ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Tuesday, September 8, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Tsakanin Yanayin Sanyi Da Na Zafi Wanne Ya Fi Maka Dadi?

by Muhammad Bakir Bello
1 week ago
Yanayin

Muhawararmu ta wannan makon, an tattauna ta ne kai tsaye da masu karatu, kan shin tsakanin yanayin sanyi da na zafi, wanne ka fi so ko kuma ya fi maka dadi? Kamar kowane lokaci, SANI ANWAR da MUHAMMAD BAKIR, su ne suka tattaro ra’ayoyin naku.

Bature Umar, Jihar Kano

Batu na gaskiya, na fi son yanayin sanyi. Dalili kuwa, a lokacin sanyi, an fi lafiya, cututtuka da dama neman su ake a rasa duk sun kama gabansu. Musamman ma mu a Nijeriya, ba mu da cutar da ta fi ta Maleriya, sakamakon yawan Sauron da muke da shi, wanda a lokacin sanyi, mafi yawan Sauro mutuwa yake yi.

ADVERTISEMENT

Matsalar kawai ta ce, a lokacin sanyi a kan takura, mutane su kasa sakewa, ko wanka ma sai mutum ya yi da gaske zai iya yi. Amma duk da haka, lokacin sanyin ya fi na zafi dadin sha’ani.

Ibrahim Ahmed Ibrahim, Zaria

LABARAI MASU NASABA

Mene Ne Ra’ayinku Kan Shigar Mata Harkokin Siyasa Gadan-gadan?

Tsakanin Digiri Da Sana’a Wanne Ya Fi Muhimmanci A Wannan Lokacin?

Kai wallahi sanyi ya fi min dadi sosai. Da sanyi ina iya koyarwa lafiya, ba tare da gumi ya jika rigata ba. Dalibai ma suna kula da karatu yadda ya kamata, amma da zafi kuwa, aji yana yin zafi, fanka ba ta isa, kowa yana share gumi.

Haka nan, ko da daddare ma a lokacin sanyi, bacci ya fi dadi sosai, mutum zai iya rufe jikinsa da bargo ya yi bacci mai nauyi.

Halima Elukpo

Na fi son yanayin sanyi, domin kuwa na fi samun lafiya da nutsuwa yadda ya kamata. Duk lokacin da na zo yin bacci, rufa nake yi na yi kwanciyata, har gari ya waye ba ni da wata matsala. Amma a lokacin zafi kuwa, musamman idan babu wuta, baki-daya bacci gagara yake yi, sai dai mutum ya yi ta faman juyi.

Haka zalika, a lokacin zafi kwata-kwata ma bacci bai cika yin dadi ba, ko da kuwa akwai wuta. Sannan, duk ‘yan kananan cututtuka, sun fi tashi a lokacin zafi, musamman cutar Maleriya sakamakon cizon sauro.

Kueen Merry Onokome

Na fi son lokacin sanyi, saboda ya fi saukin samun dumi fiye da yadda yake da saukin rage zafi. Bugu da kari, mutane suna samun kuzari da kuma yin ayyuka yadda ya kamata a lokacin sanyi.

Ina son sanya rigunan sanyi masu dadin jin dumi da cin abinci mai zafi da kuma samun barci mai dadi yayin da ake jin sautin ruwan sama ko kuma rungume juna a cikin bargo.

Haka kuma, lokacin sanyi yana sa lokacin rana ya wuce da sauri, ma’ana, lokaci ya fi saurin tafiya.

Abdulmudallib Ibrahim Bature, Baure Katsina

Ni na  fi son lokacin bazara, wato lokacin zafi Kenan, domin kuwa ko a lokacin idan mutum ya lura saboda yadda ni’imar take, ai ko itatuwa ma lokacin suke yin sabon tofo ko sabbin ganyaye. Don haka, ni ma a lokacin ne na fi jin dadin jikina, kuma na fi yin sheki da haske.

A wannan lokacin, ina yin wanka a duk lokacin da nake so, sabanin lokacin sanyi wanda ni ma ko da wasa ba zan iya fara yin haka ba.

Buhari Abdullahi, Jihar Kaduna

Na fi jin dadin yanayin zafi. Da farko, zafi da hasken rana suna taimakawa wajen busar da tufafi da abinci.

Na biyu, tsirrai (plant) suna amfani da hasken rana wajen yin ‘photosynthesis’, wanda ke taimaka musu wajen samar da abincinsu. Na uku, yanayin zafi yana saukaka ayyuka da dama na waje, kamar noma da wasanni.

Saboda haka, a tunanina da nawa ra’ayin, yanayin zafi yana da matukar amfani ga rayuwa idan ana amfani da shi cikin daidaituwa yadda ya kamata.

Sannan kuma baya ga haka, yana kara nuna muhimmancin tsafta ko kuma a ce tsaftar jiki, muhalli da wajen kwana. Lokacin zafi, yana da matukar wahala, sai ka ga mutum bai yi wanka ba ko gyaran daki, ko kuma muhalli baki-daya, saboda kwayoyin halittu (enzymes), suna saurin yaduwa a jiki da kuma sauran al’umma baki-daya.

Ahmad Bello, Jihar Kaduna

Ni a gare ni, yanayin sanyi ya fi dadi sosai. Saboda a lokacin sanyi, mutum ya kan zauna cikin yanayin nutsuwa, wanda ba kasafai yake samu a lokacin zafi ba. A lokacin sanyi, na kan fi jin dadin karatu, saboda babu takura ta rashin iska sosai. Haka kuma, na kan samu damar yin tunani cikin nutsuwa ba tare da jin wata wahala ba.

Ban cika son lokacin zafi ba, saboda rana ta kan yi zafi sosai a wannan lokacin. Hakan yana sa mutum ya ji gajiya sosai da rashin kuzarin yin aiki. Saboda haka, idan aka ba ni zabi tsakanin yanayin sanyi da na zafi, zan zaɓi yanayin sanyi.

Zakari Ya’u Hashim, Mando Kaduna

Magana ta gaskiya, na fi son yanayin sanyi, wanda kuma ba irin na damina ba. Domin a lokacin sanyi, na fi jin dadin jikina tare da samun walwala, amma a lokacin zafi (Bazara), sam ba na samun cikakkiyar walwala da jin dadi, duk sai jikina ya daddaure. Shi yasa ma idan an shiga wannan lokaci na zafi, har kosawa nake yi, ina yin Allah-Allah ya fita.

Yanayin
Muhammad Bakir Bello
+ postsBio
    This author does not have any more posts.

MASU ALAKA

Mene Ne Ra’ayinku Kan Shigar Mata Harkokin Siyasa Gadan-gadan?
Taskira

Mene Ne Ra’ayinku Kan Shigar Mata Harkokin Siyasa Gadan-gadan?

September 5, 2026
Tsakanin Digiri Da Sana’a Wanne Ya Fi Muhimmanci A Wannan Lokacin?
Taskira

Tsakanin Digiri Da Sana’a Wanne Ya Fi Muhimmanci A Wannan Lokacin?

July 25, 2026
Tasirin AI (Artificial Intelligence) A Harkokin Al’umma Na Yau Da Kullum
Taskira

Tasirin AI (Artificial Intelligence) A Harkokin Al’umma Na Yau Da Kullum

July 18, 2026
Next Post
Yanayin

JAMB Ta Ƙara Wa’adin Amincewar Guraben Karatu Zuwa 30 Satumba

LABARAI MASU NASABA

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026
Xi Ya Zanta Ta Wayar Tarho Da Firaministan Birtaniya

Xi Ya Zanta Ta Wayar Tarho Da Firaministan Birtaniya

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.