An ce sharrirruka guda uku ne: Akwai sharrin da ya rataye da addinin mutum, wannan sharrin su ne kamar kafirci, kaman hawa bidio’i da addini bai yarda da su ba, kaman fasikanci, aikata manya manyan laifuka, da sauransu. Waɗannan in suka taru sai su zama babba. Ana cewa, sarkin yawa ya fi sarkin karfi.
Waɗannan su ne sharrikan da suka rataya da addinin mutum.
Sai sharrin da ya rataya da jikin ɗan’Adam. Na daga masifa da ta rataye da jikin sa, kamar rashin lafiya ko tsamin jiki ko rauni da ya samo sanadiyyar faɗa, Allah ya kiyaye, har ya zama jikin ya nakasa ba zai iya yin komai ba, ko kuma kwarauniya ta tsufa, Ko kasala – kana da lafiyan, kana da komai, amma ba zai iya tashi ya yi wani abu na kirki ba. Duk sharri ne da ya rataye da jikin ɗan’Adam. Kasala kenan. Ko kuwa kana da karfin, kana da komai, amma ga ragwontaka, Allah ya zuba ma a cikin zuciya. Shi kenan duk ba zaka iya komai din nan ba. To wannan ma sharri ne da ya rataye da jikin ɗanAdam.
Sharri na uku kuma, shi ne abin da Allah ya bai wa ɗanAdam ta rataye da dukiya. Kamar dukiya, ɗanAdam bai san a taba masa. Kaman rashin lafiyan ƴaƴa. Dole sai ka kai su asibiti, ka fitar da kudin ka. Ko mutuwar ƴaƴa, ko kuwa rashin kudin ma, wannan duk sharri ne da ya rataye da dukiya.
To wai duk in ka ce, “A’uzu billahi minash-shaitanir-rajeem,” Allah ya isar ma wannan. In ka iya ka halarto su gabaki daya. In ma ba zaka iya ba, ka kudure kai dai duk wani sharri ma na shedan ma da duk abin da ya rataye da shedan din ka nemi tsari da Allah da shi. Kuma Allah tabaraka wa ta’ala zai tsare ka a cikin wannan.
Bismillah tana da sirri kuma aya ce a cikin Suratu Fatiha.
Duk da akwai sabani a ciki amma sabanin ba shi da amfani. Bismillah a cikin Fatiha take, yana daga cikin abunda Shehu Ibrahim RA ya kawo mana, ya kafawa nahiyar Afrikan nan, ya mayar da ita kan sunnan manzon Allah SAW, cewa duk in za mu yi sallah sai mun ce “bismillahir rahmanir rahim”.
Haka muka gada. A fiƙihu, mu Malikawa ne, Malikancin Ɗan Ƙasim. Dan Ƙasim kuwa, shi ya karbo Malikanci daga Imam Malik, zuwa Misra, ta nahiyar Afirka, inda ya yaɗa Malikancin sa. Amma Dan Ƙasim ya yi shekara goma rabon sa da Imam Malik, kuma Imam Malik yana raye akan ƙasa, yana fatawa. Abunda Dan Ƙasim ya zo mana da shi, Imam Malik yace, “bismillah, karahiya ce a cikin sallah”. Shi ko karahiya, ita ce kamar abunda Malamai suke fassara da cewa, “yin ta banza, barin ta banza”, sai dai ana cewa, “Dattijo, ya dace ya barta”.
Amma ba wani malami da ya taba cewa, “in kayi karahiya a sallah, sallah ta baci”. Toh abunda Ɗan Ƙasim ya zo da shi kenan.
Amma shi ko Imam Shafi’i a wajen sa, duk mutumin da bai yi bismillah ba a cikin sallah, to ba shi da sallah, sabida hadisan da suke hannun sa.
Toh yanzu Imam Malik yace in kayi, kayi karahiya. Karahiya kuma in kayi ba ta bata sallah ba. Shafi’i shi kuma ya ce, in baka yi ba, ba ka da sallah. Duba da irin wannan fatawoyi biyu, gwara ma kayi kenan. In ma Imam Malik ne da gaskiya, sallah bata baci ba, Karahiya ce kawai kayi a cikin sallah.
Toh haka muka gaji Malikancin Ɗan Ƙasim, cewa “bismillahir rahmanir rahim” karahiya ce a cikin sallah. Ma’ana kace “bismillahir rahmanir rahim, alhamdulillahir rabbil alamin”. Bayan Dan Ƙasim ya baro Imam Malik, Imam Malik ya haɗu da Imamun Nafiu, inda ya tambaye shi, wai me kuka rawaito wajen Annabi ne SAW a bismillah ta cikin sallah? Imamun Nafiu yace, abunda muka rawaito wajen manzon Allah SAW, “al jaharu biha – a bayyana ta”. Ba wai ba’ayi ba, a’a, ai ba wani malamin da ya taba cewa, ba’ayin bismillah a sallah. Illa dai, waɗansu malamai sun ce, a asirta ta, kamar malaman Saudiyya. A mazhabar su ta Hambali. Ba wai ba’ayi bane, amma mu kuma ƴan koyo, shi kenan sai gashi ma duk mun dakatar da karanta ta.
Sabida fatawar Imam Nafiu da Imam Malik ya samu, sai ya dawo da cewa “bismillahir rahmanir rahim”, amma Ɗan Ƙasim yana nan Afirka, ya kafa Malikancin sa da cewa, “salla da bismillah karahiya ce”. Toh haka iyayen mu suka ɗauko, haka kakannin mu suka ɗauko, haka malamai suka ɗauko.
Amma alhamdullilahi, Allah ya kawo mana gausin zamani wanda ya iya mayar da malaman mu na Afirka daga su tashi daga kan furu’a (fiƙihu) su koma usulu (Kitab wa sunnah). Banda Shehu ba wanda ya isa yayi wannan.
Shehu Tijjani wannan abu ya taba shi a zuciya kwarai sosai. Shehu Tijjani Abul Abbas yana cewa, “ina ƙauna wajen Allah, Allah ya bamu wani irin malami mai ilmi wanda zai zo ya reraye mana fiƙhun nan ya zubar da hashwun malamai, wanda ba su da komai sai wuta. Sai dai in Allah ya riskesu da rahamarsa.”
To, Allah ya amshi wannan addu’a, Allah ya tabbatar da addu’ar shi a kan Sheikh Ibrahim Inyass RA.
Hakan na daga cikin abin da Sheikh Ibrahim yayi, ya mayar da shehunnan mu da ke Kano, kamar gidan Salga da suka shahara a fiƙihu zuwa kan Usulu. Babu wanda ya isa ya yi hakan in ba Shehu Ibrahim Inyas ba.
Haka nan, Shehunnan mu na Zariya sai da ya taso da su daga kan furu’u ya mayar da su kan usulu, ya take Katsina, ya take ko wane gari.
Alhamdulillah, yanzu wannan na daga cikin alamun ƴan faila, faɗin “Bismillahi rrahmani rrahim, alhamdulillahirabbil alamin”.
To Alhamdullilahi, “bismillahir rahmanir rahim”, aya ce acikin suratul fatiha.
Fatiha, yana daga cikin girman ta, Allah tabaraka wa ta’ala, ya faɗa wa manzonsa, Annabi Muhammad SAW cewa, ni na baka fatiha da ƙur’ani gabaki daya, (walaƙad ataina ka sab’an minal masani wal ƙur’anal azim).
Ya ishi Suratul Fatiha girma cewa, ita ce uwar littafin ma gabaki daya, ana ce mata “uwar ƙur’ani”.
Manzon Allah yana cewa, “da Allah ya saukar wa Yahudawa Suratul Fatiha, da ba su bata ba. Da Allah ya saukar wa Nasara fatiha da basu bata ba”.
Fatiha tana da falala mai yawa.
Yana daga falalan ta, hadisin da yazo, na “billahillazi la ilaha illa wa”, duk wanda ya rawaito hadisin sai yayi irin wannan rantsuwa, har zuwa ga sayyidina Abubakar, har zuwa ga manzon Allah SAW.
Manzon Allah ya ce, “billahillazi la ilaha illa, na rantse da ubangijin da ba wani ubangiji sai shi, na ji jibrilu yace, ni ma sai da jibrilu ya ce min billahillazi la ilaha illa huwa. Ya ce, jibrilu yace Mika’il ya ce, shima mikail sai da ya ce billahillazi la ilaha illa huwa. Ya ji rabbul izza ya ce, shi ko rabbul izzati sai da ya ce na rantse da girmana da buwaya ta, duk wanda ya karanta fatiha ya haɗa da bismillahi rrahmanirrahim, alhamdulillahir rabbil alamin, ba zan azabtar da shi da wutar jahannama ba.”
Kowa sai da ya ce billahillazi la ilaha illa huwa.
To, mun gode wa Allah, mu Tijjanawa, bayan mun ce “a’u’zubillahi minash shaiɗanir rajim”, kuma sai mun ce bismillahir rahmanir rahim a dukkan cikin azkaran mu, sai mu kawo wannan aya. Sannan, in mun gama fatiha, sai mu hau rukuni na farko, astagfirullah, astagfirullah, ko astagfirullahal azim allazi la ilaha illa huwal ƙayyum.
Istighfari sha’anin sa yana da girma kwarai da gaske.














Discussion about this post