ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yadda Kamfanin Dangote Ya Gudanar Da Bikin Ranar Matasa Ta Duniya A Obajana

by Rabi'u Ali Indabawa
3 weeks ago
Obajana

Kamfanin Simintin Dangote, Obajana, ya gudanar da bikin Ranar Matasa ta Duniya, tare da sake jaddada ƙudirinsa na bunƙasa matasa ta hanyar shirye-shiryen karfafawa daban-daban, da kuma ƙara tasirinsa mai kyau ga al’umma.

A cikin wata sanarwa da Sashen Hulɗa da Jama’a na kamfanin ya fitar, an ce sama da mutum 100 ne suka halarci taron, waɗanda suka haɗa da jakadun masu nasara, masu koyon aikin digiri, masu koyon aikin gudanarwa, ƴan bautar ƙasa (NYSC) da sauran baƙin da aka gayyata.

Sanarwar ta ce taron ya zama wata dama ga matasa wajen gabatar da sabbin dabaru, musayar ilimi da kuma duba hanyoyin magance matsalolin da suka shafi ɗorewar muhalli da wuraren aiki.

ADVERTISEMENT

Gabatarwar da aka yi a taron ta shafi batutuwa daban-daban, daga sake sarrafa shara da kare muhalli zuwa hanyoyin da fasaha ke samarwa, ciki har da amfani da jirage marasa matuƙi (drones) domin inganta tsaro a ayyukan haƙar ma’adanai.

Da yake jawabi a wajen taron, Shugaban Sashen Kula da Ma’aikata (HAM) da Gudanarwa, Mista Adeniyi Azeez, ya yaba wa mahalarta bisa ƙirƙire-ƙirƙirensu da himmarsu.

LABARAI MASU NASABA

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

Ya ƙarfafa wa matasan gwiwa da su ci gaba da bunƙasa ƙwarewarsu, rungumar ƙirƙire-ƙirƙire, da kuma amfani da damar da za ta taimaka wajen ci gabansu da bunƙasa sana’o’insu.

Shi ma Shugaban Sashen Ayyukan Jin Daɗin Al’umma, Mista Ademola Adeyemi, ya jaddada muhimmancin shigar matasa cikin ƙoƙarin samar da makoma mai ɗorewa.

Ya buƙkaci matasa da su ci gaba da nuna kishin kare muhalli, ci gaban al’umma da shugabanci nagari, yana mai cewa dabarun da ake samarwa a yau na iya zama mafita mai tasiri gobe.

Shirin ya ƙunshi gabatar da sabbin dabaru, gabatarwa kan ɗorewar muhalli, waƙoƙin baka, nishaɗin kiɗa, wasanni da kuma zaman tattaunawa da suka sa mahalarta suka kasance cikin nishaɗi da sha’awa a tsawon taron.

An kuma nuna wani faifan bidiyo da ya ƙunshi ayyukan bikin Ranar Matasa ta Duniya da aka gudanar a baya, wanda ya zaburar da mahalarta tare da ƙara nuna musu muhimmancin rawar matasa wajen samar da sauyi mai kyau.

Mahalarta taron sun bayyana bikin a matsayin mai ƙayatarwa da kuma tasiri, inda suka ce ya taimaka wajen ƙara musu ƙwarin gwiwa, ƙwarewar magana a gaban jama’a da kuma ƙudurin tallafawa shirye-shiryen kare muhalli da ɗorewa a cikin al’ummominsu.

Sanarwar ta ce nasarar bikin Ranar Matasa ta Duniya ta shekarar 2026 ta nuna ƙudurin kamfanin Simintin Dangote na ƙarfafa matasa, bunƙasa ƙirƙire-ƙirƙire da kuma tabbataccen ci gaba mai.

Ta ƙara da cewa taron ya nuna cewa idan aka bai wa matasa ingantaccen dandali da kwarin gwiwa, za su iya samar da hanyoyin magance matsaloli a aikace, tare da zama masu bayar da gudummawa wajen samar da tabbatacciya makoma.

Obajana
Rabi'u Ali Indabawa
+ postsBio
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ƙungiya Ta Gudanar Da Zaɓen Sabbin Shugabanninta A Abuja
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Jihar Katsina Da UNICEF Sun Ceto Rayuwar Yara Ta Hanyar Samar Da Abinci Mai Gina Jiki
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Yadda Tinubu Ya Kashe Naira Biliyan 37.64 A Tafiye-tafiye
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ta’addaci: Mutum 14,500 Sun Bace A Arewa Maso Gabas

MASU ALAKA

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu
Labarai

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

September 9, 2026
Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu
Manyan Labarai

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

September 9, 2026
’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja
Manyan Labarai

’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

September 9, 2026
Next Post
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Malamai 7,525 Ke Karɓar Alawus Duk Wata Domin Wanzar Da Zaman Lafiya A Katsina

LABARAI MASU NASABA

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

September 9, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

September 9, 2026
Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

September 9, 2026
Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

September 9, 2026
Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

September 9, 2026
Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

September 9, 2026
Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

September 9, 2026
“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

September 9, 2026
’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

September 9, 2026
Taron Kolin Urumqi Ya Mayar Da Hankali Kan Kwarewar Shugabanci A Xinjiang Da Muhimmancinta Ga Duniya

Taron Kolin Urumqi Ya Mayar Da Hankali Kan Kwarewar Shugabanci A Xinjiang Da Muhimmancinta Ga Duniya

September 9, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.