ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Friday, September 11, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Sojoji Sun Kashe ‘Yan Ta’adda 24 Tare Da Ƙwato Makamai Masu Yawa A Yobe

by Sulaiman
5 months ago
Sojoji

Dakarun rundunar ‘Operation HADIN KAI’ sun daƙile wani harin haɗin gwiwa da ‘yan ta’adda suka kai a Kukareta da ke Jihar Yobe a daren Alhamis, inda suka kashe aƙalla ‘yan ta’adda 24 tare da kwato makamai masu yawa.

A wata sanarwa da aka wallafa a shafin Facebook na rundunar sojin Nijeriya a safiyar Alhamis, an bayyana cewa an kai harin ne a tsakar dare na ranar 23 ga Afrilu, 2026, inda aka shafe sa’o’i ana gwabzawa har zuwa misalin ƙarfe 3:00 na daren. Sai dai sojojin Sector 2 na hadin gwiwa (Arewa ta gabas) sun mayar da martani cikin gaggawa da haɗin kai.

Sanarwar, mai ɗauke da sa hannun Jami’in Yaɗa Labarai, Laftanar Kanal Sani Uba, ta ce sojojin sun “yi nasarar daƙile wani ƙaƙƙarfan harin ta’addanci a yankin Kukareta,” inda suka aiwatar da “tsarin farmaki da kariya” wanda ya tilasta maharan ja da baya cikin ruɗani.

ADVERTISEMENT

A yayin fafatawar, rahotanni sun nuna cewa sojojin sun yi wa maharan mummunar illa, inda aka kashe ‘yan ta’adda 24 zuwa yanzu, yayin da ake ci gaba da sintiri da bincike a yankin da lamarin ya afku.Hukumomin soji sun kuma tabbatar da kwato manyan makamai da alburusai.

Kayayyakin da aka kwato sun haɗa da bindigogi AK-47 guda 18, manyan bindigogin GPMG guda 3, bindigogin PKT masu sarrafa kansu guda 2, bututun RPG guda 3, bututun mortar guda 2, gurneti guda 4, magazin AK-47 guda 18, da kuma alburusai masu yawa na 7.62mm da ake amfani da su a bindigar PKT.

LABARAI MASU NASABA

ASUU Ta Yi Barazanar Shiga Yajin Aiki Na Ƙasa Gaba Ɗaya

Dalilin Da Ya Sa Ba Zan Janye Wa Atiku Ba A Zaɓen 2027 – Peter Obi

Sojoji
Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Gwarzon Gwamnan Shekarar 2026 Kwamared Nasir Idris
  • Sulaiman
    Gwarzon Shekarar 2026 Abdulsamad Rabiu
  • Sulaiman
    Buƙatar Ɗaukar Matakan Daƙile Yaɗuwar Cutar Mashaƙo A Nijeriya
  • Sulaiman
    Ding Xuexiang Ya Halarci Taron Kolin CIFTIS Tare Da Ganawa Da Manyan Jami’an Kasashen Waje

MASU ALAKA

Sojoji
Manyan Labarai

ASUU Ta Yi Barazanar Shiga Yajin Aiki Na Ƙasa Gaba Ɗaya

September 11, 2026
Sojoji
Manyan Labarai

Dalilin Da Ya Sa Ba Zan Janye Wa Atiku Ba A Zaɓen 2027 – Peter Obi

September 11, 2026
Cutar Kwalara Na Ci Gaba Da Yi Wa ‘Yan Nijeriya Kisan Mummuƙe
Manyan Labarai

Buƙatar Ɗaukar Matakan Daƙile Yaɗuwar Cutar Mashaƙo A Nijeriya

September 11, 2026
Next Post
Bayan Artabu Na Tsawon Awanni 3, Sojoji Sun Kashe ‘Yan Ta’adda Da Dama A Zamfara

Bayan Artabu Na Tsawon Awanni 3, Sojoji Sun Kashe 'Yan Ta’adda Da Dama A Zamfara

LABARAI MASU NASABA

Sojoji

ASUU Ta Yi Barazanar Shiga Yajin Aiki Na Ƙasa Gaba Ɗaya

September 11, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwarzon Gwamnan Shekarar 2026 Kwamared Nasir Idris

September 11, 2026
Sojoji

Dalilin Da Ya Sa Ba Zan Janye Wa Atiku Ba A Zaɓen 2027 – Peter Obi

September 11, 2026
Farashin Siminti Zai Ragu Idan Farashin Kayan Aiki Ya Sauka – BUA

Gwarzon Shekarar 2026 Abdulsamad Rabiu

September 11, 2026
Cutar Kwalara Na Ci Gaba Da Yi Wa ‘Yan Nijeriya Kisan Mummuƙe

Buƙatar Ɗaukar Matakan Daƙile Yaɗuwar Cutar Mashaƙo A Nijeriya

September 11, 2026
Ding Xuexiang Ya Halarci Taron Kolin CIFTIS Tare Da Ganawa Da Manyan Jami’an Kasashen Waje

Ding Xuexiang Ya Halarci Taron Kolin CIFTIS Tare Da Ganawa Da Manyan Jami’an Kasashen Waje

September 10, 2026
Sin Ce Ta Zo Ta Farko A Rahoton Yanayin Tsaron Jama’a Na Duniya

Sin Ce Ta Zo Ta Farko A Rahoton Yanayin Tsaron Jama’a Na Duniya

September 10, 2026
Sin Ta Ciri Tuta Game Da Rawar Gani Da Take Takawa A Fannin Warware Kalubalen Tsaro A Gabas Ta Tsakiya

Sin Ta Ciri Tuta Game Da Rawar Gani Da Take Takawa A Fannin Warware Kalubalen Tsaro A Gabas Ta Tsakiya

September 10, 2026
Gwamnatin Tarayya Ta Gwangwaje Tawagar Kwallon Kwando Ta Mata Da Dala 100,000 Kowace

Gwamnatin Tarayya Ta Gwangwaje Tawagar Kwallon Kwando Ta Mata Da Dala 100,000 Kowace

September 10, 2026
Sin Da Amurka Na Gudanar Da Tattaunawa Dangane Da Yiwuwar Rage Harajin Ramuwar Gayya Wanda Darajarsa Ka Iya Kaiwa Dala Biliyan 30

Sin Da Amurka Na Gudanar Da Tattaunawa Dangane Da Yiwuwar Rage Harajin Ramuwar Gayya Wanda Darajarsa Ka Iya Kaiwa Dala Biliyan 30

September 10, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.