A yau Talata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana cewa, ya kamata a yi cikakkiyar mutunta ‘yancin kai, da tsaro, da kuma kiyaye martabar yankunan kasashen yankin Gabas ta Tsakiya da na Gulf, da tabbatar da tsaron ma’aikata, da sauran wurare, da cibiyoyin dukkan kasashen duniya yadda ya kamata.
Xi ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da Sheikh Khaled bin Mohamed bin Zayed Al Nahyan, yarima mai jiran gado na Abu Dhabi na Hadaddiyar Daular Larabawa, a nan birnin Beijing.
Xi Jinping ya gabatar da shawarwari guda hudu kan karfafa zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin Gabas ta Tsakiya, wadanda suka hada da kiyaye ka’idar zaman tare cikin lumana, da mutunta ka’idar ‘yancin kan kasa, da bin dokokin kasa da kasa, da bin ka’idar daidaiton samun ci gaba da kuma tsaro. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)















Discussion about this post