Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sake jaddada matsayar gwamnatinsa kan cire tallafin man fetur, yana mai bayyana cewa duk wani nau’in tallafi da ke cinye albarkatun ƙasa ba tare da haifar da ci gaba mai ɗorewa ga al’umma ba, cikas ne ga haɓakar tattalin arziƙi da ya zama dole a kawo ƙarshensa.
A yayin da yake fayyace manufofin gwamnatinsa kan harkokin tattalin arziƙi, Shugaba Tinubu ya nuna cewa tsohon tsarin tallafin man fetur ya kasance wata babbar kafa da ke zuƙe kuɗaɗen shigar ƙasa tare da ciyar da ƴan tsirarun dillalai da masu fasa-ƙaurin mai zuwa maƙwabtan ƙasashe gaba, a maimakon talakawan da ake iƙirarin ana yi dominsu.
Shugaban ya bayyana cewa gwamnatinsa ta yanke shawarar dakatar da ɓarnatar da biliyoyin kuɗaɗe a kan tallafin mai ne domin karkatar da albarkatun ƙasar zuwa fannonin da za su amfani ƴan ƙasa kai-tsaye. Ya kafa misali da ƙaddamar da shirin bayar da lamunin karatu ga ɗalibai (NELFUND), shirin sauya fasalin sufuri zuwa amfani da iskar gas (CNG), da tallafa wa ɓangaren noma da kiwon lafiya.
Tinubu ya jaddada cewa babu wata ƙasa da za ta iya gina ingantaccen tattalin arziƙi idan tana ci gaba da binne kuɗaɗenta a cikin tallafin da ba ya ƙara wa ƙasa komai a fannin samar da ababen more rayuwa.
Ya buƙaci ƴan Nijeriya da su ci gaba da nuna haƙuri da fahimta kan matakan sauye-sauyen da ake ɗauka, yana mai tabbatar da cewa ƙalubalen da ake fuskanta na wucin-gadi ne kuma zai share fagen samun ɗorewar tattalin arziƙi a nan gaba.














