Yau Juma’a aka gudanar da taron dandalin tattauna kasuwancin makamashi na Sin da Rasha karo na 8 a Vladivostok na Rasha, inda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aike da sakon taya murna ga dandalin.
Cikin sakon, Xi Jinping ya ce a bana ake cika shekaru 30 da kulla dangankatar abota bisa manyan tsare-tsare, da cika shekaru 25 da rattaba hannu kan yarjejeniyar makwabtaka ta kwarai da hadin gwiwar abota tsakanin Sin da Rasha.
Ya ce yayin da ake ganin sauye-sauye masu sarkakiya a yanayin duniya, dangantakar abota bisa manyan tsare-tsare tsakanin Sin da Rasha a sabon zamani ya kai wani babban matsayi, kuma hadin gwiwarsu a fannin makamashi ya haifar da kyawawan sakamako, wanda ya daukaka ci gaba na bai daya ga kasashen biyu da zama misalin hadin gwiwar moriyar juna tsakaninsu.
Shugaba Xi ya kuma nanata cewa, an daidaita tsarin makamashi na duniya, amma kuma damarmaki da kalubale a bangare sun hade da juna. Ya ce a shirye Sin take ta hada hannu da Rasha wajen ci gaba da zurfafa hadin gwiwar makamashi da hada hannu wajen tabbatar da tsarin samar da makamashi cikin kwanciyar hankali ba tare da tangarda ba. (Mai Fassara: Fa’iza Mustapha)














