ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Tuesday, September 8, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Batun Dawo Da Tallafin Mai Da Atiku Ya Yi Na Ci Gaba Da Tayar Da Kura

by Leadership Hausa
5 days ago
Tallafin

Furuncin da tsohon  mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar shugaban kasa a jam’iyyarsa ta ADC Alhaji Atiku Abubakar ya shelantawa ‘yan Nijeriya cewa, idan an zabe shi, shugaban kasa a 2027, zai maido da tallafin Man fetur da gwamnatin shugaba Bola Tinubu ta cire, daga hauwanta kan Karagar shubancin kasar, furucin, ya bude wani sabon babin tattaunawa tare da tabka, zazzafar mahawara a tsakanin ‘yan kasar, kan wannan batun, da ke cike da sarkakiya.

Bayan wannan furuncin na Atiku, sai dai, tawagarsa ta yada labarai, sun bayyana cewa, Wazirin na Adawama, ya janye wannan furucin na sa, amma a bangaren tsohon shugaban kasar, ya kara nanata matsayarsa, ta cewa, furucinsa, kan batun, na nan daram dam, kuma bai janye shi ba, inda ma ya kara jaddada cewa, zai dawo da tallafin, musamman duba da irin kangin talauci, da cewar, ta jefa rayuwar ‘yan kasar a ciki, musamman talakawa.

Sai dai, ba nan gizon ke yin saka ba, domin tun a baya, wasu ‘yan siyasar kasar, da ke yin takara, na fakewa da Guzuma domin harbin Karsana, ta hanyar yiwa ‘yan kasar Romom baka, inda suke fakewa, da wasu tsararan sauye-sauye da suka jefa rayuwarsu a cikin kunci, cewar za su kawar da su, amma da zarar an zabe su, sai su bijero da wasu dalilai, marasa makama, na cewa, alakawarin da suka yi, a lokacin yakin zabensu, ba mai yuwa bane.

ADVERTISEMENT

Ga yawancin ‘yan kasar, an cire tallafin ne, bisa wasu manufofi, na son rai kawai.

Hatta a kasashen duniya da ake cewa sun ci gaba, gwamnatocin kasashen na kirkiro da sauye-sauyen da za su ragewa ‘yan kasar matsin rayuwa, musamman, ta hanyar samar da tallafi.

LABARAI MASU NASABA

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue

Sai dai, batun a Nijeriya,  ba haka yake ba, musamman saboda yadda cin hanci da rashawa, ya yi katutu a kasar, wanda hakan ke sanyawa, ‘yan kasar da aka yi abin domin su, ba su iya cin gajiyar sauye-sauyen, da gwamnatin ta kirkiro da su.

Misali, a lokacin tsohowar gwamnatin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, ya yi kokarin cire tallafin Man, amma hakan ya faskara, saboda wasu jan wuyan a kasar da ke amfana da tallafin, suka tsorata gwamnatinsa, ta yi watsi da batun.

Haka batun ya ke, a lokacin tsohowar gwamnatin tsohon shugaban kasa marigayi Muhammadu Buhari, wanda duk da irin zafin da yake da shi, a lokacin yana kan Karagar mulkin kasar, shi ma , ya gaza cire tallafin, na Man.

Sai dai, gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu, ta yi hobbasa, ta cire tallafin Man, tare da sauya tsarin, inda hakan ya haifarwa da tattalin arzikin kasar, nakasu da kuma tagayyara rayuwar talakawan kasar, wanda har zuwa yanzu, suke ci gaba da karbar gashi.

A yanzu dai, ‘yan Nijeriya za a iya cewa, na ci gaba da yin rayuwa ne, ba tare da samun kowanne irin tallafi, daga gun gwamnati ba.

A ra’ayin wannan Jaridar, mai yuwa hakan ne ya sanya Atiku Abubakar, ya yi bijiro da wannan furucin na sa, na cewa, idan ya lashe zaben, zai maido da tallafin, na Man fetur, wanda kuma wannan furucin, ya yiwa akasarin ‘yan kasar, musamman talakawa, dadi.

A zahirance, ‘yan Nijeriya ba su iya amfana da manufar cire da tallafin Man, da gwamnatin shugaba Tinubu ta yi ba, sai dai ma, bakar ukuba da cirewar, ta jefa rayuwarsu a ciki.

Akwai alamun tabbacin idan har Atiku ya zama shugaban kasar, zai dawo da tallafin, koda ba dan komai ba, sai domin ya sanya rayuwar ‘yan Nijeriya, a cikin farin ciki.

Duba da cewa, Atiku dan siyasa ne da ya yi fice a kasar nan, ace wannan furucin na sa, ya yi ne kawai, domin yaudarar ‘yan kasar, domin kawai, ya samu damar dafa madafun ikon kasar, hakan da kamar wuya, furucin na sa, ya zama yaudara.

A gafe daya, wani abu da ‘yan Nijeriya ke zargi shi ne, cewa shi ma a Atiku, ba za a iya tsame shi, daga wanzuwar cin hanci da rashawa a kasar ba.

A zahiri, sakon da muke son isarwa a wannan bayanin daga Teburi Edita shi ne, batun na sake dawo da tallafin Man, mai yuwa ba zai yi wani karfi, wajen kokarin samun kuri’un, wadanda suka kai munzalin kada kuri’a a zaben shugaban kasa, na badi ba.

Tuni dai, batun cin hanci da rashawa a kasar, ya riga ya yi tasiri ga tsarin, musamman a tsakanin wadanda ke ci gaba da ci ga gumin talakawan kasar, wanda su kuma ‘yan kasar, suke ci gaba da ji, a jikinsu.

Tallafin
Leadership Hausa
Website |  + postsBio
  • Leadership Hausa
    Karuwar Farin Jinin Gwamna Umaru Bago A Siyasar Jihar Neja
  • Leadership Hausa
    Kyakkyawan Tsarin Laken Asiri Zai Dakile Shirin Magudin Zabe A Nijeriya —Mohammed
  • Leadership Hausa
    Batun Guguwar Kakar Yakin Neman Zabukan 2027 A Nijeriya
  • Leadership Hausa
    Batun Hare-haren Ƴan Bindiga A Wasu Ƙauyukan Kaduna

MASU ALAKA

Ballon D'or
Manyan Labarai

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

September 8, 2026
Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue
Manyan Labarai

Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue

September 8, 2026
2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi
Manyan Labarai

2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi

September 8, 2026
Next Post
Cutar Mashaƙo Ta Ɓarke A Kano, Katsina Da Filato

Cutar Mashako:Yadda Yara Ke Mutuwar Bazata A Jihohin Katsina Da Kano

LABARAI MASU NASABA

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026
Xi Ya Zanta Ta Wayar Tarho Da Firaministan Birtaniya

Xi Ya Zanta Ta Wayar Tarho Da Firaministan Birtaniya

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.