An bude bikin nune-nunen motoci na Turin na shekarar 2026, a birnin Turin na Italy a jiya Juma’a, wanda ya kunshi sabbin nau’o’in motoci da wasu shirye-shirye, ciki har da gwajin tukin motoci da wasu shirye-shiryen da ke mayar da hankali kan tsara fasalin motoci.
Galibin Sinawa masu kera motoci sun samu lambobin yabo a bikin bayar da lambobin yabon fasalin motoci na Torino watau TADA, da ya gudana a jiyan, a dakin taro na Teatro Regio.Da yake jawabi yayin bikin, babban jami’in karamin ofishin jakadancin Sin a Milan, Zhang Chenggang, ya ce masana’antar kera motoci ta Sin, na kara nacewa kan kirkire-kirkire masu zaman kansu da ingancin kayayyaki da saukaka wa masu amfani.
Ya kara da cewa, Italiya na da kwarewa sosai wajen tsara fasali da kiyaye ka’idoji da binciken injiniya da samar da kayayyaki. Yana cewa kasashen biyu na da karfin da ka iya mara wa juna baya da bangarori da dama na kara hada gwiwa.
Jimilar tamburan motoci da cibiyoyin tsara fasali 47 daga kasar Sin da sauran kasashe ne suka halarci bikin na TADA na bana. Masu kera motoci na Sin da suka hada da Chery da Geely da Great Wall Motor (GWM) da GAC, sun samu lambobin yabo a rukunoni daban-daban.
Andrea Levy, shugaban bikin nune-nunen motocin na Turin, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Sin Xinhua cewa, masu kera motoci na Sin sun kai sabbin fasahohi Italiya da Turai, kuma suna kara samun karbuwa a wajen masu sayayya. (Fa’iza Mustapha)














