ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, July 15, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Cikin Shekaru 28, Kudiri Ƙasa Da 10 Sanatocin Zamfara Ta Arewa Suka Gabatar A Majalisa – Shinkafi

by Muhammad
2 months ago

Ɗan takarar kujerar Sanatan Zamfara ta Arewa a ƙarƙashin jam’iyyar APC, Dr. Sani Abdullahi Shinkafi, ya bayyana cewa wakilan yankin da suka yi sanata cikin shekaru 28 da suka gabata sun gabatar da ƙasa da kudirin dokoki 10 kacal.

Shinkafi ya bayyana hakan ne a Abuja jim kaɗan bayan ya miƙa fom ɗinsa na tsayawa takara, inda ya ce ya shiga takara ne domin ya gyara abin da ya kira ƙarancin wakilci da ya jefa yankin baya a fagen ci gaban ƙasa.

Ya ce daga shekarar 1999 zuwa yau, kujerar sanata ta Zamfara ta Arewa ta kasance tana karkata ne a hannun wasu yankuna, abin da ya sa wasu sassan yankin ke jin an ware su daga ci gaba da wakilci.

ADVERTISEMENT

A cewarsa, yankin ya ƙunshi ƙananan hukumomi huɗu, amma ba a ba su cikakken wakilci na gaskiya ba a Majalisar Dattawa, yana mai cewa hakan ya haifar da rashin adalci da rashin daidaito a siyasa.

Shinkafi ya kuma koka cewa duk da yawan shekarun da wakilan yankin suka shafe a majalisa, ba su kawo manyan ayyukan gwamnatin tarayya masu tasiri a yankin ba, musamman a fannin ilimi da ci gaban tattalin arziki.

LABARAI MASU NASABA

Tsohon Ɗan Takarar Gwamnan SDP A Gombe Ya Koma PDP, Ya Mara Wa Pantami Baya

Tsohon Sanatan Gombe, Bayero Nafada, Ya Fice Daga PDP Bayan Ganawa da Shugabannin APC

Ya bayyana cewa lokaci ya yi da za a kawo sauyi, yana mai cewa zai tsaya tsayin daka don ganin an samu sabon salo na wakilci a yankin Zamfara ta Arewa.

Dangane da batun tsarin zaɓen fidda gwani, Shinkafi ya ce bai yarda da tsarin sasanci ba, yana mai cewa zai tsaya ne kawai kan tsarin zaɓen fidda gwani kai tsaye kamar yadda doka ta tanada.

Ya ce dole ne a bai wa kowane ɗan takara dama ya fafata, yana mai cewa “duk wanda ya yi nasara shi ne zai wakilci jam’iyya.”

A wani ɓangare kuma, ɗan takarar Sanatan Ekiti ta Arewa, Senator Ayo Arise, ya bayyana cewa ya koma takara ne saboda kiran al’ummarsa, na burin ya ci gaba da aikin da ya fara a baya a Majalisar Dattawa.

Ya ce ya taimaka wajen samar da Jami’ar Tarayya ta Oye-Ekiti wadda ta taimaka wajen bunƙasa ilimi da ci gaban yankin, kuma yana son ƙara faɗaɗa irin wannan ci gaba idan aka sake zaɓensa.

Ya ƙara da cewa zai bar wa jama’a su yanke hukunci kan wanda ya fi cancanta ya wakilce su a Majalisar Dattawa a 2027.

Muhammad
+ postsBio
  • Muhammad
    2027: NNPP Ta Yi Wa Korarrun Mambobinta Afuwa, Ta Yi Alƙawarin Basu Tikitin Kai-tsaye
  • Muhammad
    Musulunci Na Fuskantar Barazana A Karƙashin Mulkin Tinubu — Datti Baba-Ahmed
  • Muhammad
    Kwankwaso Tamkar Tsuntsu Ne A Siyasa Da Yake Sauya Sheƙa Daga Nan Zuwa Can – Ganduje
  • Muhammad
    PDP Ta Tsayar Da Mustapha Sule Lamido A Matsayin Ɗan Takarar Gwamna Jigawa A 2027

MASU ALAKA

Tsohon Ɗan Takarar Gwamnan SDP A Gombe Ya Koma PDP, Ya Mara Wa Pantami Baya
Manyan Labarai

Tsohon Ɗan Takarar Gwamnan SDP A Gombe Ya Koma PDP, Ya Mara Wa Pantami Baya

July 15, 2026
Tsohon Sanatan Gombe, Bayero Nafada, Ya Fice Daga PDP Bayan Ganawa da Shugabannin APC
Manyan Labarai

Tsohon Sanatan Gombe, Bayero Nafada, Ya Fice Daga PDP Bayan Ganawa da Shugabannin APC

July 14, 2026
ADC Ta Nemi A Binciki Nafiu Bala Bayan INEC Ta Ƙaryata Iƙirarinsa
Siyasa

ADC Ta Nemi A Binciki Nafiu Bala Bayan INEC Ta Ƙaryata Iƙirarinsa

July 14, 2026
Next Post
Ikorodu City Ta Hau Matsayi Na Uku Bayan Doke Wikki Tourists Da Ci 3-1

Ikorodu City Ta Hau Matsayi Na Uku Bayan Doke Wikki Tourists Da Ci 3-1

LABARAI MASU NASABA

Majalisa Ta Ba da Tallafin ₦50m Ga Iyalan Malamai Da Jami’an Tsaro Da Aka Kashe A Aikin Ceto A Oyo

Majalisa Ta Ba da Tallafin ₦50m Ga Iyalan Malamai Da Jami’an Tsaro Da Aka Kashe A Aikin Ceto A Oyo

July 15, 2026
Xi Ya Bukaci A Mayar Da Hankali Kan Bukatun Jama’a Yayin Rangadin Da Ya Yi A Shanghai

Xi Ya Bukaci A Mayar Da Hankali Kan Bukatun Jama’a Yayin Rangadin Da Ya Yi A Shanghai

July 15, 2026
Katsina: Kotu Ta Yanke Wa Hauwa’u Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya Kan Taimaka Wa ’Yan Bindiga

Lalata Da Ƙaramar Yarinya: Kotu Ta Yanke Wa Tsoho Mai Shekara 75 Hukuncin Ɗaurin Shekara 10 A Ribas

July 15, 2026
Ci Gaban Fasaha Na Hidimtawa Jama’a Cikin Kowane Yanayi A Kasar Sin

Ci Gaban Fasaha Na Hidimtawa Jama’a Cikin Kowane Yanayi A Kasar Sin

July 15, 2026
‘Yan Bindiga Sun Sace Shugaban Makaranta, Jami’in NECO Da Ɗalibai A Kogi

‘Yan Bindiga Sun Sace Shugaban Makaranta, Jami’in NECO Da Ɗalibai A Kogi

July 15, 2026
Tsohon Ɗan Takarar Gwamnan SDP A Gombe Ya Koma PDP, Ya Mara Wa Pantami Baya

Tsohon Ɗan Takarar Gwamnan SDP A Gombe Ya Koma PDP, Ya Mara Wa Pantami Baya

July 15, 2026
Zazzaɓin Lassa: Mutum 31 Sun Kamu Da Cutar A Jihohi 4, Waɗanda Suka Rasu Sun Kai 221

Zazzaɓin Lassa: Mutum 31 Sun Kamu Da Cutar A Jihohi 4, Waɗanda Suka Rasu Sun Kai 221

July 15, 2026
‘Yansanda Sun Kama Shugaban PFIPC, Adeyemi

‘Yansanda Sun Kama Shugaban PFIPC, Adeyemi

July 15, 2026
‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga Da Kuɗin Fansa Naira Miliyan 5 A Delta

‘Yansanda Sun Kama Wani Kan Zargin Yi Wa ‘Yan Bindiga Safarar Makamai A Kano

July 15, 2026
Sakamakon Binciken Masana Na Kasar Da Ake Fitarwa Kyauta Yana Kara Jan Hankalin Duniya

Sakamakon Binciken Masana Na Kasar Da Ake Fitarwa Kyauta Yana Kara Jan Hankalin Duniya

July 14, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.