Fitaccen dattijo a siyasar Nijeriya, Alhaji Tanko Yakasai, ya yi wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu fatan nasara a zaɓen shugaban ƙasa na 2027, yayin da ya halarci ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na APC a Abuja.
Yakasai, wanda ya ce an haife shi a shekarar 1925, ya bayyana hakan ne a ranar Laraba, yayin ƙaddamar da Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na Jam’iyyar APC a Abuja.
Dattijon ya nuna godiyarsa ga Shugaba Tinubu da shugabannin jam’iyyar bisa gayyatar da suka yi masa domin halartar taron, yana mai cewa halartar taron ya ba shi damar sake haɗuwa da tsofaffin abokansa da abokan hulɗarsa a siyasa.
Yayin jawabin nasa, Yakasai ya ce: “Ina kuma son isar da saƙon fatan alheri ga Mai Girma Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, tare da yi masa fatan samun nasara a zaɓe mai zuwa.”
Ya kuma gode wa Allah bisa raya shi har zuwa wannan lokaci, tare da miƙa godiyarsa ga shugaban ƙasa saboda ba shi damar yin jawabi a wajen taron.
Haka kuma, ya yaba wa shugabannin APC bisa yadda suka nuna masa girmamawa da kuma gayyatarsa domin ya kasance cikin mahalarta taron.
Yakasai ya ce, kasancewarsa wanda aka haifa a shekarar 1925, yana da wuya ya samu wani daga cikin mahalarta taron da zai kira sa’a a tsakaninsu.
Ya ce: “Na san cewa a halin yanzu, kasancewata wanda aka haifa a shekarar 1925, ba ni da wanda zan kira sa’a a tsakaninku a nan.”
Dattijon ya kammala jawabin nasa ne da yi wa mahalarta taron fatan alheri tare da addu’ar Allah Ya yi musu albarka.













