4 hours ago
Kebbi

Sojojin Nijeriya ƙarƙashin rundunar Operation Fansan Yamma sun kuɓutar da mutane 11 da aka yi garkuwa da su a wasu hare-hare biyu da suka gudanar a Ƙaramar Hukumar Danko-Wasagu ta Jihar Kebbi. An gudanar da ayyukan ne tsakanin ranakun 30 da 31 ga Oktoba, 2026, bayan samun rahotannin hare-haren ƴan bindiga a yankin.

Kakakin rundunar sojojin, Laftanar Kanal Osoba Olaniyi, ya bayyana cewa aikin farko ya biyo bayan kiran gaggawa kan wasu mahara da suka tare hanyar zuwa garin Ribah, tare da ƙoƙarin shiga cikin garin. Sojojin da aka tura yankin sun gano cewa an yi garkuwa da wasu mazauna yankin, yayin da aka ga wasu babura da aka bari a wurin.

Ya ce dakarun sun bi sawun maharan, inda aka yi musayar wuta da su, lamarin da ya tilasta musu tserewa tare da barin mutum bakwai da suka yi garkuwa da su. An bayyana sunayen waɗanda aka kuɓutar da su da Sa’adu Bala, Dantani Yahyi, da Nura Musa, da Nasiru Muhammad, da Abdulakeem Abubakar, da Abdulahi Maikudi da Zaki Gom. Rundunar ta ce an mayar da su ga iyalansu.

ADVERTISEMENT

A wani sumamen na daban a yankin Wasagu, sojojin da ke sintiri sun fuskanci harin wasu da ake zargin ƴan ta’adda ne. Dakarun sun mayar da martani tare da fatattakar maharan, waɗanda suka gudu suka bar mutum huɗu da aka yi garkuwa da su a gonakinsu a ƙauyen Wasagu. Waɗanda aka kuɓutar su ne Lawali Ali, Samaila Shuaibu, Kasimu Shuaibu da Aliyu Bala, waɗanda daga bisani aka miƙa wa shugaban al’ummar yankin.

Rundunar sojojin ta ce za ta ci gaba da gudanar da ayyukan yaƙi da ƴan bindiga da sauran masu aikata laifuka domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma. Ta kuma tabbatar wa mazauna yankin cewa za ta ci gaba da mayar da martani cikin gaggawa kan duk wata barazanar tsaro.

LABARAI MASU NASABA

Zama Shugaban Nijeriya Babbar Ni’ima Ce Daga Allah — Tinubu

‘Yan Ta’adda Sun Yi Wa Tawagar ’Yansanda Kwanton Ɓauna A Hanyar Zamfara

Kebbi
Abubakar Sulaiman
Website |  + postsBio
  • Abubakar Sulaiman
    Dino Melaye Ya Ƙalubalanci Tinubu Gasar Karanta Alƙur’ani
  • Abubakar Sulaiman
    Ba Za Mu Yarda Da Maguɗin Zaɓe Ba – Dino Melaye Ya Gargaɗi INEC
  • Abubakar Sulaiman
    Tinubu Ne Zai Lashe Zaɓen Shugaban Ƙasa A 2027 – Barau
  • Abubakar Sulaiman
    Sojoji Sun Fara Farautar Maharan Da Suka Kashe Abokin Aikinsu A Filato

MASU ALAKA

Tinubu
Manyan Labarai

Zama Shugaban Nijeriya Babbar Ni’ima Ce Daga Allah — Tinubu

November 2, 2026
‘Yan Ta’adda Sun Yi Wa Tawagar ’Yansanda Kwanton Ɓauna A Hanyar Zamfara
Labarai

‘Yan Ta’adda Sun Yi Wa Tawagar ’Yansanda Kwanton Ɓauna A Hanyar Zamfara

November 2, 2026
Kano: An Kama ’Yan Kasuwa Bisa Zargin Ƙoƙarin Sauya Ranar Ƙarewar Amfanin Wata Madara
Manyan Labarai

Kano: An Kama ’Yan Kasuwa Bisa Zargin Ƙoƙarin Sauya Ranar Ƙarewar Amfanin Wata Madara

November 2, 2026
Next Post
Xi Jinping Ya Tattauna Da Sultan Na Oman Haitham Bin Tariq Al- Said

Xi Jinping Ya Tattauna Da Sultan Na Oman Haitham Bin Tariq Al- Said

LABARAI MASU NASABA

Tinubu

Zama Shugaban Nijeriya Babbar Ni’ima Ce Daga Allah — Tinubu

November 2, 2026
Bautawa Jama’a-Mabudin Fahimtar Ayyukan JKS

Bautawa Jama’a-Mabudin Fahimtar Ayyukan JKS

November 2, 2026
‘Yan Ta’adda Sun Yi Wa Tawagar ’Yansanda Kwanton Ɓauna A Hanyar Zamfara

‘Yan Ta’adda Sun Yi Wa Tawagar ’Yansanda Kwanton Ɓauna A Hanyar Zamfara

November 2, 2026
Ma’aunin JKS Na Zabar Mambobi Da Jami’anta

Ma’aunin JKS Na Zabar Mambobi Da Jami’anta

November 2, 2026
Kano: An Kama ’Yan Kasuwa Bisa Zargin Ƙoƙarin Sauya Ranar Ƙarewar Amfanin Wata Madara

Kano: An Kama ’Yan Kasuwa Bisa Zargin Ƙoƙarin Sauya Ranar Ƙarewar Amfanin Wata Madara

November 2, 2026
Xi Jinping Ya Tattauna Da Sultan Na Oman Haitham Bin Tariq Al- Said

Xi Jinping Ya Tattauna Da Sultan Na Oman Haitham Bin Tariq Al- Said

November 2, 2026
Sojoji Sun Kuɓutar Da Mutane 11 Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Kebbi

Sojoji Sun Kuɓutar Da Mutane 11 Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Kebbi

November 2, 2026
Dino Melaye Ya Ƙalubalanci Tinubu Gasar Karanta Alƙur’ani

Dino Melaye Ya Ƙalubalanci Tinubu Gasar Karanta Alƙur’ani

November 2, 2026
Shin Wannan Ce Shekarar Da “Kano Pillars” Za Su Sake Lashe Kofin NPFL?

Shin Wannan Ce Shekarar Da “Kano Pillars” Za Su Sake Lashe Kofin NPFL?

November 2, 2026
Yusuf Ya Miƙa Sunan Sunusi Bature Da Tsohon Kakakin Majalisa Gani Domin Naɗa Su Kwamishinoni

Yusuf Ya Miƙa Sunan Sunusi Bature Da Tsohon Kakakin Majalisa Gani Domin Naɗa Su Kwamishinoni

November 2, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.