Kamar dai yadda aka sani shafin RUMBUN NISHADI na zakulo muku fitattun jarumai manya da kanana har ma da mawaka daga cikin masana’antar shirya finafinan hausa ta Kannywood. A yau ma shafin ya yi cozali da wata fitacciyar mawakiyar da ta shafe tsahon shekaru tana waka a cikin masana’antar shirya finafinan hausa ta Kannywood wato, MARYAM ABDULKARIM SULAIMAN wacce aka fi sani da MARYAM SANGANDALE Inda ta bayyanawa masu karatu irin gwagwarmayar da ta sha kafin fara waka da kuma kalubalen da ta fuskanta bayan fara waka, har ma da wasu batutuwan masu yawa wadanda suka shafi rayuwarta.
Ga dai tattaunawar tare da wakiliyar jaridar LEADERSHIP HAUSA RABI’AT SIDI BALA kamar haka:
Da farko masu karatu za su so su ji cikakken sunanki tare da sunan da aka fi saninki da shi.
Ni sunana Maryam Abdulkarim Sulaiman wacce aka fi sani da Maryam A. Baba ko Maryam Sangandale.
Ko za ki iya fadawa masu karatu dan takaitaccen tarihinki?
Ni Maryam an haife ni a kasar Ghana ne a nan Zango, saboda mahaifina dan kasuwa ne da yake zuwa kasashe fataucin kayan masarufi, nan ya hadu da mahaifiya ta suka yi aure, har Allah ya basu albarkar samun mu ni da Yayana. Kuma shi Baban nawa dan garin Kano ne a karamar hukumar Kura. Bayan ya bar Ghana ya dawo Legas aka haifi kanwata Zainab, daga nan ya zo Kaduna. Kar ki manta na ce miki dan kasuwa ne, ana nan ya dawo garinsa Kanon Dabo ci gari cibiyar Kasuwanci. Tam zaman mu a Kano lokacin mun kara wayo aka saka mu a makarantar Islamiyya Rabi’u Speaking, a nan Unguwar Sani Mainagge da ke Tal’udu. A takaice dai a garin Kanon na yi ‘primary’, ‘secondary,’ ‘college’, har na dan yi aiki da NTA Kano ‘Temporary’ da Freedom Radio da Dala FM.
Me ya ja hankalinki har ki ka tsunduma harkar waka?
Abin da ya ja ra’ayi na shi ne, kallon wasan kwaikwayo na Hausa, kuma sai naga ana waka a cikin sa, sai na ji inada sha’awar ace ni ma ina bada tawa gudunmawar a harkar.
Za ki yi kamar shekara nawa da fara waka?
Shekara ta 26 Ina wannan masana’antar Kannywood din, ina harkar wake-wake na ta fannoni daban-daban a harkar waka kuma a wakance.
Ya gwagwarmayar farawar ta kasance?
Gaskiya an sha gwagwarmaya kam, saboda farkon fara waka ta ban iya bin kida ba, idan za a yi wakar sai da na sha wuya ma kafin na samu a dauke ni ace min zo ki yi wakar, kuma daga makaranta idan na tashi nake zuwa wajen yin wakar.
Ya batun iyaye lokacin da ki ka fara sanar musu kina so ki fara waka, shin kin fuskanci wani kalubale daga gare su?
Lokacin da suka ji na fara waka cewa suka yi, ni da nake karatu kuma meye ya hada ni da waka? Babana ya ce na bari tukunna na kammala abin da ya dora ni akai sannan daga baya na zo da abin da nake son yi. To, kalubalen da na samu a kan hakan daga wajen mahaifina sai ya ce min idan kuma ba zan daina zuwa wajen wakar ba to, ba zan kara fita ba, na zauna a gida tunda shi ba waka ya ce na yi ba, karatu shi ne burin sa da ni. Kwana 3 ban ci abinci ba saboda ya hana ni fita daga gida dan kar na je wajan waka. Sai daga baya mahaifiyata ta ce masa ba na fa cin abinci tun lokacin da ya hana ni fita, shi ne ya yi ta yi min fada ya ce to, shi makaranta ya tura ni ba wajen waka ba, don haka na zo na tafi makaranta amma ban da zuwa wajen waka na ce to, shi ne fa sai lokacin na fara cin abinci to, kin ji kalubalen da na fuskanta daga gidan mu wajen iyayena. Allah ya ji kan babana ya gafarta masa zunubansa ya sa aljannar firdausi ta zama makoma a gare shi.
Ya farkon fara wakar ya kasance?
Kuka na kama yi saboda shi ‘director’ na fim din ya kasance mafadaci ne shi, Dalilin fadan nasa kuma na kasa tafiya da kidan da wakar tare, saboda shi ne farkon yi na ban iya hada su a tare da waka da kidan ba, ba na yi daidai sh ine fa ya kama fada har sai da nayi kuka na ce ba zan yi wakar ba. Sai wanda ya kai ni wajan wato Ahmad Aliyu Tage da Alibaba Yakasai da Yakubu Muhd suka rika ba ni hakuri suna ta rarrashi na, suka ce na zauna a gefe Idan na huce sai na zo na kara yi ai zan Iya haka suka ce kuma a hakan aka yi. Amma fa sai da aka fitar da shi daga wajan, sannan na iyayin wakar kuma ta yi kyau ta yi dadi.
Da wanne mawaki ko mawakiya ki ka fara yin waka, kuma kin fara ne da amshi ko da rubutacciyar wakar da ki ka rubuta?
Tare da Yakubu Muhd da Sani Danja na Fara waka, kuma wakar sune suka rubuta muka rera tare da su, sunan wakar Jinjinjina da bazar mu mazan gari suke takawa. An ce sunan fim din ‘Gobe Da Labari’. To kin ji yadda ta kasance.
Lokacin da za ki fara rubuta waka ta kanki, shin kin samu taimakon wani ko wata, ko kuwa da kanki ki ka rubuta kuma ki ka rera?
Eh, to! akwai wata waka da na rubuta irin wakokin mu na ‘secondary school’ kuma na rera ta babu taimakon kowa ban da wanda ya yi min kidan wakar har nayi ta, kuma ta yi dadi.
Kin yi wakoki sun kai kamar guda nawa?
Cabdijan ban san adadin su ba wallahi, saboda suna da yawa wallahi shekara fa 26 hmmmm.
Ko za ki iya fadowa masu karatu sunayen kadan daga cikin wakokin da ki ka rera ko ki ka rubuta?
Wadanda na rera akwai Sangandale, Leshi Gami Da Shadda, Sanafahna, Masar Bauchi, Sakataye, Taho Taho Dan Yaro kyakykyawa in Maka Tawai, Izzina Nayi Nuni da Kai Sahibina, Rabo Rabo, Samari, Mace Tagari, Tsuntsunbisa Tsurutsuhu, Munshigo da Kafar Dama Industry, Langa Langa da Langaye. Kai da dai sauran su sun fi karfin kirgawa fa hmmm da yawa wallahi.
Akwai mawakiyar da muryarku take kamanceceniya wanda a lokutan baya ake tunanin wakokinki ne, sai kuma a yanzu da ta bayyana ake gane cewa wakokinta ne, me za ki ce akan hakan?
Baiwa ce kowa da yadda Allah ya bashi tashi. Wallahi mutane suna cewa wai kamar ni idan ta yi waka, Amma fa ni ba na jin hakan kuma ita ma na tabbata ba ta jin hakan, saboda kowannen mu yana da yadda yake rerawa wajan salo da sarrafa harshen ma ba iri daya bane wallahi, nata ma har ya fi nawa dadi sosai a nesa ma ba nan kusa ba saboda babu gami ko kadan ta fi ni iya waka gaskiya Fatima Khalil baiwar Allah muryar ta akwai dadi sosai wallahi ba kamar tawa ba. Allah ya kara basira da hazaka ‘yar’uwa [jinjina].















Discussion about this post