ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ba Mu Sayar Wa Dangote Da Reshen Jami’ar SAZU Na Yuli Ba-Gwamnatin Bauchi

by Khalid Idris Doya
2 months ago

Gwamnatin Jihar Bauchi ta musanta jita-jitar da ke yawo a kafafen sada zumunta da cewa ta na shirin mayar da reshen Jami’ar Sa’adu Zungur (SAZU) da ke Yuli a cikin garin Bauchi zuwa harabar dindindin ta jami’ar da ke Gadau.

Haka kuma, gwamnatin ta ƙaryata bayanan da suke yaɗuwa da ke cewa ta sayar ko za a sayar da reshen Jami’ar na Yuli ga fitaccen attajiri, Alhaji Aliko Dangote, tana mai bayyana iƙirarin a matsayin ƙarya tsagwaronta, kuma mara tushe balle makama.

Kwamishiniyar ma’aikatar kula da manyan makarantun gaba da sakandare, Dakta Hadiza Abdulkadir Kango, ta musanta wannan zargi a cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Lahadi.Sanarwar da Jami’in yaɗa labarai na ma’aikatar, Awwal Sani Waziri, ya sanya wa hannu ta ja hankalin jama’a da su yi watsi da jita-jitar da ake cewa za tashi reshen Bauchi (Yuli) ta Jami’ar Sa’adu Zungur zuwa Gadau kuma a sayar da reshen makarantar.

ADVERTISEMENT

Ma’aikatar ta bayyana cewa wasu masu son tayar da fitina daga ciki da wajen jami’ar ne suka ƙirƙiri wannan labari domin haifar da rashin jituwa da kuma cimma muradunsu na ƙashin kansu ta hanyar yaɗa labaran ƙarya.Kwamishiyar ta ma’aikatar kula da ilimi mai zurfi ta kuma yi Allah-wadai da wannan batun tare da kira ga al’umma da su yi watsi da jita-jitar, tana mai jaddada cewa an ƙirƙire ta ne da gangan domin yaudarar jama’a.

Dakta Kango ta bayyana cewa hukumomin da abin ya shafa sun fara bincike domin gano waɗanda suka ƙirƙiri da kuma yaɗa wannan bayanin na ƙarya, inda za a ɗauki matakin doka a kansu idan ya zama dole.

LABARAI MASU NASABA

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

Ta kuma tabbatar da cewa gwamnatin Jihar Bauchi ba ta da wani shiri na mayar da ko sayar da reshen Jami’ar ta Yuli.A maimakon haka, ta ce gwamnati na ci gaba da jajircewa wajen bunƙasa reshen Jami’ar, inda ta tsara gudanar da ayyukan gina hanyoyin shiga harabar, ɗakin kwanan ɗalibai mata da kuma katanga domin inganta walwalar ɗalibai, yanayin koyo da kuma tsaro.

Kwamishiniyar ta kuma gode wa jama’ar da suka gaggauta sanar da ma’aikatar game da wannan jita-jita, tare da yin kira ga mazauna jihar su ci gaba da bai wa gwamnati goyon baya wajen ƙarfafa ilimi mai zurfi a Jihar Bauchi.

Khalid Idris Doya
+ postsBio
  • Khalid Idris Doya
    https://hausa.leadership.ng/author/khalid-idris-doya/
    Yaro Ya Harbe Kansa Har Lahira Bayan Mafarauci Ya Yi Sakaci Da Bindigarsa A Bauchi
  • Khalid Idris Doya
    https://hausa.leadership.ng/author/khalid-idris-doya/
    An Kama Mutane 5 Da Sassan Jikin Ɗan’Adam Za Su Yi Tsafi A Bauchi
  • Khalid Idris Doya
    https://hausa.leadership.ng/author/khalid-idris-doya/
    Tsohon Mai Neman Takarar Gwamnan Bauchi, Bala Jibrin, Ya Fice Daga APC Kan Zargin Ɗoki-ɗora
  • Khalid Idris Doya
    https://hausa.leadership.ng/author/khalid-idris-doya/
    ‘Yansanda Sun Cafke Tsoho Mai Shekara 70 Kan Zargin Yi Wa ‘Yar Shekara 8 Fyaɗe A Bauchi

MASU ALAKA

Sojoji
Manyan Labarai

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Ballon D'or
Manyan Labarai

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

September 8, 2026
Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue
Manyan Labarai

Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue

September 8, 2026
Next Post
Sojoji Sun Daƙile Yunƙurin ISWAP Na Sace Ɗalibai A Borno, Sun Ceto 46

Sojoji Sun Daƙile Yunƙurin ISWAP Na Sace Ɗalibai A Borno, Sun Ceto 46

LABARAI MASU NASABA

Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.