ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Xi Jinping Ya Tattauna Da Kim Jong Un

by CGTN Hausa and Sulaiman
3 months ago
Xi

Da maraicen yau Litinin 8 ga watan nan, babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, kana shugaban kasar, Xi Jinping, ya tattauna tare da babban sakataren jam’iyyar kwadago ta Koriya kuma shugaban kasar Koriya ta Arewa, Kim Jong Un, a birnin Pyongyang na kasar Koriya ta Arewa.A tattaunawarsu, shugaba Xi ya ce, Sin da Koriya ta Arewa, dukkansu kasashe ne masu bin tsarin gurgurzu da ke karkashin jagorancin jam’iyyar kwaminis.

Ya ce dadadden zumuncin kasashen biyu ya samo asali ne daga akidu da ra’ayoyi da kuma burikansu iri daya, da zumuncin da ke da dogon tarihi da tubalin siyasa mai inganci gami da alaka ta kut da kut.

Kana, zumunta ta zuriya bayan zuriya, da al’umma mai makoma ta bai daya, da taimaka wa juna, su ne salon musamman na dangantakar Sin da Koriya ta Arewa.

ADVERTISEMENT

Ya kara da cewa, duk da sauyawar halin da duniya take ciki, jam’iyyar kwaminis gami da gwamnatin kasar Sin ba za su canza matsayinsu na mayar da hankali sosai wajen inganta zumunci tsakanin kasashen biyu ba, kuma ba za su canza goyon-bayansu ga harkokin gurgurzu na Koriya ta Arewa da ke karkashin shugabancin Kim Jong Un ba, kana ba za su canza kudurinsu na kiyaye muradun kasashen biyu da managarcin yanayin da suke ciki bisa manyan tsare-tsare ba. Shugaba Xi ya kuma bayar da wasu muhimman shawarwari hudu game da bunkasa dangantakar kasarsa da Koriya ta Arewa.

Shi kuwa a nasa bangaren, Kim Jong Un ya ce, zabar Koriya ta Arewa a matsayin wuri na farko da shugaba Xi Jinping ya ziyarta a shekarar da muke ciki, ya shaida yadda kasar Sin take mayar da matukar hankali kan dangantakarta da Koriya ta Arewa, da kuma zumunci mai karfi da ke tsakaninsu, wanda ya karfafa wa Koriya ta Arewa gwiwa sosai.

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Shugaba Kim ya ce, zai ci gaba da ayyana batun raya dangantakar kasashen biyu a matsayin babban sha’ani mafi muhimmanci bisa manyan tsare-tsare, da yin bakin kokari wajen raya dangantakar kasashen biyu har ta zama abar koyi ga dangantakar kasa da kasa, don bayar da gudummawa ga shimfida zaman lafiya da samar da ci gaba a duniya. (Murtala Zhang)

Xi
CGTN Hausa
+ posts Bio
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

    Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa
Xi
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • Sulaiman
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • Sulaiman
    ‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna
  • Sulaiman
    Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

MASU ALAKA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
Daga Birnin Sin

September 8, 2026

Next Post
Zamfara

’Yan Bindiga Sun Sace Dattawan Zamfara 50 Yayin Taron Sulhu A Cikin Daji

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci