Jiya Juma’a, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bukaci a yi kokarin gudanar da ayyukan bincike da ceto a tsanake, bayan rugujewar bangaren wani tsauni, a wata gunduma dake dab da birnin Chongqing na kasar Sin, lamarin da ya haddasa makalewar mutane a tsakanin baraguzai, yayin da wasu kuma suka bace.
Ibtila’in ya faru ne da misalin karfe 9:10 na safe a ranar Juma’a, agogon kasar Sin, a yankin Hanjia na gundumar Pengshui, inda zabtarewar kasa ta haddasa rushewar gidaje da dama.
Xi ya jaddada bukatar kandagarkin sake abkuwar wani ibtila’i a wurin, da samar da kulawa ga wadanda suka ji rauni, da gudanar da ayyuka na bayan faruwar lamarin yadda ya kamata. Ban da haka ya bukaci a yi kokarin gano musabbabin aukuwar ibtla’in, da daukar darussa daga gare shi, sannan a tantance tare da kawar da barazanar duk wani nau’in ibtila’i da ka iya abkuwa.
Shugban na kasar Sin ya kara da cewa, ya kamata dukkan yankunan kasar da sassa masu ruwa da tsaki su karfafa sa ido kan bangarori da ka iya gamuwa da hadari, da inganta tsarin yin gargadi, don kare rayukan jama’a da kadarorinsu. (Bello Wang)














