ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Sojoji Sun Daƙile Yunƙurin Garkuwa da Mutane, Sun Ceto Shugaban Kwalejin Tarayya A Zamfara

by Sulaiman
1 month ago
Zamfara

Dakarun Sojin Shiyya 2 na Rundunar Haɗin Gwiwa ta Operation FANSAN YAMMA sun daƙile wasu yunƙurin garkuwa da mutane tare da ceto Shugaban Kwalejin Fasaha ta Tarayya da ke Kaura Namoda, Dakta Aminu Yusuf, da wasu mutane da dama a wasu hare-hare daban-daban da aka kai a Jihar Zamfara.

Rundunar sojin ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da Jami’in Yaɗa Labarai na ‘Operation FANSAN YAMMA’, Laftanar Kanal Aliyu Danja, ya wallafa a shafinsa na X a ranar Talata.

Sanarwar ta ce, harin farko ya faru ne da sanyin safiyar ranar 28 ga Yuli, lokacin da dakarun suka amsa kiran gaggawa kan wani harin da ‘yan ta’adda suka kai a yankin Titin Tsohon Tasha da ke Ƙaramar Hukumar Kaura Namoda.

ADVERTISEMENT

A cewar Danja, maharan sun kutsa cikin gidan shugaban kwalejin, inda suka kashe jami’in tsaronsa tare da jikkata wani mazaunin gidan, kafin su yi yunƙurin yin garkuwa da Dakta Aminu Yusuf da iyalansa.

Ya ce, “Dakarun sun isa wurin cikin gaggawa tare da fafatawa da ‘yan ta’addan, lamarin da ya tilasta wa ‘yan ta’addan tserewa tare da barin waɗanda suka yi ƙoƙarin yin garkuwa da su. An ceto shugaban kwalejin da iyalansa cikin ƙoshin lafiya ba tare da sun ji rauni ba.”

LABARAI MASU NASABA

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

Kakakin rundunar ya ƙara da cewa a wani samame da aka gudanar a wannan rana, dakarun da ke sintiri da dare sun amsa wani kiran gaggawa daga al’ummar Tungan Dorawa da ke ƙauyen Barkeji, inda ‘yan ta’adda ke ƙoƙarin yin garkuwa da mazauna yankin.

Ya ce duk da cewa, babu hanya mai kyau dake kaiwa ga al’ummar yankin, amma duk da haka, jami’an sun ci gaba da bibiyar maharan, inda suka fafata da su, tare da daƙile yunƙurin yin garkuwa da mutanen yankin.

Zamfara
Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi
  • Sulaiman
    Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara
  • Sulaiman
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • Sulaiman
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

MASU ALAKA

Sojoji
Manyan Labarai

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Ballon D'or
Manyan Labarai

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

September 8, 2026
Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue
Manyan Labarai

Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue

September 8, 2026
Next Post
Firaministan Sin Ya Jaddada Bukatar Karfafa Matakan Rigakafin Abkuwar Ibtila’i Da Daukar Matakan Gaggawa

Firaministan Sin Ya Jaddada Bukatar Karfafa Matakan Rigakafin Abkuwar Ibtila’i Da Daukar Matakan Gaggawa

LABARAI MASU NASABA

Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.