• English
  • Business News
Thursday, October 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Taron Wakilan Jam’iyyar Kwaminis Ta Kasar Na 20 Da Muhimmancinsa

by CMG Hausa
3 years ago
Kwaminis

A ranar Lahadi 16 ga watan Oktoba ne aka bude taron wakilai karo na 20 na jam’iyyar kwaminis da ke kan karagar mulkin kasar Sin (JKS) a Beijing, babban birnin kasar Sin, taron dake da muhimmancin gaske, wanda har ya jawo hankalin kasa da kasa. A wannan karon dai an samu halartar wakilai, gami da wadanda aka ba su goron gayyata na musamman sama da 2300.

Babban sakataren kwamitin kolin JKS, kana shugaban kasar ta Sin, Xi Jinping ya bayyana yayin bude taron cewa, cikin shekaru 10 da suka gabata, an samu wasu manyan nasarori 3 masu matukar muhimmanci, wandada suka shiga tarihin JKS da al’ummar kasar.

  • Sin Dake Bin Hanyar Samun Bunkasuwa Cikin Lumana Wata Dama Ce Ga Duniya

“Mun cika shekaru 100 da kafuwar JKS, gami da mun shiga wani sabon zamani na gurguzu mai sigar kasar Sin, kuma mun fatattaki kangin talauci baki daya, kana mun kammala ginin al’umma mai matsakaicin ci gaba ta kowanne bangare, wato dai, mun cika burinmu na farko a lokacin da muke murnar cika shekaru 100 da kafuwar JKS.”
Hakika, abin da ya jawo hankalina shi ne, yadda aka fitar da dukkanin mutane da ke fama da kangin talauci a karkarar kasar Sin da yawansu ya kai kusan miliyan 100, abin jinjinawa ne, wanda kuma ya bayar da babbar gudummawa wajen kawar da talauci a duk fadin duniya.

Ta fannin tattalin arziki kuwa an samu haurawar tattalin arziki kakkarfa a shekaru goman da suka wuce.

Ma’aunin GDP na kasar a karkashin jagorancin shugaba Xi Jinping a inuwar JKS ya nuna ma’aunin ya karu zuwa kudin Sin Yuan triliyan 114 (kimanin dalar Amurka triliyan 17.72), wannan ya dauki kaso 18.5 na tattalin arzikin duniya. Kasar Sin dai ita ce kasa ta biyu mafi girman tattalin arziki a duniya.

LABARAI MASU NASABA

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

A baya baya kuwa yaki da cutar COVID-19 ita ma gagarumar nasara ce. Abin jinjinawa ne da burgewa a ganin yadda a karkashin jagorancin JKS aka yaki cutar COVID-19.

Gwamantin kasar karkashin shugabancin Xi Jinping ta bayar da duk abin da ya kamata domin ganin an kawar da cutar kamar: kayan gwaje-gwaje da magunguna da gina asibitocin gaggawa da kandagarki a duk fadin kasar. In dai akwai jagoranci na-gari to za’a samu nasara a duk abin da aka yi niyyar aiwatarwa.

Duk wannan ci gaban, da kasar Sin take samu ba abin mamaki ba ne, domin kuwa wannan ya samo asali ne daga jagoranci mai inganci da JKS take bayarwa musamman daga shekarar 1949 da aka kafa jamhuriyar jama’ar Sin da kuma daga shekarar 1978 lokacin da aka fara yin kwaskwarima a gida da kuma bude kofa ga ketare, da kuma nasarorin da aka samu a shekaru goman da suka wuce. (Lawal Sale)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko
Daga Birnin Sin

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

October 8, 2025
Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan
Daga Birnin Sin

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

October 8, 2025
Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana
Daga Birnin Sin

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

October 8, 2025
Next Post
Kasar Sin Na Adawa Da Yin Shisshigi Cikin Harkokin Gidan Kasashe Masu Tasowa Bisa Hujjar Kare Hakkokin Dan Adam

Kasar Sin Na Adawa Da Yin Shisshigi Cikin Harkokin Gidan Kasashe Masu Tasowa Bisa Hujjar Kare Hakkokin Dan Adam

LABARAI MASU NASABA

Gobara Ta Sake Ƙone Kasuwar Oba A Benin

Gobara Ta Sake Ƙone Kasuwar Oba A Benin

October 9, 2025
Kofin Duniya U-20: Argentina Ta Lallasa Nijeriya Da Ci 4-0

Kofin Duniya U-20: Argentina Ta Lallasa Nijeriya Da Ci 4-0

October 9, 2025
Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu

Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu

October 9, 2025
HOTUNA: Yadda Obasanjo Ya Ƙaddamar Da Sabuwar Cibiyar Taron Ƙasa Da Ƙasa A Bauchi

HOTUNA: Yadda Obasanjo Ya Ƙaddamar Da Sabuwar Cibiyar Taron Ƙasa Da Ƙasa A Bauchi

October 9, 2025
Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

October 9, 2025
Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

October 8, 2025
Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

October 8, 2025
Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

October 8, 2025
Majalisa Ta Nemi Jami’an Tsaro Su Ceto Daliban Jami’ar Gusau 30 Da Aka Sace

Kafa ‘Yansandan Jihohi Na Da Matuƙar Muhimmanci Wajen Magance Matsalar Rashin Tsaro

October 8, 2025
Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

October 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.