ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Wasu Sassan Birnin Abuja Na Fuskantar Barazanar Rusau

by Rabi'u Ali Indabawa
2 months ago
Abuja

An rushe wasu cibiyoyin kasuwanci, ciki har da sanannen shagon Pizza da wasu shagunan sayar da kayan hadin wayoyin salula, a yankin Area 11 da ke Garki, a Babban Birnin Tarayya (Abuja), a ranar Talata.

Abuja Metro ta ruwaito cewa rushe-rushen sun biyo bayan zargin cewa wani sabon mai harkar gine-gine ya mallaki fili da wasu gine-gine na kashin kansa.

Aikin rusau cin ya fara ne da misalin karfe 10:00 na safe, inda aka kawo manyan injinan rushe gine-gine domin gudanar da aikin.

ADVERTISEMENT

Lokacin da wakilan Abuja Metro suka isa wurin da misalin karfe 1:30 na rana, sun samu ana ci gaba da rushe gine-ginen, yayin da ba a tabbatar da ko wane ne mai filin ba.

An ga ma’aikata da masu shaguna cikin gaggawa suna kwashe kujeru, tebura, kayan hadin wayoyi, kayan aiki da sauran kayayyaki masu daraja kafin a rushe gine-ginen.

LABARAI MASU NASABA

Karuwar Farin Jinin Gwamna Umaru Bago A Siyasar Jihar Neja

Kyakkyawan Tsarin Laken Asiri Zai Dakile Shirin Magudin Zabe A Nijeriya —Mohammed

Wasu daga cikin wadanda abin ya shafa sun shaida wa wakilan jaridar cewa mai filin ya ba su wa’adin watanni shida su fice daga wurin, kuma wa’adin ya kare tun watanni da suka gabata.

A halin da ake ciki, wasu ma’aikatan shagon Pizza, wadanda suka nemi a boye sunayensu, sun bayyana rushewar a matsayin abin takaici, tare da nuna damuwa kan makomar ayyukansu.

Sun ce rusau din ya zo musu ba zato ba tsammani, kuma wasu daga cikinsu na fargabar shiga cikin jerin masu zaman banza da marasa aikin yi a Nijeriya.

Wasu ma’aikatan sun kuma bayyana cewa reshen shagon yana daukar sama da ma’aikata 20 aiki, tare da nuna fatan cewa kamfanin zai mayar da su aiki zuwa wasu rassansa da ke fadin Babban Birnin Tarayya (FCT).

Kokarin jin ta bakin mahukuntan shagon Pizza da sauran kasuwancin da abin ya shafa bai yi nasara ba, domin jami’ansu sun ki yin magana da manema labarai.

Haka kuma, Abuja Metro ta kasa samun amsa daga sabon mai filin, wanda ake zargin shi ne ke gudanar da aikin rushewar.

Mai magana da yawun Sashen Kula da Tsare-tsaren Gine-gine na Babban Birnin Tarayya (FCDCD) ya shaida wa Abuja Metro cewa hukumar ba ita ce ta gudanar da aikin rushewar ba.

Abuja
Rabi'u Ali Indabawa
+ postsBio
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ƙungiya Ta Gudanar Da Zaɓen Sabbin Shugabanninta A Abuja
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Jihar Katsina Da UNICEF Sun Ceto Rayuwar Yara Ta Hanyar Samar Da Abinci Mai Gina Jiki
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Yadda Tinubu Ya Kashe Naira Biliyan 37.64 A Tafiye-tafiye
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ta’addaci: Mutum 14,500 Sun Bace A Arewa Maso Gabas

MASU ALAKA

Gwamnatin Neja Ta Bayar Da Umarnin Kawo Karshen Matsalar Tsaro
Rahotonni

Karuwar Farin Jinin Gwamna Umaru Bago A Siyasar Jihar Neja

September 5, 2026
Kyakkyawan Tsarin Laken Asiri Zai Dakile Shirin Magudin Zabe A Nijeriya —Mohammed
Rahotonni

Kyakkyawan Tsarin Laken Asiri Zai Dakile Shirin Magudin Zabe A Nijeriya —Mohammed

September 5, 2026
Jihar Katsina Da UNICEF Sun Ceto Rayuwar Yara Ta Hanyar Samar Da Abinci Mai Gina Jiki
Rahotonni

Jihar Katsina Da UNICEF Sun Ceto Rayuwar Yara Ta Hanyar Samar Da Abinci Mai Gina Jiki

September 5, 2026
Next Post
Direba Ya Hallaka Ɗalibar Jami’ar Kiwon Lafiya Ta Azare, Ya Gudu

Direba Ya Hallaka Ɗalibar Jami'ar Kiwon Lafiya Ta Azare, Ya Gudu

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.