An samu tsaiko wajen gudanar da zaɓe a ranar Asabar a mazaɓar tsohon gwamnan jihar Osun, kuma tsohon Ministan Harkokin Cikin Gida, Ogbeni Rauf Aregbesola da ke garin Ilesa, bayan da wasu da ake zargin ‘yan banga ne sun far wa yankin.
Wannan lamari ya sanya wasu masu kaɗa ƙuri’ar tserewa daga mazaɓar, inda hakan ya dakatar da aikin zaɓen na wani ɗan lokaci tare da haifar da fargaba a tsakanin al’ummar da ke wajen. Hakan ya faru ne ana tsaka da gudanar da zaben gwamnan jihar Osun, wanda ya janyo fargaba game da tsaron masu jefa kuri’a da kuma yadda zaɓen zai gudana lami lafiya a yankin da abin ya shafa.
Wasu daga cikin wakilan jam’iyyu a mazaɓar sun yi zargin cewa waɗannan ‘yan banga da suka kawo cikas suna da alaƙa da jam’iyyar APC. To sai dai kuma, wakiliyar jam’iyyar APC a mazaɓar, Misis Abogunloko Olufunke, ta yi watsi da wannan zargi, inda ta ce ba ta san mutanen ba kuma jam’iyyar ba ta san su ba.
Ya zuwa lokacin hada wannan rahoto, ba a bayyana ainihin abin da ya haifar da rikicin ba, yayin da ake ci gaba da jiran ƙarin bayani kan ko jami’an tsaro sun yi wani kamu ko kawo ɗauki a wajen.














