Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Jami’a ta Ƙasa (JAMB) ta ƙara wa’adi ga ɗaliban da aka ba guraben karatu daga shekarar 2021 zuwa yanzu za su amince ko su ƙi amincewa da guraben da aka ba su da suka rage a tsarin hukumar. Yanzu an tsawaita wa’adin zuwa 30 ga Satumba, 2026, domin bai wa ɗaliban damar yanke hukunci kan guraben karatunsu.
JAMB ta bayyana cewa tun da farko ta sanya 31 ga Agusta, 2026 a matsayin ranar ƙarshe, amma ta yanke shawarar ƙara wa’adin domin ɗaliban da har yanzu ke da guraben karatu da ba su amince ko suka ƙi ba su ɗauki matakin da ya dace. Muƙaddashin Daraktan Hulɗa da Jama’a da Ka’idojin Aiki na hukumar, Dakta Fabian Benjamin, ne ya sanar da ƙarin wa’adin a ranar Asabar.
Hukumar ta shawarci ɗaliban da ke da guraben karatu da suka rage, ko ta hanyar tsarin karɓar ɗalibai na yau da kullum ko Centralised University and Institution Admission (CUIIA), da su amince ko su ƙi amincewa da guraben kafin ranar 30 ga Satumba. JAMB ta yi gargaɗin cewa rashin ɗaukar mataki kafin wa’adin zai iya shafar matsayin gurbin karatun ɗalibi.
JAMB ta ce ɗaliban da suka amince da guraben za su iya ci gaba da buga takardar shaidar admission. Waɗanda suka ƙi amincewa da guraben kuma za a mayar da bayanansu a dashboard zuwa “Not Admitted”, domin hukumar ta sabunta bayananta da kuma tabbatar da cewa tsarin bayanan ƙasa na admission ya nuna ainihin matsayin kowane ɗalibi.
Hukumar ta kuma fayyace cewa ɗaliban da ba sa karatu a makarantar da aka ba su gurbi a baya, ko waɗanda suke karatu a wani shiri daban, za su iya amincewa da tsohon gurbin sannan su nemi gyara ko gogewa idan ya dace.
Haka kuma, ɗalibin da aka ba shi gurbin karatu a 2026 amma yana da tsohon gurbi da bai amince da shi ba zai iya ƙin tsohon gurbin ba tare da hakan ya shafi sabon gurbin 2026 ba. JAMB ta ce wannan shi ne damar ƙarshe ga waɗanda abin ya shafa su daidaita matsayin tsoffin guraben karatunsu.














