ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Wang Yi Ya Yi Kira Da A Kara Karfafa Hadin Gwiwa Tsakanin Kasashe Domin Habaka Ci Gaban Duniya Gaba

by Sulaiman and CGTN Hausa
1 month ago
Wang

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Ministan harkokin wajen kasar Sin, Wang Yi, ya halarci wani taro na manyan jami’ai da aka shirya bisa cika shekaru biyar da gabatar da shawarar bunkasa ci gaban duniya (GDI), a birnin Beijing jiya Talata, inda ya yi kira ga kasashe da su ci gaba da riko da tambarin samun bunkasa da karfafa hadin gwiwa, kana su yi aiki tare domin gina makoma mai kyau.
Wang, wanda har ila yau memba ne a ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na Jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin (JKS), ya ce a yayin da ake fama da yanayin kasa da kasa mai sauyawa da ke cike da rudani, muhimmancin shawarar ta GDI ya kara fitowa fili. Yana mai kira ga kasashe da su kara himmar daidaita tsakanin shawarar GDI da ajandar samar da ci gaba ta Majalisar Dinkin Duniya.

Ya gabatar da shawarwari guda hudu domin inganta habaka ci gaban duniya. Na farko, Wang ya yi kira da a karfafa goyon bayan juna da hadin kai domin samar da yanayi na zaman lafiya don samun bunkasa. Na biyu, ya bukaci kasashe su yi aiki kafada-da-kafada domin hanzarta aiwatar da ajandar ci gaba mai dorewa ta shekarar 2030. Ya ce, kasar Sin za ta ci gaba da samar da karin albarkatu na ci gaba ga kasashe masu tasowa da kuma taimakawa wajen magance rashin daidaito da karancin abubuwan da ake bukata a bangaren ci gaban duniya.

Na uku kuwa, Wang ya yi kira da a bude kofa, a yi koyi da juna, da kuma samar da ci gaba ta hanyar kirkire-kirkire. Ya ce kasar Sin a shirye take ta zurfafa hadin gwiwa da dukkan bangarori wajen taimaka wa kasashe masu tasowa ta fuskar cin gajiyar sabbin damammaki da kuma magance kalubalen da ke tasowa. Na hudu, ya jaddada muhimmancin yin riko da tsarin damawa da mabambantan bangarori da kuma inganta jagoranci a duniya.

ADVERTISEMENT

Yayin da yake nuni da cewa ba za a iya raba ci gaban kasar Sin da duniya ba, kuma shi kansa ci gaban duniya ma yana bukatar gudummawar kasar Sin. Wang ya jaddada cewa, duk irin yadda yanayin kasa da kasa ya sauya, kasar Sin za ta ci gaba da sauke nauyin da ya rataya a wuyanta a matsayinta na babbar kasa, tare da sada ci gabanta da na kasashen duniya bai-daya, da kuma taka rawar gani a matsayin mai karfafawa da kuma ba da gudummawa ga ci gaban duniya. (Mai Fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)

Wang
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara
  • Sulaiman
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • Sulaiman
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • Sulaiman
    ‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna
Wang
CGTN Hausa
+ posts Bio
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

MASU ALAKA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
Daga Birnin Sin

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
Daga Birnin Sin

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi
Daga Birnin Sin

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Next Post
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Sojoji Sun Daƙile Yunƙurin Garkuwa da Mutane, Sun Ceto Shugaban Kwalejin Tarayya A Zamfara

LABARAI MASU NASABA

Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.