Ko shakka babu, tsarin tantance lafiya kafin a kai ga yin aure, yana da matukar amfani a tsanin al’umma.
Ya kamata a lura da cewa, idan aka gano guda daga cikin masu shirin yin aure yana dauke da wannan cuta, ba fa auren ake fasa yi ba, illa kawai dai za a dora shi a kan magani ne na tsawon wani lokaci, sannan kuma da zarar ya warke daga wannan ciwo na hanta, sai a daura auren.
Daga cikin dalilan saukar da shari’a, akwai batun kiyaye lafiya. Saboda da haka, wannan tsari na tantance lafiya kafin aure; ya kamata ya zama wajibi a kan kowa da kowa.
Idan guda daga cikin ma’aurata yana dauke da wannan cuta ta hanta, zai iya harbin aboki ko abokiyar zaman tasa; ba tare da ya sani ba, wannan shi ita ce babbar hikimar yin gwaje-gwaje a tsakanin masu shirin yin aure, kafin su kai ga yi.
Don haka, hanyoyin da ciwon hanta ke yaduwa sun hada da:
1- Musayar yawu ta hanyar sumbatar juna- Ma’ana, ta hanyar sumbatar juna a tsakanin ma’aurata, idan guda daga cikinsu na dauke da cutar, nan da nan dayan shi ma zai kamu da cutar.
2- Gaurayewar jini ko haduwar jini- Haduwar jini, misali; idan wani ya yi amfani da reza ya yanke, dayan ya yi amfani da ita, zai iya kamuwa da cutar, ko kuma wani abu maikama da haka.
3- Bangaren saduwa a tsakanin ma’aurata- A wajen saduwa tsakanin mata da miji, ta hanyar haduwa maniyyi ko maziyyi da sauran makamantansu, wannan cuta za ta samu hanyar shigewa nan take da daya daga cikinsu na dauke da ita.
Don haka, wadannan hanyoyi da aka ambata dukkanninsu na iya faruwa a zamantakewar aure, kamar yadda masana kiwon lafiya suka sanar.
Saboda haka, ya zama wajibi mutane su kiyaye tare da bin ka’idojin wadannan masana, musamman ta fuskar aiwatar da gwaje-gwaje, kafin a kai ga yin aure.
Wajibi ne ka kiyaye tare da kula da lafiyarka da kuma ta iyalinka, domin kuma sai an tambaye ka a kan yadda ka kula da ita. Sannan, yin wannan gwaji ba wani kayan gabas ba ne, duk da cewa; wasu na nuna tsoronsu a fili wajen zuwa a gwada su, wai a cewarsu; suna zaman-zamansu ka da ce; ba su da lafiya.
A nan, irin abin da Bahaushe yake cewa ne, “An gudu, ba a tsira ba”. Don haka, tun wuri kafin ku kai ga yin aure, ku je kai da yarinyar da za ka aura a gwada ku, a tabbatar da kwa dauke da wannan cuta ta hanta.
Haka nan kuma, su ma sauran ma’aurata; da zarar guda daga cikinsu, ya ji alamu ko an tabbatar masa da yana dauke da wannan cuta, ya yi kokarin taimaka wa abokin zaman nasa, ta hanyar zuwa yin gwaje-gwaje da kuma yin rigakafin kamuwa da cutar.
Mutane da dama, ba su san cewa; ana yin rigakafin wannan cuta ba, wanda abu ne da aka jima ana yi; ba lallai sai wanda ya kamu da cutar ba, kowa ma zai iya zuwa a yi masa kamar yadda masu iya magana ke cewa; “Rigakafi ya fi maganai”.













