ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Monday, July 20, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Tsaro: Goyon Bayan Gwamna Lawal Ga Sojoji Ba Kasafai Ake Samun Irin Sa Ba — Babban Hafsan Tsaro

by Sulaiman
3 months ago

Babban Hafsan Tsaron Nijeriya, Janar Olufemi Oluyede, ya yaba da irin gagarumin goyon bayan da Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ke bai wa rundunar Operation Fansan Yamma, yana mai cewa irin wannan tallafi ba kasafai ake ganin irinsa ba.

Janar Oluyede ya bayyana hakan ne a yayin wata ziyarar aiki da ya kai Jihar Zamfara, inda ya gana da gwamnan tare da duba hedikwatar rundunar Operation Fansan Yamma da ke Gusau.

A lokacin ziyarar girmamawa da ya kai Gidan Gwamnatin Jihar Zamfara, Babban Hafsan Tsaron ya jaddada muhimmancin haɗin kai tsakanin gwamnatin jiha da rundunar sojoji wajen magance matsalolin tsaro da suka addabi yankin.

ADVERTISEMENT

Ya ce, ya zo jihar ne domin nuna godiya ga gwamnan bisa irin rawar da yake takawa wajen tallafa wa rundunar, yana mai ƙarawa da cewa haɗin kai tsakanin gwamnati da al’umma na da matuƙar muhimmanci wajen shawo kan ƙalubalen tsaro.

Janar Oluyede ya kuma yaba wa al’ummar jihar bisa yadda suke karbar jami’an tsaro hannu bibbiyu, yana mai jaddada cewa Nijeriya ƙasa ɗaya ce da ke buƙatar haɗin kan kowa domin fuskantar barazanar tsaro.

LABARAI MASU NASABA

Sojoji Sun Daƙile Yunƙurin ISWAP Na Sace Ɗalibai A Borno, Sun Ceto 46

Ba Mu Sayar Wa Dangote Da Reshen Jami’ar SAZU Na Yuli Ba-Gwamnatin Bauchi

Ya ƙara da cewa, ya ziyarci hedikwatar rundunar Operation Fansan Yamma, inda ya gana da jami’an tsaro, ya saurari ƙalubalen da suke fuskanta, tare da warware wasu daga cikinsu, yayin da sauran aka ɗauki matakan da suka dace domin magance su nan gaba.

A nasa bangaren, Gwamna Dauda Lawal ya bayyana cewa magance matsalar ‘yan bindiga a Zamfara na nufin an rage kusan kashi 75 cikin 100 na matsalar a duk faɗin Nijeriya.

Ya ce, wajibi ne shugabanni su ɗauki matakan da suka dace domin tabbatar da zaman lafiya da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a, yana mai jaddada cewa babu wani ƙarfi da ya wuce na rundunar sojojin Nijeriya.

Gwamnan ya bayyana cewa gwamnatin sa na ci gaba da bayar da cikakken goyon baya ga jami’an tsaro, yana mai tunatar da cewa a kwanan nan Ministan Tsaro ya ƙaddamar da sabbin motocin aiki na zamani da gwamnatin jihar ta samar domin taimaka wa rundunar.

Ya kuma jaddada cewa duk wani ci gaba ba shi da amfani idan babu tsaro, don haka ne gwamnatin jihar ke bai wa bangaren tsaro fifiko a cikin manufofinta.

Gwamna Lawal ya gode wa Shugaban Ƙasa bisa tallafin da yake bai wa jihar, tare da jaddada buƙatar ƙarin goyon baya domin cimma nasarar yaƙi da matsalar tsaro.

A ƙarshe, ya tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da aiki kafaɗa da kafɗa da rundunar sojoji da sauran hukumomin tsaro domin kawo ƙarshen matsalar ’yan bindiga a jihar.

Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Tawagar Jami’an Lafiya Ta Sin Ta Bayar Da Gudunmuwar Kayayyaki Ga Asibitin Burkina Faso
  • Sulaiman
    Ra’ayin Sin Game Da AI Mai Mayar Da Hankali Kan Bukatun Dan Adam Ya Samu Goyon Bayan Kasa Da Kasa
  • Sulaiman
    Kada A Bar Kasashe Masu Tasowa A Baya A Zamanin AI
  • Sulaiman
    Gwamna Radda Ya Kaddamar da Tattaunawar Kasafin Kuɗin 2027

MASU ALAKA

Sojoji Sun Daƙile Yunƙurin ISWAP Na Sace Ɗalibai A Borno, Sun Ceto 46
Labarai

Sojoji Sun Daƙile Yunƙurin ISWAP Na Sace Ɗalibai A Borno, Sun Ceto 46

July 19, 2026
Ba Mu Sayar Wa Dangote Da Reshen Jami’ar SAZU Na Yuli Ba-Gwamnatin Bauchi
Manyan Labarai

Ba Mu Sayar Wa Dangote Da Reshen Jami’ar SAZU Na Yuli Ba-Gwamnatin Bauchi

July 19, 2026
NDLEA Ta Cafke Kwayoyin Tramadol Miliyan 1.63 Da Akai Nufin Shigar Da Su Kano
Manyan Labarai

NDLEA Ta Cafke Kwayoyin Tramadol Miliyan 1.63 Da Akai Nufin Shigar Da Su Kano

July 19, 2026
Next Post
Kamfanonin Jamus Na Fatan Kara Amfani Da Damammaki A Kasuwar Sin

Shugaba Tinubu Zai Yi Jawabi Ga Shugabannin Duniya A Taron MDD Karo Na 81

Shugaba Tinubu Zai Yi Jawabi Ga Shugabannin Duniya A Taron MDD Karo Na 81

July 19, 2026
majalisar kasa

Damawa Da Mata A Siyasa: Kujerun Majalisun Tarayya Na Iya Ƙaruwa Zuwa 121, da Kuma 397 A 2027

July 19, 2026
Kofin Duniya

Abubuwa Uku Da Ya Kamata Kusani Akan Kofin Duniya

July 19, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.