ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Friday, October 23, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

’Yan Bindiga Sun Ƙona Ofishin ’Yan Sanda A Abiya, Sun Kashe Jami’ai Biyu

by Muhammad
5 days ago

Wasu ’yan bindiga sun kai hari ofishin ’yan sanda na Uratta da ke birnin Aba, a Jihar Abia, inda suka kashe jami’an ’yan sanda biyu tare da jikkata wasu mutum uku.

Maharan sun kai harin ne da sanyin safiyar Asabar, inda suka yi amfani da abubuwan fashewa tare da cinna wa wasu sassan ofishin wuta.

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Abia, Wilfred Afolabi, ya tabbatar da mutuwar jami’an biyu, inda ya ce wasu mutum uku, ciki har da jami’an ’yan sanda biyu da farar hula guda, sun samu raunuka kuma ana kula da su a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jihar Abia da ke Aba.

ADVERTISEMENT

Afolabi ya bayyana hakan ne yayin da yake duba barnar da aka yi a ofishin tare da Gwamnan Jihar Abia, Alex Otti.

Ya ce har yanzu ba a kama wani da ake zargi da hannu a harin ba, amma rundunar ’yan sandan ta fara ƙoƙarin gano waɗanda suka aikata laifin domin gurfanar da su a gaban shari’a.

LABARAI MASU NASABA

NUJ Ta Gargadi ‘Yan Jarida Kan Yaɗa Rahotannin Da Ba Su Da Inganci Kan Cire Limami Kan Tallata Tinubu A Bauchi

Ma’aikatan Lafiya Sun Fara Shirin Tsunduma Yajin Aiki Kan Bashin Alawus Na Wata 19

Kwamishinan ya ce, “Na isa wurin da misalin ƙarfe 4 na asuba, kuma abin da ya fi muhimmanci shi ne kamo waɗanda suka aikata laifin. Abin da muke yi ke nan.”

Ya ƙara da cewa rundunar za ta yi duk mai yiwuwa wajen tabbatar da an kama maharan, ko da sun yi ƙoƙarin ɓuya.

An Ƙona Motar ’Yan Sanda, An Lalata Wasu Kayan Aiki

Rahotanni sun nuna cewa maharan sun ƙona motar sintiri ta ’yan sanda tare da lalata wasu motoci da janareta da sauran kayayyakin da ke cikin ofishin.

Wata majiya da ta san yadda lamarin ya faru, wadda ta nemi a sakaya sunanta saboda ba ta da izinin yin magana da manema labarai, ta ce maharan sun yi kama da waɗanda suka kai hari da nufin kwashe makaman da ke cikin ma’ajiyar makamai ta ofishin.

Sai dai majiyar ta yi iƙirarin cewa maharan sun tarar da ma’ajiyar babu makamai. Ta kuma yi zargin cewa sun kwashe wasu kayan uniform na ’yan sanda.

Majiyar ta ƙara da cewa an harbi ɗaya daga cikin maharan, amma abokan tafiyarsa sun tafi da shi.

Sai dai rundunar ’yan sandan jihar ta bayyana cewa babu makamai ko alburusai da aka kwashe daga ofishin yayin harin.

Gwamna Otti Ya Ziyarci Waɗanda Suka Jikkata

Bayan kai harin, Gwamna Alex Otti ya ziyarci waɗanda suka jikkata a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jihar Abia da ke Aba domin duba lafiyarsu.

Gwamnan ya kuma duba barnar da aka yi a ofishin ’yan sandan, yayin da jami’an tsaro suka fara gudanar da bincike domin gano waɗanda suka kai harin.

Rundunar ’yan sandan ta ce an shawo kan lamarin tare da dawo da zaman lafiya a yankin, yayin da ake ƙara tsaurara matakan tsaro da sa ido domin kama waɗanda suka aikata laifin.

Kwamishinan ’yan sandan ya yi Allah-wadai da harin, tare da miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan jami’an da suka rasa rayukansu da kuma rundunar ’yan sandan ƙasar baki ɗaya.

Ya kuma yi kira ga mazauna yankin da su kwantar da hankalinsu, su kasance masu sanya ido, tare da taimaka wa jami’an tsaro da bayanan da za su taimaka wajen gudanar da bincike.

Ba Wannan Ne Karon Farko Da Aka Kai Hari Ofishin Ba

Rahotanni sun nuna cewa an taɓa kai hari ofishin ’yan sandan na Uratta a ranar 23 ga Fabrairu, 2021.

A wancan lokacin, maharan sun kashe wani sajena na ’yan sanda mai suna Okezie tare da ƙona motar sintirin ’yan sandan da gwamnatin jihar ta bayar.

Sabon harin ya sake jawo hankalin jama’a kan matsalar tsaro da kuma buƙatar ƙarfafa kariya ga jami’an tsaro da wuraren aikinsu.

Ya zuwa lokacin da aka fitar da rahoton, rundunar ’yan sandan ba ta sanar da kama wani da ake zargi da hannu a harin na baya-bayan nan ba.

Muhammad
+ postsBio
  • Muhammad
    2027: Matawalle Ya Bai Wa ’Yan Majalisar Zamfara Takwas Motocin Alfarma Kirar SUV
  • Muhammad
    UTME: Ɗalibai 108 Daga 39,000 ’Yan Ƙasa Da Shekaru 16 Ne Suka Cika Sharuddan Shiga Jami’a
  • Muhammad
    ’Yan Sanda Sun Kama ’Yan Ƙungiyoyin Asiri Takwas da Masu Damfarar ATM Uku A Kogi
  • Muhammad
    Majalisar Dokokin Kano Ta Dakatar Da Ɗan Majalisa Na Watanni 3 Kan Fitar Bidiyon Jan Kunnen Zomo

MASU ALAKA

NUJ Ta Gargadi ‘Yan Jarida Kan Yaɗa Rahotannin Da Ba Su Da Inganci Kan Cire Limami Kan Tallata Tinubu A Bauchi
Labarai

NUJ Ta Gargadi ‘Yan Jarida Kan Yaɗa Rahotannin Da Ba Su Da Inganci Kan Cire Limami Kan Tallata Tinubu A Bauchi

October 23, 2026
Ma’aikatan Lafiya Sun Fara Shirin Tsunduma Yajin Aiki Kan Bashin Alawus Na Wata 19
Labarai

Ma’aikatan Lafiya Sun Fara Shirin Tsunduma Yajin Aiki Kan Bashin Alawus Na Wata 19

October 23, 2026
NLC Ta Gabatar Da Buƙatu 6 Tare Da Barazanar Yajin Aiki A Nijeriya Baki Ɗaya
Labarai

NLC Ta Gabatar Da Buƙatu 6 Tare Da Barazanar Yajin Aiki A Nijeriya Baki Ɗaya

October 23, 2026
Next Post

‘Ba Za Mu Janye Wa Atiku Ba’ - Kwankwaso Ya Mayar Wa ADC Martani

LABARAI MASU NASABA

Xi Jinping Ya Umarci Yin Bakin Kokari Wajen Ceto Mutanen Da Girgizar Kasa Mai Karfin Maki 7.0 Ta Rutsa Da Su A Xizang

Xi Jinping Ya Umarci Yin Bakin Kokari Wajen Ceto Mutanen Da Girgizar Kasa Mai Karfin Maki 7.0 Ta Rutsa Da Su A Xizang

October 23, 2026
Binciken CGTN: Daga Samar Da Tsare-tsare Zuwa Aiwatarwa Tsarin Jagorancin Duniya Na Bukatar Karin Dabaru Na Hakika

Binciken CGTN: Daga Samar Da Tsare-tsare Zuwa Aiwatarwa Tsarin Jagorancin Duniya Na Bukatar Karin Dabaru Na Hakika

October 23, 2026
NUJ Ta Gargadi ‘Yan Jarida Kan Yaɗa Rahotannin Da Ba Su Da Inganci Kan Cire Limami Kan Tallata Tinubu A Bauchi

NUJ Ta Gargadi ‘Yan Jarida Kan Yaɗa Rahotannin Da Ba Su Da Inganci Kan Cire Limami Kan Tallata Tinubu A Bauchi

October 23, 2026
Ma’aikatan Lafiya Sun Fara Shirin Tsunduma Yajin Aiki Kan Bashin Alawus Na Wata 19

Ma’aikatan Lafiya Sun Fara Shirin Tsunduma Yajin Aiki Kan Bashin Alawus Na Wata 19

October 23, 2026
Cikakke Kuma Tsattsauran Jagoranci A Kanta Dabarar JKS Ce Ta Gina Kanta

Cikakke Kuma Tsattsauran Jagoranci A Kanta Dabarar JKS Ce Ta Gina Kanta

October 23, 2026
Shugaba Xi Ya Aike Da Sako Ga Dandalin Xiongan Na 2026

Shugaba Xi Ya Aike Da Sako Ga Dandalin Xiongan Na 2026

October 23, 2026
Real Madrid Na Tattaunawa Da Bellingham Don Tsawaita Kwantiraginsa

Real Madrid Na Tattaunawa Da Bellingham Don Tsawaita Kwantiraginsa

October 23, 2026
MOC: Manufofin Bunkasa Amfani Da Kayayyaki Sun Fadada Kasuwar Cinikayyar Kayayyaki A Kai A Kai A Farkon Watanni 9 Na Bana

MOC: Manufofin Bunkasa Amfani Da Kayayyaki Sun Fadada Kasuwar Cinikayyar Kayayyaki A Kai A Kai A Farkon Watanni 9 Na Bana

October 23, 2026
NLC Ta Gabatar Da Buƙatu 6 Tare Da Barazanar Yajin Aiki A Nijeriya Baki Ɗaya

NLC Ta Gabatar Da Buƙatu 6 Tare Da Barazanar Yajin Aiki A Nijeriya Baki Ɗaya

October 23, 2026
Sin: Dole Ne Gyaran Kwamitin Sulhu Ya Kunshi Canza Karfin Wakilcin Kasashe Masu Wadata Fiye Da Kima

Sin: Dole Ne Gyaran Kwamitin Sulhu Ya Kunshi Canza Karfin Wakilcin Kasashe Masu Wadata Fiye Da Kima

October 23, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.