Kwamitin Riko na Ƙasa (INWC) na jam’iyyar PDP ƙarƙashin jagorancin Kabiru Tanimu Turaki (SAN), ya sanar da miƙa sunan tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan ga Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) a matsayin ɗan takararta na shugaban ƙasa a zaben 2027.
Sakataren Yaɗa Labarai na ɓangaren, Comrade Ini Ememobong, ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da ya gudanar a Abuja ranar Alhamis, 31 ga Yuli, 2026. Ya ce sun miƙa sunan Jonathan tare da na ‘yan takarar gwamnoni da ‘yan majalisar dokoki tare.
Ememobong ya bayyana cewa sun miƙa takardun da hannu ne bayan hukumar INEC ta ƙi ba su lambobin shiga shafinta na yanar gizo (access codes). Sai dai ya jaddada cewa hukumar ta karɓi takardun domin cika ƙa’idojin Dokar Zaɓe ta 2026.
Ɓangaren na Turaki ya shaida cewa har yanzu su ne shugabanni na halak na PDP sakamakon rikicin shugabanci da ya biyo bayan hukuncin Kotun Ƙoli. Sun kuma yi gargaɗin cewa za su ɗauki matakin shari’a idan har INEC ta wallafa wasu sunaye na daban.
Haka zalika, Ememobong ya soki hukuncin Kotun Tarayya da ke Abuja ƙarƙashin Mai Shari’a Salim Oluwasupo Ibrahim, inda ya bayyana cewa sun riga sun ɗaukaka ƙara. Ya kuma zargi hukumar INEC da nuna bambanci da rashin adalci ga ɓangaren nasu.














