ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 24, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Xi Jinping: Matasa Ne Suka Kirkiro Dangantakar Sin Da Amurka

by CGTN Hausa and Sulaiman
5 months ago
Amurka

A jiya Lahadi aka kammala rangadi na shirin musayar al’adu da kimiyya da fasaha na matasan Amurka na bana a birnin Chongqing na kasar Sin, wanda ya samu halartar dalibai da malamai 106 daga jami’o’i sama da 20 na Amurka.

Rangadin ya kushi ziyarce-ziyarce a jami’o’i da cibiyoyin bincike na kimiyya da fasaha da wuraren tarihi da sauransu, wanda ke nufin dalibai da malamai ’yan asalin Amurka 106 sun ganewa idanunsu kasar Sin tare da fahimtar al’adu da ci gaban kasar.

Shin mene ne fa’idar irin wannan ziyara?

ADVERTISEMENT

A matsayinsu na kasashe masu karfin tattalin arziki da ma karfin fada a ji a duniya, kowa ya san irin alfanun da za a samu daga kyautatuwar dangantaka tsakanin Sin da Amurka, domin ba su kadai da al’ummominsu ne za su amfana ba, har da sauran sassan duniya.

A baya-bayan nan, shugaban kasar Sin ya aike da wani sakon taya murna albarkacin cika shekaru 55 da kulluwar diplomasiyya tsakanin kasar Sin da Amurka daga wasan Kwallon Tebur watau Ping-Pong Diplomacy, wadda ta share fagen dangantakar kasashen biyu, inda ya ce, “jama’a ne suka gina tushen dangantakar Sin da Amurka, kana matasa ne suka kirkiro makomarta.” Tabbas matasa suna da rawar takawa wajen inganta dangantaka tsakanin kasa da kasa, musamman irin dangantakar da ke tsakanin Sin da Amurka da a kullum ake samun masu neman shafawa Sin bakin fenti da yada karairayi.

LABARAI MASU NASABA

Musk Ya Hango Gagarumin Ci Gaban Mutum-Mutumi Masu Siffar Dan’Adam A Kasar Sin Tare Da Yabawa Da Yadda Kasar Ke Da Ban Sha’awa

Dandalin Al’adu Na Beijing Zai Mayar Da Hankali Ga Batun Gadon Al’adu Da Koyi Da Juna Tsakanin Mabanbantan Wayewar Kai

Hausawa na cewa, gani ya kori ji. Irin wannan musaya za ta taka rawa matuka gaya wajen kyautata fahimtar juna da rage kyama ko wariya da kuma gina alaka mai dorewa tsakanin al’ummomin kasashen. Idan matasa suka hadu, suka yi mu’amala tare, to ba makawa za a samu fahimtar al’adun juna wanda ya zarce ra’ayi na siyasa da suke dauke da shi, haka kuma dama ce ta koyi da juna. Wannan mu’amala ce za ta gina tubalin aminci da abota da saukaka duk wani sabani da ke akwai.

Baya ga haka, dama ce ta musayar ra’ayi a ilimance, lamarin da zai haifar da ingantattun kirkire-kirkire da ci gaba ga duniya baki daya. Mu’amala tsakanin matasa tamkar shuka iri ne da zai girma a ci moriyarsa a nan gaba. Hakika Sin ta yi hangen nesa, na bude kofofinta ga matasan Amurka, domin ba su damar fahimtar kasar da samun ra’ayi na kashin kansu maimakon abun da suke ji da gani a kafafen yada labarai, inda wannan ra’ayi ba zai tsaya a zukatansu ba, domin za su yayata abun da suka gani ga sauran ’yan uwansu da abokan arziki. Fatan ita ce matasan bangarorin biyu su ci gaba da kirkiro kyakkyawar makomar dangantakar kasashen biyu domin gina al’umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya ta Sin da Amurka. (Fa’iza Mustapha)

Amurka
CGTN Hausa
+ posts Bio
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Musk Ya Hango Gagarumin Ci Gaban Mutum-Mutumi Masu Siffar Dan’Adam A Kasar Sin Tare Da Yabawa Da Yadda Kasar Ke Da Ban Sha’awa
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Dandalin Al’adu Na Beijing Zai Mayar Da Hankali Ga Batun Gadon Al’adu Da Koyi Da Juna Tsakanin Mabanbantan Wayewar Kai
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Li Qiang Ya Halarci Bikin Bude Taron Nuna Kwarewar Sana’o’i Na Duniya Na Shekarar 2026
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Yayin Da Taron UNGA Na 81 Ya Zo A Lokacin Da Duniya Ta Shiga Tsaka-mai-wuya…
Amurka
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Sultan Ya Gargaɗi Malaman Addini Kan Kare Masu Cin Hanci Da Rashawa
  • Sulaiman
    ’Yansanda Sun Ƙwato Motoci 52, Sun Kama Masu Laifi 177 A Mako Guda
  • Sulaiman
    Kada Ku Ɗauki Nauyin Aikin Hajji Da Kuɗaɗen Da Aka Sace — Sultan Ga ’Yan Siyasa
  • Sulaiman
    Ya Kamata Kowane Dan Nijeriya Ya Samu Horon Soja – Ministan Tsaro

MASU ALAKA

Musk Ya Hango Gagarumin Ci Gaban Mutum-Mutumi Masu Siffar Dan’Adam A Kasar Sin Tare Da Yabawa Da Yadda Kasar Ke Da Ban Sha’awa
Daga Birnin Sin

Musk Ya Hango Gagarumin Ci Gaban Mutum-Mutumi Masu Siffar Dan’Adam A Kasar Sin Tare Da Yabawa Da Yadda Kasar Ke Da Ban Sha’awa

September 23, 2026
Dandalin Al’adu Na Beijing Zai Mayar Da Hankali Ga Batun Gadon Al’adu Da Koyi Da Juna Tsakanin Mabanbantan Wayewar Kai
Daga Birnin Sin

Dandalin Al’adu Na Beijing Zai Mayar Da Hankali Ga Batun Gadon Al’adu Da Koyi Da Juna Tsakanin Mabanbantan Wayewar Kai

September 23, 2026
Li Qiang Ya Halarci Bikin Bude Taron Nuna Kwarewar Sana’o’i Na Duniya Na Shekarar 2026
Daga Birnin Sin

Li Qiang Ya Halarci Bikin Bude Taron Nuna Kwarewar Sana’o’i Na Duniya Na Shekarar 2026

September 23, 2026
Next Post
Babu Shirin Hana Jam’iyyun Adawa Shiga Zaɓen 2027 – Fadar Shugaban Ƙasa

Babu Shirin Hana Jam’iyyun Adawa Shiga Zaɓen 2027 – Fadar Shugaban Ƙasa

LABARAI MASU NASABA

Musk Ya Hango Gagarumin Ci Gaban Mutum-Mutumi Masu Siffar Dan’Adam A Kasar Sin Tare Da Yabawa Da Yadda Kasar Ke Da Ban Sha’awa

Musk Ya Hango Gagarumin Ci Gaban Mutum-Mutumi Masu Siffar Dan’Adam A Kasar Sin Tare Da Yabawa Da Yadda Kasar Ke Da Ban Sha’awa

September 23, 2026
Zargin Maita: ‘Yansanda Sun Cafke Mutum Huɗu Bisa Hallaka Wani A Bauchi

Zargin Maita: ‘Yansanda Sun Cafke Mutum Huɗu Bisa Hallaka Wani A Bauchi

September 23, 2026
Dandalin Al’adu Na Beijing Zai Mayar Da Hankali Ga Batun Gadon Al’adu Da Koyi Da Juna Tsakanin Mabanbantan Wayewar Kai

Dandalin Al’adu Na Beijing Zai Mayar Da Hankali Ga Batun Gadon Al’adu Da Koyi Da Juna Tsakanin Mabanbantan Wayewar Kai

September 23, 2026
Sultan

Sultan Ya Gargaɗi Malaman Addini Kan Kare Masu Cin Hanci Da Rashawa

September 23, 2026
Li Qiang Ya Halarci Bikin Bude Taron Nuna Kwarewar Sana’o’i Na Duniya Na Shekarar 2026

Li Qiang Ya Halarci Bikin Bude Taron Nuna Kwarewar Sana’o’i Na Duniya Na Shekarar 2026

September 23, 2026
‘Yansanda Sun Kashe Masu Garkuwa Da Mutane 8, Sun Kubutar Da Mutane 3 A Jihar Bauchi

’Yansanda Sun Ƙwato Motoci 52, Sun Kama Masu Laifi 177 A Mako Guda

September 23, 2026
Yayin Da Taron UNGA Na 81 Ya Zo A Lokacin Da Duniya Ta Shiga Tsaka-mai-wuya…

Yayin Da Taron UNGA Na 81 Ya Zo A Lokacin Da Duniya Ta Shiga Tsaka-mai-wuya…

September 23, 2026
Sultan

Kada Ku Ɗauki Nauyin Aikin Hajji Da Kuɗaɗen Da Aka Sace — Sultan Ga ’Yan Siyasa

September 23, 2026
Liu Guozhong Ya Halarci Shagulgulan Bikin Girbi Na Manoman Kasar Sin Na Bana

Liu Guozhong Ya Halarci Shagulgulan Bikin Girbi Na Manoman Kasar Sin Na Bana

September 23, 2026
Basukan Giratuti: Gwamnatin Bauchi Ta Fara Biyan ₦10bn Ga ‘Yan Fansho 1,700

Basukan Giratuti: Gwamnatin Bauchi Ta Fara Biyan ₦10bn Ga ‘Yan Fansho 1,700

September 23, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.