Tsohon shugaban kasar Croatia, Ivo Josipovic, ya zanta da wata wakiliyar kafar CMG a kwanan baya, inda ya ce kasar Sin ta fahimci muhimmancin mutunta ikon mulkin kai, kana tana kallon sauran kasashe a matsayin daidai da juna.
Mista Josipovic ya kara da cewa, ya kamata kasashen Turai su daina damuwa kan kasar Sin, bisa zargin wai za ta “yi babakere a kasuwannin duniya”.
Ya ce, a hakika, kasar Sin abokiyar hulda ce mai aminci. Kana bangarorin Turai da Sin za su iya samarwa juna da taimako a harkokin da kowaccensu ke da fifiko, da karfafa huldar hadin gwiwa tsakaninsu.Ban da haka, Josipovic ya ce, yana jinjinawa kasar Sin, bisa nagartacciyar manufarta ta kokarin wanzar da zaman lafiya a duniya.
Yana kuma fatan ganin karin kasashe sun bi sawun Sin wajen magance halartar yaki, ko ta da rikici a wurare daban daban na duniyarmu.
Kana tsohon shugaban na kasar Croatia, ya ce matakin kasar Sin na bude kofarta ga sauran kasashe yana amfani ga ci gaban tattalin arzikinta, gami da samar da gudunmowa ga yunkurin tabbatar da kwanciyar hankali a duniya. (Bello Wang)















Discussion about this post