Wasu mutanen da suka tsira daga barkewar cutar mashaƙo da ke addabar wasu sassan Arewacin Nijeriya, ciki har da jihohin Katsina, Kano, Filato da Nasarawa, sun bayyana irin abubuwan da suka fuskanta, inda wasu daga cikinsu suka ce ba su san yadda suka kamu da cutar ba.
Al’ummomin da abin ya shafa a jihohin na ci gaba da fama da barkewar cutar, wadda ta yi sanadin mutuwar mutane da dama tare da tilasta kwantar da wasu marasa lafiya a cibiyoyin killace masu fama da cututtuka.
Badiya Bishir, mazauniyar Sabuwar Unguwa da ke cikin birnin Katsina, wadda ta warke daga cutar mashaƙo, ta ce ba ta san lokacin ko inda ta kamu da cutar ba.
Ta ce, “Ban san lokacin da na kamu da cutar ba. Ta fara ne lokacin da na fara samun wahalar haɗiye yawu. A wannan daren ban iya barci ba. Da na fara tofa, sai jini ya fito tare da yawuna.”
An garzaya da ita zuwa asibiti, inda aka tabbatar da cewa tana fama da cutar mashaƙo, sannan aka fara ba ta magani.
Ta ce, “Daga baya aka ba ni magani, kuma yanzu na warke.”
Shi ma Sadiq Muhammad Tukur, wanda matarsa ta kamu da cutar mashaƙo, ya ce da farko ya damu matuƙa da yanayin da take ciki, amma bai fahimci cewa cutar mashaƙo ce ta kama ta ba.
Ya ce tun farko yana tunanin alamomin da take nunawa na farjin hanci ne, kafin daga bisani likitoci su tabbatar masa cewa cutar ce.
“Na damu sosai lokacin da abin ya fara. Da farko ina tunanin farin hanci ne, amma daga baya aka tabbatar da cewa cutar ce,” in ji shi.
Tukur ya bayyana cewa ya kashe sama da N50,000 wajen sayen magunguna da kula da matarsa, lamarin da ke nuna irin nauyin kuɗaɗen da cutar ke haifarwa ga iyalai.
Ma’aikatan Lafiya A Katsina Sun Ƙi Janye Yajin Aiki Yayin Da Marasa Lafiya Da Ma’aikata Ke Shan Wahala
A wani ɓangaren kuma, yajin aikin da ma’aikatan lafiya a Jihar Katsina ke shirin fara yi na barazanar ƙara jefa tsarin kiwon lafiyar jihar cikin matsala, a daidai lokacin da hukumomi ke fama da barkewar cutar mashaƙo, yayin da asibitoci ke fuskantar ƙarin ɗimbin marasa lafiya.
Ƙungiyar Ma’aikatan Lafiya da Magunguna ta sanar da cewa za ta fara yajin aikin daga ƙarfe 12:00 na dare ranar Talata, bisa zargin cewa gwamnatin Jihar Katsina ta gaza magance buƙatunta dangane da ƙarin albashi, alawus-alawus, jin daɗin ma’aikata da sauran haƙƙoƙin aikin yi.
Yajin aikin da aka shirya ya haifar da fargabar tasirinsa ga harkokin kiwon lafiya, musamman ga marasa lafiyar da ke karɓar maganin cutar mashaƙo da sauran cututtuka masu yaɗuwa.
Sai dai ƙungiyar ta dage cewa an fara shirye-shiryen yajin aikin ne tun kafin barkewar cutar mashaƙo ta zama babban abin damuwa a jihar.
Da yake magana kan batun, Kwamared Ibrahim Awal Balengi ya ce ƙungiyar ta shafe sama da shekaru biyu tana tattaunawa da gwamnati kan jin daɗin ma’aikata da sauran ƙorafe-ƙorafe.
Ya ce ƙungiyar ta ba gwamnati wa’adin ne tun kafin barkewar cutar mashaƙo ta zama babban abin damuwa a jihar.
A cewar Balengi, ganawar da gwamnati ta yi da ma’aikatan a baya-bayan nan ba tattaunawa ce ta neman matsaya ba, illa dai “ganawa ce ta sanarwa”, inda jami’an gwamnati suka gabatar da matsayar gwamnati kan buƙatun ma’aikatan.
Ya ce gwamnati ta bayar da shawarar ƙarin kashi 10 cikin 100 kan bambancin albashin da ma’aikatan ke nema, amma ma’aikatan sun ƙi amincewa da tayin.
Ma’aikatan sun kuma nemi a inganta musu alawus-alawus da sauran alfanun aiki, suna cewa takwarorinsu da ke jihohin makwabta da cibiyoyin kiwon lafiya na tarayya suna samun kyakkyawan yanayin aiki.
Balengi ya ce ƙungiyar a shirye take ta ci gaba da tattaunawa, kuma za ta iya sake duba batun yajin aikin idan gwamnati ta koma kan teburin tattaunawa na gaskiya.
“A shirye muke mu tattauna. Muna sa ran gwamnati za ta sake yin zama da mu,” in ji shi.
Martanin Gwamnati
Da aka tuntubi Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina, Masa’udu Mustapha Banyi, domin jin ra’ayinsa kan yajin aikin da aka shirya da kuma ƙorafe-ƙorafen ma’aikatan, ya ƙi yin tsokaci kai tsaye.
Sai dai wani saƙo daga ofishinsa ya bayyana cewa jami’an gwamnati na gudanar da wani taro kan batun, kuma za su yi wa manema labarai bayani “a lokacin da ya dace.”
Shirin yajin aikin ya ƙara jawo hankalin marasa lafiya da masu ruwa da tsaki a fannin kiwon lafiya, waɗanda ke fargabar cewa ƙarin tangarda a harkokin kiwon lafiya na iya ƙara matsa wa tsarin kiwon lafiyar jihar da tuni yake fama da matsin lamba.
Ma’aikatan Lafiya Na Fuskantar Matsin Lamba
Wani bincike da jaridar LEADERSHIP ta gudanar ya gano cewa matsalolin jin daɗin ma’aikatan lafiya a jihar sun fi batun takaddamar albashi da ake ciki a yanzu.
Wasu ma’aikatan lafiya da aka zanta da su sun nuna rashin gamsuwa da albashin da suke karɓa da kuma sauran yanayin aikin, musamman idan aka kwatanta da takwarorinsu da ke cibiyoyin kiwon lafiya na tarayya.
Rahotanni sun nuna cewa wannan yanayi ya taimaka wajen ficewar wasu ƙwararrun ma’aikatan lafiya daga tsarin kiwon lafiyar jama’a na jihar, inda wasu suka yi murabus domin neman aiki a asibitoci masu zaman kansu, cibiyoyin tarayya da sauran wurare.
Binciken ya kuma gano cewa kimanin likitoci 14 sun bar asibitocin gwamnatin jihar tsakanin watan Fabrairu zuwa Yuni 2026, lamarin da ya ƙara tsananta ƙarancin ma’aikata a wasu cibiyoyin kiwon lafiya.
Haka kuma, ana zargin ma’aikatan lafiya na kula da adadi mai yawa na marasa lafiya, inda wasu ma’aikatan cibiyoyin kiwon lafiyar gwamnati ke kula da sama da marasa lafiya 60 a rana ɗaya.
Haɗuwar ƙarancin ma’aikata, yawan marasa lafiya da kuma damuwar da ake da ita kan albashi ta jawo tambayoyi kan yadda tsarin kiwon lafiyar jihar zai iya ci gaba da samar da ingantaccen aiki, musamman a lokacin da ake fama da barkewar cuta mai yaɗuwa.
Nasarawa Ta Yi Rajistar Mutane 15 Da Aka Tabbatar Sun Kamu Da Cutar Mashaƙo
Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Nasarawa ta tabbatar da samun mutane 15 da suka kamu da cutar mashaƙo a yayin barkewar cutar da ake fama da ita a jihar, inda mafi yawan masu cutar suke a Ƙaramar Hukumar Keffi.
Daraktan Kiwon Lafiyar Jama’a, Dr Attah Peter, ne ya bayyana hakan a wata hira da aka yi da shi ranar Laraba.
A cewarsa, mutane 11 daga cikin 15 da aka tabbatar sun kamu da cutar daga Keffi suke, uku daga Lafia, yayin da ɗaya yake daga Wamba. Yaran da cutar ta kama shekarunsu na tsakanin wata biyu zuwa shekaru 11.
Ya bayyana barkewar cutar a matsayin matsalar da ke sake faruwa, wadda babban abin da ke haddasa ta shi ne rashin yi wa yara rigakafi.
“Yawancin yaran da suke kamuwa da cutar mashaƙo su ne yaran da ba a yi wa rigakafi ba — yaran da iyayensu ko masu kula da su suka kasa kai su lokacin da ake yi wa yara rigakafin da aka tsara bayan haihuwa,” in ji Peter.
Ya bayyana mamakinsa kan yadda yaro mai shekaru 11 zai kasance cikin haɗarin kamuwa da cutar, yana mai cewa da an yi masa rigakafin yadda ya kamata, da an kare shi.
“Matsala ce da ke sake faruwa. Sai ka fara mamakin yadda yaro mai shekaru 11 yake kamuwa da cutar mashaƙo a wannan lokaci. Shekaru 11 da suka gabata, ya kamata mai kula da shi ya kai shi a yi masa rigakafi. Ba a yi hakan ba, shi ya sa har yanzu yaron yake cikin haɗarin kamuwa da cutar,” in ji shi.
Peter ya danganta abin da ke faruwa a Nasarawa da barkewar cutar a wasu jihohi, inda ya ambaci Kano, inda abokin aikinsa ya ba da rahoton samun masu cutar da suka kai shekaru 50 waɗanda ba a taɓa yi wa rigakafin cutar ba.
“Idan ba a yi maka rigakafi ba, ba za ka samu garkuwar jiki da za ta iya kare ka daga kamuwa da cutar ba,” in ji shi.
Dangane da mace-mace, daraktan ya ce an samu mutuwar mutane a jihar a bara, amma babu wani mutum da ya mutu a bana daga cikin waɗanda suka kai kansu cibiyoyin lafiya.
Ya ce, “Saboda mun shirya tun da wuri a bana, kuma daga cikin waɗanda suka kai kansu cibiyoyin lafiya, ba mu samu wata mace-mace ba. Wataƙila hakan ya faru ne saboda likitocin sun yi zargin cutar tun da wuri sannan aka fara magani cikin gaggawa.”
Ya ce an samar da allurar rigakafi a Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya da ke Keffi da kuma Asibitin Koyarwa na Jami’ar Tarayya da ke Lafia domin kula da marasa lafiya, ciki har da wani mara lafiya da aka tura daga Wamba.
Peter ya bukaci iyaye da masu kula da yara su yi amfani da damar rigakafin da ake bayarwa kyauta a cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko da ke faɗin jihar.
“Rigakafin da ake yi wa kowane yaro kyauta ne. Abin da ake buƙata shi ne ka yi ƙoƙari ka kai yaron inda ake samun rigakafin, kuma kyauta ne, sannan ana samun sa cikin sauƙi a kusan kowace cibiyar kiwon lafiya ta matakin farko,” in ji shi.
Ya tunatar da masu kula da yara cewa ana fara yi musu rigakafin yau da kullum tun daga haihuwa har zuwa watanni 18, ciki har da rigakafin cutar zazzabin shawara da kyanda a wata tara, ƙarin rigakafin kyanda a wata 15, da kuma rigakafin HPV ga ’yan mata masu shekaru tara zuwa 11 domin kare su daga cutar kansar mahaifa.
Ya kuma shawarci duk wanda yake da alamomin da za su iya nuna cewa yana fama da cutar mashaƙo da ya garzaya zuwa cibiyar lafiya mafi kusa domin samun magani cikin gaggawa.
Cutar Mashaƙo: Abubuwan Da Ya Kamata ’Yan Nijeriya Su Sani
Yayin da Arewacin Najeriya ke ci gaba da fama da barkewar cutar mashaƙo, an shawarci iyaye, masu kula da yara da al’umma da kada su yi watsi da alamomin da ka iya nuna kamuwa da cutar, domin gano cutar da wuri, fara magani cikin gaggawa da yin rigakafi na da matuƙar muhimmanci wajen hana mace-mace da kuma ƙarin yaɗuwar cutar.
Cutar mashaƙo cuta ce mai tsanani da ƙwayoyin cuta ke haddasawa. Galibi tana shafar hanci da maƙogwaro, kuma a wasu lokuta tana iya shafar fata. A lokutan da cutar ta tsananta, ƙwayoyin cutar na iya samar da guba da ke lalata ƙwayoyin jiki da gabobi, lamarin da zai iya sanya cutar cikin haɗarin yin sanadin mutuwa.
Darakta-Janar na Cibiyar Kula da Cututtuka ta Najeriya (NCDC), Dr Jide Idris, ya ce mutanen da ba a taɓa yi wa rigakafin ba, ko waɗanda aka yi wa kashi ɗaya kacal na rigakafin pentavalent, suna cikin waɗanda suka fi fuskantar haɗarin kamuwa da cutar.
Ya ce haɗarin ya fi yawa ga mutanen da ke zaune a wuraren da cunkoso ya yi yawa ko kuma wuraren da tsaftar muhalli ba ta da kyau. Ma’aikatan lafiya da sauran mutanen da suke yawan hulɗa ta kusa da waɗanda ake zargin sun kamu da cutar ko waɗanda aka tabbatar sun kamu da ita su ma suna cikin haɗari.
Ta Yaya Ake Kamuwa Da Cutar Mashaƙo?
A cewar NCDC, cutar mashaƙo tana yaɗuwa ne musamman ta hanyar kusanci kai tsaye da wanda ya kamu da cutar da kuma ɗigon majina ko miyau da ke fita yayin da mai cutar yake tari ko atishawa.
Haka kuma, ana iya kamuwa da cutar ta hanyar taɓa tufafi ko wasu abubuwan amfani da mutumin da ya kamu da cutar ya gurɓata.
Saboda haka, gidaje, makarantu, wuraren aiki da sauran wuraren da mutane ke yawan kasancewa kusa da juna na iya sauƙaƙa yaɗuwar cutar, musamman a wuraren da adadin mutanen da aka yi wa rigakafi ya yi ƙasa.
Bayan mutum ya kamu da ƙwayoyin cutar, alamomin cutar kan fara bayyana cikin kwanaki biyu zuwa 10, a cewar hukumar.
Yaya Cutar Mashaƙo Ke Bayyana?
Alamomin farko na cutar mashaƙo na iya yin kama da na wasu cututtukan numfashi da aka saba gani, lamarin da kan sa gano cutar ya zama da wahala.
NCDC ta lissafa zazzabi, majina, ciwon maƙogwaro, tari da kuma jajayen idanu a matsayin wasu daga cikin alamomin cutar.
Yayin da cutar ke ci gaba, wasu alamomi masu tsanani na iya bayyana, ciki har da kumburin wuya. A lokuta masu tsanani, wani farin ko toka mai kauri na iya samuwa a kan tonsils ko a bayan maƙogwaro.
Hukumar ta bukaci ma’aikatan lafiya da su kasance masu taka-tsantsan wajen zargin cutar, musamman idan marasa lafiya sun zo da alamomin da suka yi daidai da cutar, kuma ba a san tarihin rigakafinsu ba ko kuma ba su cika yin rigakafin da aka tsara ba.
Me Ya Kamata A Yi Idan Ana Zargin Cutar?
Dr Idris ya ce duk wanda ya fara nuna alamomin da za su iya kasancewa na cutar mashaƙo ya nemi kulawar lafiya cikin gaggawa, sannan ya guji kusantar sauran mutane yayin da ake jiran a duba shi.
Ya shawarci mutanen da ke da alamomi masu kama da na cutar da su killace kansu tare da sanar da hukumomin lafiya da abin ya shafa, ciki har da Ƙaramar Hukumar da suke, Jami’in Kula da Yaduwar Cututtuka na Jiha (DSNO) ko kuma NCDC ta hanyar layinta na kyauta.
Darakta-Janar din ya kuma shawarci mutanen da suka yi kusanci da wanda aka tabbatar ya kamu da cutar kada su ɗauka cewa ba su cikin haɗari kawai saboda ba su nuna wata alama ba.
NCDC ta ba da shawarar a sa ido sosai kan mutanen da suka yi kusanci da masu cutar, sannan a ba su maganin rigakafi na kariya idan ya dace. Haka kuma, ya kamata a ba su maganin diphtheria antitoxin idan likitoci suka ga ya dace.
Ma’aikatan lafiya da ke kula da waɗanda ake zargin sun kamu da cutar ko waɗanda aka tabbatar sun kamu da ita su ma dole ne su ɗauki matakan kariya da hana yaɗuwar cututtuka domin kare kansu da kuma hana ƙarin yaɗuwar cutar.
Ta Yaya Za A Hana Cutar Mashaƙo?
NCDC ta bayyana cewa rigakafi shi ne hanya mafi inganci ta kare kai daga cutar mashaƙo.
A tsarin rigakafin yara na Najeriya, ana ba da shawarar a yi wa yara kashi uku na rigakafin pentavalent, wanda ya ƙunshi sinadarin rigakafin mashaƙo, a makonni shida, 10 da 14 bayan haihuwa.
Baya ga rigakafi, rage cunkoso, kiyaye tsafta da muhalli, da kuma gano waɗanda ake zargin sun kamu da cutar da wuri tare da ba su kulawar da ta dace na taimakawa wajen takaita yaɗuwar cutar.
Ci gaba da samun barkewar cutar mashaƙo a Najeriya na nuna illar da gibin rigakafi ke haifarwa. Idan yara suka rasa damar samun rigakafin da ake yi a kai a kai, gibin kariyar jiki na iya taruwa, lamarin da ke samar da al’ummomin da mutane da yawa ba su da kariya, inda cututtukan da za a iya hana su ta hanyar rigakafi za su iya sake bayyana su yaɗu.
Rahoton Cutar A Ƙididdigar Kiwon Lafiya
Najeriya ta samu mutane 40,460 da aka tabbatar sun kamu da cutar mashaƙo, yayin da mutane 2,151 suka mutu tsakanin Makon Cutar na 19 na shekarar 2022 da Makon Cutar na 3 na shekarar 2026, a cewar rahoton ƙididdigar cututtuka na NCDC.
Sabuntaccen rahoton NCDC na Janairu 2026 ya nuna cewa an samu rahotannin mutane 61,930 da ake zargin sun kamu da cutar a dukkan jihohin 36 na Najeriya da Babban Birnin Tarayya Abuja, a cikin ƙananan hukumomi 450 a wannan lokaci.
Daga cikin mutanen da ake zargin sun kamu, 40,460 (kashi 65.3) an tabbatar da cewa sun kamu da cutar, 17,020 (kashi 27.5) an kawar da zarginsu, yayin da 4,450 (kashi 7.2) ke jiran a tantance matsayinsu.
An samu mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar a ƙananan hukumomi 300 da ke cikin jihohi 31, inda Jihar Kano ta kasance jihar da ta fi yawan adadin waɗanda aka tabbatar sun kamu.
Kano ta samu mutane 24,687 da aka tabbatar sun kamu, sai Borno da 5,077, Bauchi 4,139, Yobe 3,159, sannan Katsina 2,589. Kaduna ta samu 156, Sokoto 146, yayin da Filato ta samu 137.
Daga cikin mutanen da ake zargin sun kamu, Kano ta samu 31,171, sai Borno 7,274, Yobe 6,682, Katsina 5,714, Bauchi 5,406, Kaduna 1,876, sannan Sokoto 481.
Jihohin nan bakwai sun haɗa suka samar da kashi 94.6 cikin 100 na dukkan mutanen da ake zargin sun kamu da cutar a wannan lokaci, yayin da mutanen da aka tabbatar sun kamu a Kano, Yobe, Bauchi, Katsina, Borno, Filato, Sokoto da Kaduna suka kai kashi 99.1 cikin 100 na dukkan waɗanda aka tabbatar sun kamu.
Yara ne suka fi fuskantar illar barkewar cutar, inda mutane 26,226, wato kashi 64.8 cikin 100 na waɗanda aka tabbatar sun kamu, suke tsakanin shekara ɗaya zuwa 14.
Matsayin rigakafin waɗanda suka kamu da cutar ma ya kasance abin damuwa. Mutane 5,974, wato kashi 14.3 cikin 100 daga cikin mutane 40,460 da aka tabbatar sun kamu, ne kawai aka tabbatar an yi musu cikakken rigakafin da ke ɗauke da sinadarin kariya daga cutar mashaƙo.
Daga cikin waɗanda aka tabbatar sun kamu da cutar, 612 an tabbatar da kamuwarsu ta hanyar gwajin dakin bincike, 987 an danganta su da wasu mutane da aka tabbatar sun kamu, yayin da 38,861 aka rarraba su a matsayin masu alamomin da suka yi daidai da cutar.
Barkewar cutar ta yi sanadin mutuwar mutane 2,151, wanda ya nuna adadin mace-macen da ya kai kashi 5.3 cikin 100 na waɗanda aka tabbatar sun kamu.
A halin yanzu kuma, zuwa ranar 28 ga Agusta 2026, Darakta-Janar na NCDC ya ce Najeriya ta samu sama da 10,000 da aka tabbatar sun kamu da cutar mashaƙo a bana, inda mafi yawan masu cutar suke a jihohin Kano, Borno da Bauchi.
Sai dai ya ce an samu gagarumin raguwar mace-mace tsakanin masu cutar idan aka kwatanta da makamancin wannan lokaci na bara.
Shugaban NMA Na Filato Ya Ce Rashin Isasshen Rigakafi Na Ƙara Haddasa Barkewar Cutar Mashaƙo
Shugaban Ƙungiyar Likitocin Najeriya (NMA), reshen Jihar Filato, Dr Andrew Shainaan, ya bayyana ƙarancin adadin mutanen da aka yi wa rigakafi a matsayin babban abin da ke taimakawa wajen barkewar cutar mashaƙo.
Ya bayyana cewa cutar mashaƙo cuta ce da ƙwayar Corynebacterium diphtheriae ke haddasawa, wadda ke samar da wata guba mai haɗari da za ta iya shafar muhimman gabobin jiki, ciki har da zuciya da ƙoda.
Shainaan ya ce cutar tana yaɗuwa ne musamman ta ɗigon majina ko miyau yayin tari da atishawa, kusanci kai tsaye da mutanen da suka kamu da cutar ko raunukan fata, da kuma ta gurɓatattun wurare ko abubuwa.
Ya jaddada muhimmancin rigakafi wajen gina kariyar al’umma da kuma kare mutanen da suka fi fuskantar haɗarin kamuwa da cutar.
Shainaan ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da jaridar LEADERSHIP a Jos.
A cewarsa, alamomin cutar da aka fi gani sun haɗa da ciwon maƙogwaro, zazzabi, wahalar numfashi da kumburi a wajen wuya ko ƙarƙashin haɓa, wanda kumburin ƙwayoyin lymph ke haddasawa.
“Yara, musamman waɗanda shekarunsu suke tsakanin huɗu zuwa 14, suna daga cikin waɗanda suka fi fuskantar haɗarin kamuwa da cutar, ko da yake manya masu ƙarancin garkuwar jiki su ma na iya kamuwa.”
Dangane da magani da kula da masu cutar, ya ce marasa lafiya na buƙatar maganin kashe ƙwayoyin cuta, maganin antitoxin, taimakon numfashi, maye gurbin ruwan jiki da suka rasa, sannan abu mafi muhimmanci shi ne killace su domin hana ƙarin yaɗuwar cutar.
Ya shawarci jama’a, musamman iyaye, da kada su ɗauki alamomin kamar tari, zazzabi da wahalar numfashi a matsayin mura kawai.
“Ya kamata a kai irin waɗannan marasa lafiya asibiti cikin gaggawa domin a gudanar da binciken da ya dace a ba su magani, maimakon yin amfani da magunguna da kansu ko zuwa wajen masu sayar da magani.”
Ya ce gano cutar da wuri, fara magani a asibiti cikin gaggawa, killace masu cutar da kuma ƙara yawan mutanen da ake yi wa rigakafi na da muhimmanci wajen dakile yaɗuwar cutar mashaƙo a jihar.
LEADERSHIP ta tuna cewa aƙalla mutane 15 ne suka mutu sakamakon zargin barkewar cutar mashaƙo a wasu al’ummomi da ke Ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa a Jihar Filato.
Haka kuma, ana zargin aƙalla mutane 117 sun kamu da cutar, lamarin da ya jawo damuwa tsakanin hukumomin lafiya kan yiwuwar barkewar cutar ta ƙara tsananta.
Jami’in Kula da Yaduwar Cututtuka na Ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa, Mista Baks Bulus, ne ya bayyana hakan ga manema labarai a sakatariyar ƙaramar hukumar.
Bulus ya ce mutanen da suka mutu sun rasu ne cikin kwanaki uku da fara barkewar cutar, yana mai gargadin cewa adadin masu cutar na iya ƙaruwa idan ba a ɗauki matakan gaggawa na kariya ba.
“Zan iya bayar da bayanin abin da ke faruwa a Jos ta Arewa. Ya zuwa yanzu, bisa bayanan da muka tattara daga al’ummomin yankin, ana zargin mutane 117 sun kamu da cutar.
“Daga cikin wannan adadi, mun riga mun samu mutane 15 da suka mutu, bisa bayanan da muke da su a yanzu,” in ji shi.
Wannan lamari ya faru ne kwanaki biyu kacal bayan da aka ruwaito cewa wata iyali a Jos ta rasa yara biyu, waɗanda shekarunsu suke tsakanin 12 zuwa 17, sakamakon zargin kamuwa da cutar.
Da yake bayyana yadda cutar ke yaɗuwa, Bulus ya ce cutar mashaƙo cuta ce da ƙwayoyin cuta ke haddasawa kuma tana iya yaɗuwa cikin sauri daga mutum zuwa mutum, musamman tsakanin mutanen da ke yawan kusantar juna.
Ya ce mutanen da suke amfani da kayayyakin mutum ɗaya, kamar kayan cin abinci da tawul, tare da wanda ya kamu da cutar suna cikin haɗarin kamuwa.
“Ana iya yada cutar mashaƙo daga mutum zuwa mutum. Tana yaɗuwa ne idan mutane suka yi kusanci da wanda ya kamu da cutar, kuma tana iya zama bala’i.
“Ga yaran da aka yi wa rigakafi, illar cutar na iya kasancewa ƙasa da tsanani kuma ba lallai ta kai ga mutuwa ba. Amma ga yaron da ba a yi wa cikakken rigakafi ba ko kuma bai kammala adadin alluran da ake buƙata ba, cutar na iya zama mai kisa,” in ji shi.
DSNO ya jaddada cewa cutar mashaƙo cuta ce da za a iya kare kai daga gare ta ta hanyar rigakafi, yana mai cewa yaran da suka karɓi adadin alluran rigakafin da aka ba da shawara suna da kariya mai kyau.
Ya buƙaci mazauna yankunan da abin ya shafa, musamman, da su kiyaye tsaftar jikinsu tare da gaggauta kai rahoton alamomin da ake zargin cutar ne zuwa cibiyoyin kiwon lafiyar gwamnati.
“Ya kamata mutane su kiyaye tsaftar kansu kuma su guji wuraren da cunkoso ya yi yawa. Muna shawartar mazauna yankin da su je cibiyar lafiya mafi kusa saboda gano cutar da wuri shi ne mabuɗin ceton rayuka.
“A mafi yawan lokuta, mutane suna zuwa wajen masu sayar da magani ko kuma su yi amfani da magunguna da kansu, abin da ba mu ba da shawara ba ne. Hanya mafi dacewa ita ce zuwa cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko, inda muke da kayan aiki da ma’aikatan da suka dace,” Bulus ya ƙara da cewa.
Ya ce an tura ma’aikatan lafiya daga ƙaramar hukumar zuwa al’ummomin da abin ya shafa domin ƙara sa ido kan cutar da kuma wayar da kan mazauna yankin kan matakan da za su taimaka wajen hana ƙarin yaɗuwar cutar.














