ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, June 25, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yadda Bunkasar Tattalin Arzikin Kasar Sin Ke Samar Da Karin Damammaki Ga Kasashe Masu Tasowa

by CGTN Hausa and Sulaiman
7 months ago
Kasar Sin

Shaidu na hakika da alkaluman da hukumomi masu ruwa da tsaki ke fitarwa na nuna yadda juriyar tattalin arzikin kasar Sin, da kwazon kasar na aiwatar da manufofin bude kofa bisa matsayin koli, suke ta kara samar da damammaki ga sassan kasa da kasa musamman kasashe masu tasowa.

Cikin shekarun baya bayan nan, cinikayyar shige da fice ta kasar Sin na kara bunkasa bisa daidaito. Kazalika, kasar Sin na ta kara samun tagomashi a kasuwanninta na cikin gida, wani mataki da masana da dama ke ganin yana matukar taimakawa kasar wajen bunkasa hada-hadar cinikayya a gida, baya ga sauran huldodin cinikayya da kasar ke yi tare da sassan kasa da kasa. Sakamakon wadannan nasarori ne kuma kasar ta Sin ke samar da damar ingiza ci gaban tattalin arzikin duniya baki daya.

Muna iya cewa, bunkasar kasuwannin cikin gida na kasar Sin, shaida ce dake nuna karfi da tasirin managartan manufofin da kasar ke aiwatarwa. Kamar dai yadda masana kan ce dorewar bunkasar tattalin arzikin ko wace kasa alama ce dake haska yadda kasar za ta iya jure matsi daga waje, tare da ci gaba da goyayya da sauran abokan hulda na duniya.

ADVERTISEMENT

Tuni kasar Sin ta wuce gaba a fannin raya fasahohin kirkire-kirkire, musamman fannoni irinsu kirkirarriyar basira ko AI, da kirar mutum-mutumin inji, da sauran muhimman fasahohin ci gaba na zamani. A daya bangaren, Sin ta yi nisa wajen raya tsarin samar da ci gaba ba tare da gurbata yanayi ba, da cin gajiyar makamashi mai tsafta, da kirar ababen hawa masu amfani da lantarki. Kuma tabbas jagorancinta a wadannan fannoni ya samar da damar rarraba fasahohinta ga sauran kasashe masu tasowa, ta hanyoyi irin su samar da tallafin gina ababen more rayuwa, da musayar ilimi, da bayar da horon sanin makamar aiki, da hadin gwiwar samar da makamashi mai tsafta a kasashe dake sassan duniya daban daban.

A bangaren hadin gwiwar raya kasuwanci da cinikayya ma kasar Sin tana daukar kasashe manya da kanana a matsayin abokan tafiya ba tare da nuna bambanci ba, tana aiki kafada-da-kafada da dukkanin sassa, wajen dakile nuna bambanci a tsarin cinikayyar kasa da kasa.

LABARAI MASU NASABA

Dokar Sin Ta Gurfanar Da Masu Rajin Ballewar Kabilun Kasar Da Ke Kasashen Waje Ta Dace

’Yan Kasuwa Na Kasashen Waje Sun Yaba Wa Yanayin Kasuwanci Na Sin

Wani abun lura ma a nan shi ne yadda a matsayinta na kasa mai tasowa ta farko a tarihin duniya da ta cimma nasarar samun wadata cikin lumana, Sin ta samar da wata taswira mai inganci, wadda sauran kasashe masu tasowa za su iya bi domin raya kansu cikin lumana, kuma karkashin hakan ne take ta fitar da shawarwari na ingiza ci gaban duniya bi da bi, irinsu shawarar raya jagorancin duniya da kasar ta gabatar a baya bayan nan. Shawarar da masharhanta da yawa ke ganin na da ma’anar gaske, wajen ingiza adalci, da daidaito a tsarin cudanyar mabanbantan sassan duniya.

A gani na tun da har kasar Sin ta kai ga gina tsari mai gamsarwa na raya kai bisa salon musamman mafi dacewa da yanayinta, wanda kuma yake ta kara samun karbuwa tsakanin kasashen duniya, a halin yanzu, kasar na kan wani matsayi na rarraba kwarewarta tare da sauran abokan tafiya, musamman kasashe masu tasowa. Wanda hakan kyakkyawan misali ne da dukkanin wata kasa a duniyan nan za ta iya lura da shi, yayin da take kokarin bunkasa kanta gwargwadon yanayin da take ciki.

Tabbas, ci gaban kasar Sin mai ban mamaki ya nunawa duniya cewa, kowace kasa na iya samun ci gaba ba tare da murdiya, muzgunawa wasu sassa, ko nuna karfin iko na siyasa ko tattalin arziki ba, maimakon hakan kasar Sin ta nunawa duniya cewa abu ne mai yiwuwa, a samu ci gaba bisa hadin gwiwar cimma moriya tare, ta yadda za a gudu tare a kuma tsira tare.

Kasar Sin
CGTN Hausa
+ posts Bio
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Dokar Sin Ta Gurfanar Da Masu Rajin Ballewar Kabilun Kasar Da Ke Kasashen Waje Ta Dace
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    ’Yan Kasuwa Na Kasashen Waje Sun Yaba Wa Yanayin Kasuwanci Na Sin
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Dandalin DAVOS Na Bana: Fage Ne Da “Kirkire-Kirkiren Sin” Ya Sadu Da “Kyakkyawan Fatan Afirka”
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Binciken CGTN: Amfanarwa A Aikace Shi Ne Nagartaccen Ma’aunin Tantance Ainihin Kimar Sabbin Fasahohi
Kasar Sin
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Dokar Sin Ta Gurfanar Da Masu Rajin Ballewar Kabilun Kasar Da Ke Kasashen Waje Ta Dace
  • Sulaiman
    ’Yan Kasuwa Na Kasashen Waje Sun Yaba Wa Yanayin Kasuwanci Na Sin
  • Sulaiman
    Yadda Uba Sani Ya Farfaɗo Da Asibitin Da Aka Yi Watsi Da Shi Tsawon Shekaru 40 – Hakimin Makarfi
  • Sulaiman
    Dandalin DAVOS Na Bana: Fage Ne Da “Kirkire-Kirkiren Sin” Ya Sadu Da “Kyakkyawan Fatan Afirka”

MASU ALAKA

Dokar Sin Ta Gurfanar Da Masu Rajin Ballewar Kabilun Kasar Da Ke Kasashen Waje Ta Dace
Daga Birnin Sin

Dokar Sin Ta Gurfanar Da Masu Rajin Ballewar Kabilun Kasar Da Ke Kasashen Waje Ta Dace

June 24, 2026
’Yan Kasuwa Na Kasashen Waje Sun Yaba Wa Yanayin Kasuwanci Na Sin
Daga Birnin Sin

’Yan Kasuwa Na Kasashen Waje Sun Yaba Wa Yanayin Kasuwanci Na Sin

June 24, 2026
Binciken CGTN: Amfanarwa A Aikace Shi Ne Nagartaccen Ma’aunin Tantance Ainihin Kimar Sabbin Fasahohi
Daga Birnin Sin

Binciken CGTN: Amfanarwa A Aikace Shi Ne Nagartaccen Ma’aunin Tantance Ainihin Kimar Sabbin Fasahohi

June 24, 2026
Next Post
Kamfanin CRCC Ya Kammala Shimfida Hanyar Jirgin Kasa A Gadar Layin Dogo Mafi Tsawo A Afrika Dake Algeria

Kamfanin CRCC Ya Kammala Shimfida Hanyar Jirgin Kasa A Gadar Layin Dogo Mafi Tsawo A Afrika Dake Algeria

LABARAI MASU NASABA

Zan Ware 10bn Don Inganta Ilimin Matasa Idan Na Ci Zabe – Atiku

‘Yan Nijeriya Ba Sa Bukatar ‘Yan Jarida Su Faɗa Musu Suna Jin Yunwa’ — Atiku

June 25, 2026
Dokar Sin Ta Gurfanar Da Masu Rajin Ballewar Kabilun Kasar Da Ke Kasashen Waje Ta Dace

Dokar Sin Ta Gurfanar Da Masu Rajin Ballewar Kabilun Kasar Da Ke Kasashen Waje Ta Dace

June 24, 2026
’Yan Kasuwa Na Kasashen Waje Sun Yaba Wa Yanayin Kasuwanci Na Sin

’Yan Kasuwa Na Kasashen Waje Sun Yaba Wa Yanayin Kasuwanci Na Sin

June 24, 2026
Yadda Uba Sani Ya Farfaɗo Da Asibitin Da Aka Yi Watsi Da Shi Tsawon Shekaru 40 – Hakimin Makarfi

Yadda Uba Sani Ya Farfaɗo Da Asibitin Da Aka Yi Watsi Da Shi Tsawon Shekaru 40 – Hakimin Makarfi

June 24, 2026
Dandalin DAVOS Na Bana: Fage Ne Da “Kirkire-Kirkiren Sin” Ya Sadu Da “Kyakkyawan Fatan Afirka”

Dandalin DAVOS Na Bana: Fage Ne Da “Kirkire-Kirkiren Sin” Ya Sadu Da “Kyakkyawan Fatan Afirka”

June 24, 2026
Binciken CGTN: Amfanarwa A Aikace Shi Ne Nagartaccen Ma’aunin Tantance Ainihin Kimar Sabbin Fasahohi

Binciken CGTN: Amfanarwa A Aikace Shi Ne Nagartaccen Ma’aunin Tantance Ainihin Kimar Sabbin Fasahohi

June 24, 2026
Kasar Sin Na Kara Zama Babban Ginshikin Ci Gaban Tattalin Arzikin Duniya Na Gaba

Kasar Sin Na Kara Zama Babban Ginshikin Ci Gaban Tattalin Arzikin Duniya Na Gaba

June 24, 2026
Tsaro: Dasuki Ya Bukaci Tinubu Ya Gyara Alaka Da Nijar Domin Kare Iyakokin Arewa-Maso-Yamma

Tsaro: Dasuki Ya Bukaci Tinubu Ya Gyara Alaka Da Nijar Domin Kare Iyakokin Arewa-Maso-Yamma

June 24, 2026
Sabbin Ministoci

Kafa ‘Yansandan Jihohi: Majalisa Ta Amince Da Tsarin ‘Yar Tinƙe Wajen Kaɗa Ƙuri’a 

June 24, 2026
Sin Ta Gabatar Da Tsarin Karfafa Kwarin Gwiwar Kamfanoni Masu Jarin Waje

Sin Ta Gabatar Da Tsarin Karfafa Kwarin Gwiwar Kamfanoni Masu Jarin Waje

June 24, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.