Malaman jami’o’i da ma’aikatan da ba malamai ba na dukkan jami’o’in mallakar Gwamnatin Jihar Legas sun tsunduma cikin yajin aikin sai-baba-ta-gani, sakamakon rashin cika musu buƙatun da suka daɗe suna nema daga gwamnatin jihar.
Shugaban Kwamitin Haɗin Gwiwa na Ƙungiyoyin Ma’aikatan (JAC), Farfesa Ibraheem Bakare, ne ya sanar da matakin a madadin ƙungiyoyin, inda ya bayyana cewa ma’aikatan sun nuna matuƙar haƙuri tare da bin dukkan hanyoyin tattaunawa na lumana, amma rashin cimma matsaya ya tilasta musu ɗaukar wannan mataki bayan an ƙure haƙurinsu.
Daga cikin manyan buƙatun da ƙungiyoyin ke nema akwai aiwatar da cikakkiyar yarjejeniyar shekarar 2025 tsakanin Gwamnatin Tarayya da ƙungiyoyin a dukkan jami’o’in jihar guda huɗu, biyan basussukan da suka taru na watanni tara daga Janairu zuwa Satumba na shekarar 2026 a lokaci guda, da kuma tabbatar da cewa ba a cire haraji a kan alawus-alawus ɗin da aka amince da su ba.
Haka kuma, ma’aikatan na neman a aiwatar da alawus na musamman na kashi 15 cikin 100 domin rage raɗaɗin tsadar rayuwa a Legas (Lagos Factor), tare da cika alƙawurran da Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya ɗauka a baya, ciki har da ƙarin albashi na kashi 20 cikin 100 da ya yi a shekarar 2023 da kuma samar da manyan motocin bas na “Marcopolo” guda biyar domin sufurin ɗalibai da ma’aikata.
Ƙungiyoyin sun gargaɗi cewa shiga tsakani na gaggawa daga Gwamna Sanwo-Olu ne kaɗai zai iya shawo kan lamarin tare da hana dakatar da harkokin karatu da gudanar da ayyuka a jami’o’in jihar baki ɗaya.














