Fitaccen mawaƙin siyasar nan na jam’iyyar APC, Dauda Kahutu Rarara, ya tsallake rijiya da baya, bayan wasu fusatattun matasa sun yi yunƙurin kai masa hari a Abuja, a yayin da yake ƙoƙarin rera waƙar yabon Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya auku ne a wani taro da aka gudanar a babban birnin tarayya Abuja, inda mawaƙin ya hau kan dakalin taron da nufin nishaɗantar da mutane da sababbin waƙoƙinsa na siyasa, sai dai matasan da ke wurin suka yi masa ca tare da fara ihu da nuna rashin amincewa da waƙoƙin.
Fusatattun matasan sun ƙi amincewa da kalaman yabon da mawaƙin ke yi wa shugaban ƙasa da gwamnatin tarayya, suna masu nuna ɓacin ransu dangane da halin ƙuncin rayuwa da tsadar kayan masarufi da al’umma ke ciki a halin yanzu, lamarin da ya kusan rikiɗe wa zuwa duka kafin jami’an tsaro su shiga tsakani.
Jami’an tsaron da ke wurin sun yi gaggawar kuɓutar da Rarara tare da kange shi domin fitar da shi daga harabar taron cikin tsaro, a daidai lokacin da dandazon matasa ke ci gaba da ihun adawa da nuna rashin jin daɗinsu.
Wannan lamari dai ya ja hankalin masu amfani da kafafen sada zumunta, inda masana ke ganin hakan a matsayin wata alama ta sauyin yanayin siyasa da kuma yadda matsin tattalin arziƙi ke sanya masu goyon bayan manufofin gwamnati fuskantar matsin lamba daga al’umma a bainar jama’a.














