A kwanakin baya ne wasu da suke da alamar Sayawa suka fito a wani gajerin bidiyo inda suke bayyana cewar Gwamnan jihar Bauchi Bala Muhammad ya amince da ƙayyade Sadakin Naira 1,500 ga Zawarawa, da sauran rukunin mata da aka musu kuɗinsu daban-daban, lamarin dai ya tada ƙura ganin cewa lamarin Shari’a.
Tunin dai gwamnatin Jihar Bauchi bidiyon da ke yawo a kafafen sada zumunta, wanda ke iƙirarin cewa Gwamna Bala Abdulkadir Mohammed ya amince da ƙayyade sadakin Zawarawa zuwa naira 1,500, a matsayin ƙarya tsagwaronta da wasu suka ƙirƙiro domin sanya ruɗani a zukatan al’umman jihar.
Bidiyon, wanda ya bazu sosai a shafukan Facebook da TikTok, ya kuma yi zargin cewa Sarkin Sayawa (Gum Zar) ya umarci al’ummar yankin da su bi wannan sabuwar tsarin da gwamnati ta ɓullo da shi.
Haka kuma, wani mai amfani da kafar sada zumunta mai suna Boroh James Hussaini ya wallafa cewa sadakin budurwa da ta taɓa haihuwa ba tare da aure ba zai kasance Naira 3,000, yayin da matan da suka daɗe ba su yi aure ba kuma ba su taɓa haihuwa ba za a aurar da su ga direbobi ba tare da an biya sadaki ba.Da ya ke ƙaryata batun yayin ganawa da manema labarai a Bauchi, Kwamishinan kula da harƙoƙin addini, Injiniya Muhammad Binni Abdulkadir, ya bayyana waɗannan iƙirari a matsayin ƙirƙirarru, marasa tushe balle makama kuma karya ce gaba ɗaya.
Ya jaddada cewa Gwamnatin Jihar Bauchi ba ta taɓa ƙirƙirar ko amincewa da wata manufa da ta shafi ƙayyade sadakin matan da aka sake su ko kuma mata marasa aure ba, yana mai cewa an ƙirƙiri waɗannan rahotanni ne da gangan domin ruɗar da jama’a.
Kwamishinan ya buƙaci al’ummar jihar da su yi watsi da waɗannan jita-jita, tare da gujewa yaɗawa ko kambama bayanan da ba a tantance ba, domin hakan na iya haifar da ruɗani da tashin hankali ba tare da wani dalili ba.Ya ƙara da cewa tun daga lokacin da ya hau mulki, Gwamna Bala Abdulkadir Mohammed ya kasance mai mutunta koyarwar addini, al’adun gargajiya da kyawawan ƙabi’un al’ummar Jihar Bauchi.
Injiniya Binni ya kuma yi kira ga jama’a da su tabbatar da sahihancin duk wani bayani kafin su yaɗa shi a kafafen sada zumunta, yana gargaɗin cewa yaɗa labaran ƙarya na iya yin illa ga zaman lafiya, haɗin kai da martabar Jihar Bauchi, tare da lalata kyawawan al’adunta da gadon addininta.
Tun bayan fitar labarin dai mutane da dama a jihar Bauchi suke nuna damuwarsu, inda suka nemi a gaggauta hukunta waɗanda suka shirya da yaɗa bidiyon domin kare martabar Shari’a da kuma al’adu da suke jihar.
Adamu Ahmed Sani mazaunin Bauchi ya shaida cewa, “A tunani an yaɗa wannan a matsayin wasan kwaikwayo da neman masu bibiya ne. To, amma gaskiya hakan babban kuskure ne. Bai dace a ce mutum ya shirya comedy ya yaɗa ya ambaci sunan jiha da gwamnan jihar ya ce ya bada umarni kan abun da an san ya saɓa da shari’ar da wasu da dama suke tafiya a kai kamar jiha ta musulmi irin Bauchi.
“Don haka a gaggauta kama waɗanda suka shirya da fitar da wannan bidiyon domin hakan ya zama izina. Gwamna da gwamnati da manufofin gwamnati ba abun wasa ba ne sam. Irin wannan jita-jitar ka iya tayar da hankali da janyo ruɗani sosai a cikin al’umma,” ya shaida.
Shi ma Samuel Adekunle, ya ce ko Sayawa ba su ji daɗin yaɗa irin wannan batun ba, “Mu ai har Sarkin Sayawa da aka kira a cikin batun ma ba daɗi ya mana ba. Don haka ba daidai ba ne mutum ya shirya irin wannan abun da zai janyo damuwa a cikin al’umma.”Shi kuma Mustapha Umar, cewa ya yi ba laifi ne mutum ya yi comedy ba, amma ambatar sunan jiha guda da gwamnanta shi ne babban kuskure.














