ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Friday, October 23, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Xi Ya Gabatar Da Ka’idoji 4 Kan Yadda Bangarori Daban-Daban Za Su Shiga Cikin Aikin Warware Manyan Matsalolin Afrika

by CGTN Hausa
1 week ago
Xi

Yau Talata da rana, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gana da shugaban majalisar ministocin kasar Togo Faure Essozimna Gnassingbe, wanda ke ziyara a kasar Sin. 

Yayin tattaunawar, Xi Jinping ya gabatar da wasu ka’idoji 4 kan yadda bangarori daban-daban za su shiga a dama da su wajen warware manyan batutuwan da ke ci wa Afrika tuwo a kwarya. 

Ka’ida ta farko ita ce, daukaka shugabancin Afrika, watau al’ummar nahiyar ne ya kamata su zama jigon jagorantar harkokinta. 

ADVERTISEMENT

Ka’ida ta biyu, daukaka adalci da gaskiya, watau bangarori masu ruwa da tsaki su kiyaye manufofi da ka’idojin kundin tsarin mulki na MDD da girmama cikakken ‘yanci da ikon kasashe masu ruwa da tsaki. 

Ka’ida ta uku ita ce, inganta dakatar da rikice-rikice da neman zaman lafiya. Ya ce yaki da kakaba takunkumai daga bangare guda, ba za su warware rikice-rikice tsakanin kasa da kasa ba, don haka ya zama wajibi a nacewa martaba juna da tuntubar juna da neman yanayin da zai karbu ga kowa da hakuri da bambance-bambance da fahimta da hakuri da juna.  

LABARAI MASU NASABA

Shugaba Xi Ya Aike Da Sako Ga Dandalin Xiongan Na 2026

MOC: Manufofin Bunkasa Amfani Da Kayayyaki Sun Fadada Kasuwar Cinikayyar Kayayyaki A Kai A Kai A Farkon Watanni 9 Na Bana

Sai ka’ida ta hudu, watau magance alamomi da tushen matsaloli. Ya ce ya kamata a yi kokarin mayar da hankali kan bukatun tsaro na gaggawa yayin da ake tsara hanyoyin samun ci gaba mai dorewa.  

A nasa bangare, Faure Gnassingbe ya ce kasarsa ta amince da muhimman ka’idojin da shugaba Xi Jinping ya gabatar game da hanyoyin da bangarori daban-daban za su bi wajen warware manyan matsalolin Afrika, kuma yana jinjina wa muhimmiyar rawar da Sin ke takawa wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankalin duniya da magance kalubalen duniya bisa hadin gwiwa. 

Baya ga haka, shugabannin kasashen biyu sun sanar da daga darajar dangantakar kasashen Sin da Togo zuwa ta hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha) 

Xi
CGTN Hausa
+ postsBio
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Shugaba Xi Ya Aike Da Sako Ga Dandalin Xiongan Na 2026
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    MOC: Manufofin Bunkasa Amfani Da Kayayyaki Sun Fadada Kasuwar Cinikayyar Kayayyaki A Kai A Kai A Farkon Watanni 9 Na Bana
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Sin: Dole Ne Gyaran Kwamitin Sulhu Ya Kunshi Canza Karfin Wakilcin Kasashe Masu Wadata Fiye Da Kima
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Sin Da Afirka Abokan Tafiya Ne Wajen Inganta Tsarin Jagorancin Duniya

MASU ALAKA

Shugaba Xi Ya Aike Da Sako Ga Dandalin Xiongan Na 2026
Daga Birnin Sin

Shugaba Xi Ya Aike Da Sako Ga Dandalin Xiongan Na 2026

October 23, 2026
MOC: Manufofin Bunkasa Amfani Da Kayayyaki Sun Fadada Kasuwar Cinikayyar Kayayyaki A Kai A Kai A Farkon Watanni 9 Na Bana
Daga Birnin Sin

MOC: Manufofin Bunkasa Amfani Da Kayayyaki Sun Fadada Kasuwar Cinikayyar Kayayyaki A Kai A Kai A Farkon Watanni 9 Na Bana

October 23, 2026
Sin: Dole Ne Gyaran Kwamitin Sulhu Ya Kunshi Canza Karfin Wakilcin Kasashe Masu Wadata Fiye Da Kima
Daga Birnin Sin

Sin: Dole Ne Gyaran Kwamitin Sulhu Ya Kunshi Canza Karfin Wakilcin Kasashe Masu Wadata Fiye Da Kima

October 23, 2026
Next Post
Sana’ar Ƙosai: Remi Tinubu Ta Yi Kira ga Burna Boy da Davido Su Taimaka wa Talakawa

Bai Kamata Yara Mata Su Fasa Zuwa Makaranta Saboda Rashin Kuɗin Sayen Audugar Al’ada Ba — Remi Tinubu

LABARAI MASU NASABA

Shugaba Xi Ya Aike Da Sako Ga Dandalin Xiongan Na 2026

Shugaba Xi Ya Aike Da Sako Ga Dandalin Xiongan Na 2026

October 23, 2026
Real Madrid Na Tattaunawa Da Bellingham Don Tsawaita Kwantiraginsa

Real Madrid Na Tattaunawa Da Bellingham Don Tsawaita Kwantiraginsa

October 23, 2026
MOC: Manufofin Bunkasa Amfani Da Kayayyaki Sun Fadada Kasuwar Cinikayyar Kayayyaki A Kai A Kai A Farkon Watanni 9 Na Bana

MOC: Manufofin Bunkasa Amfani Da Kayayyaki Sun Fadada Kasuwar Cinikayyar Kayayyaki A Kai A Kai A Farkon Watanni 9 Na Bana

October 23, 2026
NLC Ta Gabatar Da Buƙatu 6 Tare Da Barazanar Yajin Aiki A Nijeriya Baki Ɗaya

NLC Ta Gabatar Da Buƙatu 6 Tare Da Barazanar Yajin Aiki A Nijeriya Baki Ɗaya

October 23, 2026
Sin: Dole Ne Gyaran Kwamitin Sulhu Ya Kunshi Canza Karfin Wakilcin Kasashe Masu Wadata Fiye Da Kima

Sin: Dole Ne Gyaran Kwamitin Sulhu Ya Kunshi Canza Karfin Wakilcin Kasashe Masu Wadata Fiye Da Kima

October 23, 2026
Jama’ar Gari Sun Kashe ’Yan Bindiga Sama Da 30 A Wani Gumurzu A Zamfara

Jama’ar Gari Sun Kashe ’Yan Bindiga Sama Da 30 A Wani Gumurzu A Zamfara

October 23, 2026
Sin Da Afirka Abokan Tafiya Ne Wajen Inganta Tsarin Jagorancin Duniya

Sin Da Afirka Abokan Tafiya Ne Wajen Inganta Tsarin Jagorancin Duniya

October 23, 2026

Shugabar Jaridar LEADERSHIP Ta Halarci Bikin Aza Harsashin Cibiyar Ƙirƙire-Ƙirƙire Tare Da Remi Tinubu A Abuja

October 23, 2026
Yaƙin Neman Zaɓe: ’Yansanda Sun Hana Manyan Motoci Shiga Kaduna Gabanin Ziyarar Tinubu

Yaƙin Neman Zaɓe: ’Yansanda Sun Hana Manyan Motoci Shiga Kaduna Gabanin Ziyarar Tinubu

October 23, 2026
An Kai Hare-Haren Makamai Masu Linzami Birnin Riyadh

An Kai Hare-Haren Makamai Masu Linzami Birnin Riyadh

October 23, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.