Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya taya Hakainde Hichilema murnar sake lashe zaben shugaban kasar Zambia. A cikin sakon da ya aikewa shugaba Hichilema a Alhamis din nan, shugaba Xi ya ce, amincewar siyasa na kara zurfafa tsakanin Sin da Zambia, kana hadin gwiwa na hakika tsakanin sassan biyu ya haifar da tarin fa’idoji, a hannu guda kuma, Sin da Zambia suna ci gaba da aiwatar da tsare-tsare, da hadin gwiwa a harkokin kasa da kasa.
Xi Jinping ya kara da cewa, yana dora matukar muhimmanci ga ci gaban dangantakar kasarsa da Zambia, kuma a shirye yake ya yi aiki da shugaba Hichilema, wajen aiwatar da sakamakon taron koli na Beijing na dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da nahiyar Afirka.
Daga nan sai ya sha alwashin hada hannu da shugaban na Zambia, wajen ingiza kawancen gargajiya, da karfafa goyon bayan juna, da ci gaba da daga matsayin hadin gwiwa na cimma moriyar sassan biyu, ta yadda za a kai ga bunkasa cikakkiyar alakar hadin gwiwa, bisa manyan tsare-tsare tsakanin Sin da Zambia zuwa sabon matsayi, tare da samar da babban alfanu ga al’ummun kasashen biyu. (Saminu Alhassan)














