ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Saturday, July 25, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Wannan Hakki Na Tushe Yana Da Matukar Muhimmanci

by CGTN Hausa and Sulaiman
1 month ago
DONGNING@FOTO

DONGNING@FOTO

Mene ne hakkin dan Adam na tushe? Sanin kowa ne, kafin a yi magana kan hakkin wani mutum, dole ne a ba shi damar rayuwa. Sa’an nan idan an samu wata karuwa bisa wannan hakki na tushe, to, zai kai matsayin jin dadin rayuwa, batun da ya shafi hakkin mutum na raya kai.

Ko da yake wannan tunani ba mai sarkakiya ba ne, kana tun tuni Majalisar Dinkin Duniya ta tabbatar da cewa hakkin raya kai na daya daga cikin hakkokin tushe na dan Adam, amma har yanzu wasu kasashen dake yammacin duniya suna tsayawa kan ra’ayinsu na mai da hakkin siyasa a matsayin hakkin dan Adam na tushe. Sun kaskanta matsayin hakkin raya kai da gangan, da neman mallakar ikon yanke shawara kan ma’anar hakkin dan Adam, gami da tilasta wa sauran kasashe karbar ra’ayinsu dangane da hakkin dan Adam. To, wannan shi ne dalilin da ya sa kasar Sin, da kasashen Afirka, da sauran kasashe masu tasowa na yankuna daban daban, ke kokarin jaddada matsayin hakkin raya kai a matsayin hakkin dan Adam na tushe.

A wajen wani taron dandalin tattauna batun daidaita al’amura masu alaka da hakkin dan Adam a duniya, da ya gudana a birnin Beijing na kasar Sin a kwanan baya, na ji yadda jami’ai da masana na kasashe daban daban suka tattauna kan muhimmancin kare hakkin raya kai, da na daukar ra’ayi mai dacewa kan batun hakkin dan Adam:Inda tsohon shugaban kasar Iraki, Abdulatif Rashid, ya ambaci wahalhalun da kasarsa ta jure sakamakon yakin da ya ki ci ya ki cinyewa. A cewarsa, “Iraki ta san tasirin rushewar tushen raya kasa, kana ta san wahalar sake gina wannan tushe.” Ban da haka, ya ambaci Falasdinu da har yanzu ke fama da hare-haren da ake kai mata. Ya ce, cikin shekaru gommai da suka wuce, an dade ana keta hakkin raya kai na Falasdinawa, wanda ya kasance rauni a zukatan mutane masu sanin-ya-kamata.

ADVERTISEMENT

Duk a wajen taron dandalin, an nuna wani misali da ya shafi kokarin kare hakkin raya kai na dan Adam. Luogu Youge, wani jami’i ne dake aiki a kauyen Sanhe dake lardin Sichuan na kasar Sin, wanda ya yi bayani kan yadda aka kare hakkin dan Adam a kauyensa, ta hanyar raya tattalin arziki. Ya ce, ta hanyar aiwatar da matakan rage talauci, da kaurar da matalauta daga muhallin da bai dace da bukatar raya tattalin arziki ba, ya zuwa shekarar 2020, an shigar da iyalai 151 masu karamin karfi na kauyen Sanhe cikin sabbin gidajen da gwamnati ta gina musu, inda ake samun ruwan famfo, da wutar lantarki, da hidimar yanar gizo ta Intanet, da dakin girki da ban daki na zamani. A ganin Luogu Youge, hakkin dan Adam ya tabbata ne bisa sabbin gidaje da mutanen suka samu, da karuwar kudin shiga, da tsaro da jin dadin rayuwar mutanen kauyensa.

A nasa bangare, shehun malami mai suna Zhang Weiwei, dake aiki a jami’ar Fudan ta kasar Sin, ya yi tsokaci kan ra’ayin kasar Sin dangane da hakkin dan Adam. Ya ce, an samu asalin tunanin Sinawa a wannan fanni shi ne daga al’adun kasarsu na gargajiya, wanda ya shafi dimbin abubuwa, musamman ma wasu bangarori guda 3.

LABARAI MASU NASABA

Yadda Kasar Sin Ta Samar Da Ci Gaba Na Bai Daya

Sin Tana Son More Damammakin Fasahar AI a Maimakon Babakere a Wannan Bangare Da Kasashen Yamma Suka Dade Suna Yi

Na farko shi ne ra’ayin lura da daukacin fannonin wani aiki, wanda ya sa gwamnatin kasar Sin ke kokarin tabbatar da hakkin al’umma na fannoni daban daban, kamar su tattalin arziki, da siyasa, da al’adu, da more muhalli mai nagarta, da dai sauransu.

Na biyu shi ne tunanin kallon moriyar jama’a a matsayin tushen ci gaban kasa, wanda ya sa dukkan manufofin kasar ke shafar niyyar kyautata rayuwar jama’a.

Kana na uku shi ne tunanin daukar taikamaiman matakai, wanda ya sa ake aiwatar da shirye-shiryen raya hakkin dan Adam a kasar yadda ake bukata.Ra’ayin Farfesa Zhang na tabbatar da ra’ayin da ya shafi hakkin dan Adam bisa al’adun gargajiya na wata kasa, ya samu amincewa daga wasu jami’an kasashen Afirka.

Inda ministan kasar Guinea-Bissau mai kula da batun shari’a da hakkin dan Adam, Joao Vieira, ya ce yayin da ake kula da batun hakkin dan Adam a duniya, dole ne a nuna hakuri, da dora muhimmanci kan batun raya kasa.

A cewarsa, kowace kasa na da ikon neman hanyar raya kai bisa yanayin da take ciki, bisa tushen ka’idojin kundin tsarin Majalisar Dinkin Duniya da dokokin kasa da kasa. Kana Crispin Kaheru, mamban kwamitin kare hakkin dan Adam na kasar Uganda, ya ce, yayin da ake kula da al’amura masu alaka da hakkin dan Adam na duniya, to kar a nuna cewa wani tsari ya fi saura, ko kuma a ba wata kasa damar shawo kan al’amuran sauran kasashe. Kamata ya yi, a tabbatar da daidaito, da hadin kai, da girmama juna, da koyi da juna, in ji Mista Kaheru.

Tattaunawar da aka yi wajen taron dandali na wannan karo ta nuna cewa, jami’ai da masana na kasashe masu tasowa daban-daban sun cimma matsaya daya, kan batun amincewa da hakkin raya kai a matsayin daya daga cikin hakkokin dan Adam na tushe, da girmama ra’ayin kowace kasa da ya shafi hakkin dan Adam. Sai dai me ya sa har yanzu wasu kasashen dake yammacin duniya ke ci gaba da kin yarda da ra’ayin kasashe masu tasowa dangane da hakkin dan Adam? A ganin Grigorii Lukiantsev, wani jami’in kasar Rasha mai kula da harkokin waje, ko da yake wasu kasashen yamma suna fakewa da dalilin harkar shari’a wajen kaskanta matsayin hakkin raya kai na dan Adam, a hakika, suna neman yi wa kasashe masu tasowa tarnaki, a kokarinsu na neman samun ci gaba a fannonin siyasa da tattalin arziki.

Wasu masana kuma sun ce, wadannan kasashen dake yammacin duniya na kaucewa daukar nauyin samar da taimako ga sauran kasashe a fannin raya tattalin arziki, da neman yin babakere kan tunani mai alaka da hakkin dan Adam, ta yadda za su iya ci gaba da siyasantar da hakkin, da tsoma baki cikin harkokin gidan sauran kasashe. Haka zalika, suna neman kare wani tsarin tattalin arziki na duniya maras adalci, ganin yadda tsarin ke haifar musu da moriya a-kai-a-kai.

Ko da yake Majalisar Dinkin Duniya ta gabatar da sanarwar kare hakkin raya kai kusan shekaru 40 da suka wuce, ya kamata har yanzu mu ci gaba da jaddada cewa, matsayin hakkin raya kai na daya daga cikin hakkokin dan Adam na tushe.

Kare wannan hakki yana da matukar ma’ana ga kasashe masu tasowa, saboda zai ba su damar kare ikon mulkin kai, da zabar hanyar raya tattalin arziki da ta dace da yanayin da suke ciki, da tabbatar da tsaro da jin dadin rayuwar al’ummunsu, da mai da tsarin kasa da kasa ya zama mai adalci da daidaito. (Bello Wang)

Hakki
CGTN Hausa
+ posts Bio
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    An Zartas Da Sanarwar Chengdu A Taron Ministocin Kungiyar APEC Kan Harkar Raya Fasahohin Dijital Da AI
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Sin Ta Kara Kamfanoni 14 Na Tarayyar Turai Cikin Jerin Wadanda Aka Hana Fitar Masu Da Kaya
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Yadda Kasar Sin Ta Samar Da Ci Gaba Na Bai Daya
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Wani Dalilin Da Ya Sa Al’Ummar Afirka Ke Kaunar Kasar Sin Shi Ne Yadda Take Kokarin Zuba Musu Jari
Hakki
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    An Karrama Masana Ilimin Lissafi Na Kasar Sin Da Lambobin Yabo Na Fields Medal
  • Sulaiman
    Ta Da Zaune Tsaye Da Philippines Ta Yi A Teku Ba Zai Lalata Dangantakar Hadin Gwiwar Sin Da ASEAN Ba
  • Sulaiman
    An Zartas Da Sanarwar Chengdu A Taron Ministocin Kungiyar APEC Kan Harkar Raya Fasahohin Dijital Da AI
  • Sulaiman
    Sin Ta Kara Kamfanoni 14 Na Tarayyar Turai Cikin Jerin Wadanda Aka Hana Fitar Masu Da Kaya

MASU ALAKA

Yadda Kasar Sin Ta Samar Da Ci Gaba Na Bai Daya
Ra'ayi Riga

Yadda Kasar Sin Ta Samar Da Ci Gaba Na Bai Daya

July 24, 2026
Sin Tana Son More Damammakin Fasahar AI a Maimakon Babakere a Wannan Bangare Da Kasashen Yamma Suka Dade Suna Yi
Ra'ayi Riga

Sin Tana Son More Damammakin Fasahar AI a Maimakon Babakere a Wannan Bangare Da Kasashen Yamma Suka Dade Suna Yi

July 24, 2026
Me Ya Sa Ra’ayin Duniya Ke Karkata Zuwa Sin Yayin da Tasirin Amurka Ke Faduwa?
Ra'ayi Riga

Me Ya Sa Ra’ayin Duniya Ke Karkata Zuwa Sin Yayin da Tasirin Amurka Ke Faduwa?

July 23, 2026
Next Post
‘Yansanda Sun Ceto Mutum 21 Da Aka Sace, Sun Kwato N4.8m Kuɗin Fansa

’Yansanda Sun Ceto Yaro Mai Shekara Shida Da Aka Sace, Sun Cafke Wanda Ake Zargi A Borno

LABARAI MASU NASABA

An Karrama Masana Ilimin Lissafi Na Kasar Sin Da Lambobin Yabo Na Fields Medal

An Karrama Masana Ilimin Lissafi Na Kasar Sin Da Lambobin Yabo Na Fields Medal

July 24, 2026
Ta Da Zaune Tsaye Da Philippines Ta Yi A Teku Ba Zai Lalata Dangantakar Hadin Gwiwar Sin Da ASEAN Ba

Ta Da Zaune Tsaye Da Philippines Ta Yi A Teku Ba Zai Lalata Dangantakar Hadin Gwiwar Sin Da ASEAN Ba

July 24, 2026
Jadawalin INEC:Kotun Daukaka Kara Ta Kassara Fatan Jam’iyyu Da ‘Yan Siyasa

Jadawalin INEC:Kotun Daukaka Kara Ta Kassara Fatan Jam’iyyu Da ‘Yan Siyasa

July 24, 2026
An Zartas Da Sanarwar Chengdu A Taron Ministocin Kungiyar APEC Kan Harkar Raya Fasahohin Dijital Da AI

An Zartas Da Sanarwar Chengdu A Taron Ministocin Kungiyar APEC Kan Harkar Raya Fasahohin Dijital Da AI

July 24, 2026
NNPP Za Ta Kwace Mulki A Jihar Imo – Kwankwaso

Jam’iyyar NDC Ta Shirya Tsaf Domin Kafa Gwamnati A 2027 —Kwankwaso

July 24, 2026
Sin Ta Kara Kamfanoni 14 Na Tarayyar Turai Cikin Jerin Wadanda Aka Hana Fitar Masu Da Kaya

Sin Ta Kara Kamfanoni 14 Na Tarayyar Turai Cikin Jerin Wadanda Aka Hana Fitar Masu Da Kaya

July 24, 2026
Kashim Shettima Ya Mayar Da Martani Kan Tsadar Rayuwa

Kyamar Baki: Shettima Ya Ja Kunnen Gwamnatin Afirka Ta Kudu

July 24, 2026
Yadda Kasar Sin Ta Samar Da Ci Gaba Na Bai Daya

Yadda Kasar Sin Ta Samar Da Ci Gaba Na Bai Daya

July 24, 2026
Hatsin Da Kasar Sin Ta Girbe Da Lokacin Zafin Bana Ya Zarce Tan Miliyan 150

Hatsin Da Kasar Sin Ta Girbe Da Lokacin Zafin Bana Ya Zarce Tan Miliyan 150

July 24, 2026
Wani Dalilin Da Ya Sa Al’Ummar Afirka Ke Kaunar Kasar Sin Shi Ne Yadda Take Kokarin Zuba Musu Jari

Wani Dalilin Da Ya Sa Al’Ummar Afirka Ke Kaunar Kasar Sin Shi Ne Yadda Take Kokarin Zuba Musu Jari

July 24, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.