ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ya Kamata Birtaniya Ta Yi Shawarwari Kan Ikon Mallakar Tsibiran Malvinas

by CMG Hausa
4 years ago
Birtaniya

A kwanan nan ne ministan harkokin wajen kasar Birtaniya James Cleverly, ya bayyana cewa, kasarsa da kasar Mauritius, sun riga sun yanke shawarar gudanar da shawarwari kan batun da ya shafi ikon mallakar tsibiran Chagos, da sa ran cimma yarjejeniya a farkon shekara mai kamawa.

An maida irin wannan ra’ayin kasar Birtaniya, a matsayin wani muhimmin matakin da aka dauka, wajen daidaita rikicin ikon mallakar tsibiran Chagos.

  • Sharhi: Kasar Sin Na Son Kara Bude Kofarta Ga Kasashen Duniya

Tsibiran Chagos suna tsakiyar yankin ruwan tekun Indiya, yankuna ne da kasar Mauritius ta mallaka tun asali. A shekara ta 1965, a matsayin wani sharadin da aka gindayawa Mauritius don ta samu ‘yancin kai, kasar Birtaniya ta ware tsibiran Chagos daga Mauritius don su zama “yankunan dake karkashin mulkin Birtaniya a tekun Indiya”, ta kuma ce za ta mayar da su a lokacin da ya dace. Bayan da Mauritius ta samu ‘yancin kai a shekara ta 1968 har zuwa yanzu, ta dade da bukatar Birtaniya da ta maido mata da tsibiran.

ADVERTISEMENT

Kamar batun da ya shafi tsibiran Chagos, batun tsibiran Malvinas, shi ma ya wakana ne a lokacin mulkin mallaka na kasar Birtaniya. A shekara ta 1816, kasar Argentina ta gaji ikon mallakar tsibiran Malvinas, bayan da ta samu ‘yancin kai daga mulkin mallakar kasar Sifaniya, amma Birtaniya ta dauki matakan soja, har ta kwace ikon mallakar tsibiran a shekara ta 1833.

A shekara ta 1965, an zartas da kudiri mai lamba 2065 a wajen babban taron Majalisar Dinkin Duniya, inda aka bukaci kasashen Birtaniya da Argentina, da su daidaita rikici ta hanyar shawarwari. Kana kuma, har sau sama da 30, kwamitin musamman na kawar da matsalar mulkin mallaka na MDD, ya zartas da kudirori don bukatar kasar Birtaniya ta yi shawarwari da kasar Argentina. Amma Birtaniya ta yi biris da haka.

LABARAI MASU NASABA

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

Daga cikin yankuna 17 da har yanzu suke karkashin mulkin mallaka a duniya, akwai guda 10 dake karkashin mulkin Birtaniya. Ba rikicin ikon mallakar tsibiran Chagos kawai ya kamata ta warware ba, kamata ya yi ma ta gudanar da shawarwari tun da wuri tare da Argentina kan batun tsibiran Malvinas.

A wannan karnin da muke ciki, ra’ayin mulkin mallaka, da ra’ayin nuna babakere ba za su samu nasara ba. Dole ne kasar Birtaniya ta daidaita wadannan matsalolin tarihi yadda ya kamata! (Murtala Zhang)

Birtaniya
CMG Hausa
+ postsBio
  • CMG Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cmg-hausa/
    Shugabannin Kasashen Duniya Sun Yi Wa Sin Fatan Alheri A Sabuwar Shekara
  • CMG Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cmg-hausa/
    San Francisco sabon mafarin hadin gwiwar Sin da Amurka ne
  • CMG Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cmg-hausa/
    Xi Ya Halarci Kwaya-Kwaryan Taron Shugabannin Mambobin APEC
  • CMG Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cmg-hausa/
    Shugaban Kasar Sin Ya Gabatar Da Rubutaccen Jawabi Ga Taron Jagororin Masana’antu Da Kasuwanci Na APEC

MASU ALAKA

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna
Daga Birnin Sin

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

September 9, 2026
Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba
Daga Birnin Sin

Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

September 9, 2026
Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa
Daga Birnin Sin

Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

September 9, 2026
Next Post
Duniya Za Ta Dandana Kudar Matakin Da Amurka Ta Dauka

Duniya Za Ta Dandana Kudar Matakin Da Amurka Ta Dauka

LABARAI MASU NASABA

Birtaniya

Jerin Bankuna 32 Da Aka Amince Su Sayar Da Hannun Jarin Matatar Dangote

September 10, 2026
Birtaniya

Uganda Za Ta Fara Fitar Da Man Fetur Zuwa Ƙasashen Waje

September 10, 2026
Cutar Mashaƙo Ta Ɓarke A Kano, Katsina Da Filato

Mashaƙo: Adadin Mutanen Da Suka Rasu Sun Kai 27 A Filato

September 10, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

Wane Ne Dan Shagamu: Su Wane Ne Suka Kashe Shi A Kano?

September 10, 2026
Al’umma Sun Yaba Wa Sojoji Kan Yaƙar ’Yan Bindiga A Zamfara

Al’umma Sun Yaba Wa Sojoji Kan Yaƙar ’Yan Bindiga A Zamfara

September 10, 2026
Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Ɗalibai 2 A Abuja Da Abia

Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Ɗalibai 2 A Abuja Da Abia

September 10, 2026
’Yansanda Sun Kama Wadda Ta Yaɗa Labarin OPay Zai Daina Aiki A Nijeriya

’Yansanda Sun Kama Wadda Ta Yaɗa Labarin OPay Zai Daina Aiki A Nijeriya

September 10, 2026
2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa Kan Haifar Da Rikici A Sakkwato

2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa Kan Haifar Da Rikici A Sakkwato

September 10, 2026
Zabe: Gwamnatin Kano Ta Taƙaita Zirga-zirgar Mutane Da Ababen Hawa

Gwamna Yusuf Ya Umarci Jami’an Tsaro Su Gano Waɗanda Suka Kashe Danshagamu

September 10, 2026
Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

September 9, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.