ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Friday, September 11, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Taron G20 Ya Nuna Makomar Duniya Mai Haske

by Sulaiman
10 months ago
G20

A jiya Asabar aka kaddamar da taron kolin kungiyar G20 a Johannesburg na kasar Afirka ta Kudu, tare da zartas da wata hadaddiyar sanarwa.

Kafin hakan, kasar Amurka ta ki tura babban jami’i zuwa taron, bisa dalilin wai gwamnatin kasar Afirka ta Kudu tana “cin zarafin ‘yan kasar fararen fata”, kana ta yi gargadin cewa, kada a zartas da wata sanarwa a wajen taron, a matsayin ra’ayi daya da mambobin kungiyar G20 suka cimma. Sai dai abun da ya faru daga bisani ya nuna cewa, umarnin da kasar Amurka ta bayar ba shi da amfani, in ban da janyo wa kanta wulakanci.

Wannan lamarin ya zama wata nasara da kasar Afirka ta Kudu ta samu, kuma ta nuna karfafar matsayin ra’ayin kasancewar mabambantan bangarori masu fada-a-ji da yawa a duniya. Kamar yadda kakakin shugaban kasar Afirka ta Kudun Vincent Magwenya ya fada, cewa zartas da wannan hadaddiyar sanarwa a wajen taron ya nuna yadda kasashe daban daban suke kokarin hadin gwiwa da juna, da goyon bayan ra’ayin kasancewar mabambantan bangarori masu fada-a-ji a duniya. Hakan ya kuma dace da babban taken taron G20 na wannan karo, wato “Hadin Kai, da Daidaito da kuma Dorewa.”

ADVERTISEMENT

A nata bangare, kasar Sin ita ma ta jaddada matsayinta, na rungumar ra’ayin kasancewar mabambantan bangarori masu fada-a-ji a duniya, a wajen taron, inda firaministan kasar Sin Li Qiang, ya yi kira da a gaggauta yin gyaran fuska ga kungiyoyin kasa da kasa, da kara fitowa da muryar kasashe masu tasowa a duniya, da kafa wani budadden tsarin tattalin arziki da ciniki mafi adalci.

Hakika kasar Sin ta dade tana kokarin daukaka matsayin tunanin kasancewar bangarori masu fada-a-ji da yawa a duniya, inda abubuwan da kasar ta yi suka hada da, ba da taimako ga kungiyar kasashen Afirka ta AU don ta zama mambar kungiyar G20, da habaka tsare-tsaren kungiyoyin BRICS, da SCO da dai sauransu. Ban da haka, kungiyar shiga tsakani don daidaita sabani ko (IOMed) da kasar Sin da sauran kasashe fiye da 30 suka kafa, ta samar da wata sabuwar hanyar daidaita rikici, wadda ba ta cikin tsare-tsaren neman kwantar da rikici da kasashen yamma suka tsara.

LABARAI MASU NASABA

Sin Ce Ta Zo Ta Farko A Rahoton Yanayin Tsaron Jama’a Na Duniya

Sin Ta Ciri Tuta Game Da Rawar Gani Da Take Takawa A Fannin Warware Kalubalen Tsaro A Gabas Ta Tsakiya

Sai dai wani abun tambayar shi ne ko mene ne dalilin da ya sa kasar Sin take goyon bayan ra’ayin kasancewar bangarori masu fada-a-ji da yawa a duniya? Amsar ita ce hakan ya dace da tunanin da kasar ke kokarin yayatawa, na kafa “Al’ummar dan Adam mai kyakkyawar makomar bai daya”. Yayin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci tarukan kungiyar G20 a lokacin baya, ya taba bayyana tunanin kamar haka, “Ci gaba na bai daya na kasashe daban daban shi ne ci gaba na gaske”. Kana ya ce ya kamata a sanya ci gaban tattalin arzikin duniya ya amfani kasashe daban daban, inda za a yi kokarin tabbatar da adalci da daidaito, maimakon barin wata kasa a baya.

Kafofin yada labarai na kasashen yamma, suna son bayyana takarar da kasashen Amurka da Sin suke yi a matsayin abu mai matukar muhimmanci dake faruwa a duniya. Sai dai idan an kwatanta tunanin da kasar Sin da sauran kasashe suke goyon bayansa, da matakan radin kai da wasu kasashe ke dauka, za mu iya ganin cewa, babban sabani mafiya tasiri a duniya, shi ne bambancin ra’ayin da ake samu tsakanin kasashe masu tasowa, da kasashe masu sukuni dake yammacin duniya, inda wani bangarensu ke rungumar ra’ayin kasancewar bangarori masu fada-a-ji da yawa a duniya, yayin da dayan bangare ke neman kiyaye tsohon tsari na “Kasashen yamma ke ba da umarni, don sauran kasashe su bi shi”.

Sai dai tabbas, sabon tsari zai maye gurbin tsohon, ganin yadda shugabannin kasashe daban daban suka rike hannuwan juna a wajen taron kolin kungiyar G20 da ya gudana a nahiyar Afirka a wannan karo, kana gargadin da kasar Amurka ta bayar, bai hana su cimma matsaya daya ta daukaka ra’ayin kasancewar bangarori masu fada-a-ji da yawa a duniya ba. Da haka, ma iya cewa taron na wannan karo ya kara tabbatar mana da makomar duniya mai haske. (Bello Wang)

G20
Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Ding Xuexiang Ya Halarci Taron Kolin CIFTIS Tare Da Ganawa Da Manyan Jami’an Kasashen Waje
  • Sulaiman
    Sin Ce Ta Zo Ta Farko A Rahoton Yanayin Tsaron Jama’a Na Duniya
  • Sulaiman
    Sin Ta Ciri Tuta Game Da Rawar Gani Da Take Takawa A Fannin Warware Kalubalen Tsaro A Gabas Ta Tsakiya
  • Sulaiman
    Gwamnatin Tarayya Ta Gwangwaje Tawagar Kwallon Kwando Ta Mata Da Dala 100,000 Kowace

MASU ALAKA

Sin Ce Ta Zo Ta Farko A Rahoton Yanayin Tsaron Jama’a Na Duniya
Daga Birnin Sin

Sin Ce Ta Zo Ta Farko A Rahoton Yanayin Tsaron Jama’a Na Duniya

September 10, 2026

Sin Da Amurka Na Gudanar Da Tattaunawa Dangane Da Yiwuwar Rage Harajin Ramuwar Gayya Wanda Darajarsa Ka Iya Kaiwa Dala Biliyan 30
Daga Birnin Sin

Sin Da Amurka Na Gudanar Da Tattaunawa Dangane Da Yiwuwar Rage Harajin Ramuwar Gayya Wanda Darajarsa Ka Iya Kaiwa Dala Biliyan 30

September 10, 2026
Next Post
Ƴan Ta’adda Sun Sace Mata Manoma 13 A Borno

Gwamnatin Tarayya Ta Dakatar da Shirin Ƙara Kuɗin Jarabawar WAEC da NECO

Gwamnatin Tarayya Za Ta Rika Bai Wa Ɗalibai 100MB Na Data Kyauta Kullum

September 10, 2026
Sin Da Amurka Na Wanzar Da Mu’amala Game Da Shirin Ganawar Da Manyan Shugabannin Kasashen Biyu Za Su Yi A Bana

Sin Da Amurka Na Wanzar Da Mu’amala Game Da Shirin Ganawar Da Manyan Shugabannin Kasashen Biyu Za Su Yi A Bana

September 10, 2026
Sojoji Sun Ceto Fasinjoji Uku Da ‘Yan Bindiga Suka Harba A Filato

Sojoji Sun Ceto Fasinjoji Uku Da ‘Yan Bindiga Suka Harba A Filato

September 10, 2026
Xi Zai Halarci Taron BRICS Karo Na 18 A Indiya

Xi Zai Halarci Taron BRICS Karo Na 18 A Indiya

September 10, 2026
Rodri Ya Nemi Afuwar Valencia Dangane Da Kalaman Da Yayi Akanta

Rodri Ya Nemi Afuwar Valencia Dangane Da Kalaman Da Yayi Akanta

September 10, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.