Ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa a ƙarƙashin Jam’iyyar NDC, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi watsi da jita-jitar da ke yawo cewa tikitin takararsu zai iya maja a babban zaɓen 2027 domin marawa ɗan takarar Jam’iyyar ADC, Alhaji Atiku Abubakar, baya.
Kwankwaso, wanda ke takara tare da ɗan takarar shugaban ƙasa na NDC Peter Obi, ya kuma zargi Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na ADC (ADC-PCC) da kaddamar da hare-haren siyasa marasa tushe a kansu da jam’iyyarsu.
A cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na dandalin sada zumunta na X a ranar Lahadi, Kwankwaso ya jaddada cewa tikitin takarar Obi da Kwankwaso (OK Ticket) na nan daram kan aniyarsa ta fafatawa a zaɓen shugaban ƙasa mai zuwa. Ya bayyana ƙiri-ƙiri cewa: “Bari in fayyace wannan batu a sarari ba tare da wata shakka ba: ba za mu janye takararmu domin ADC ko wata jam’iyya ba; muna da cikakken kwarin gwiwa kan ƙwarewarmu, da cancantarmu, da shirye-shiryenmu na jagorantar Nijeriya zuwa ga tudun-mun-tsira.”
Tsohon Gwamnan na Jihar Kano ya zargi shugabannin kamfen ɗin ADC da mayar da hankali wajen ƙulla maƙarƙashiya maimakon bayyana cancanta da kyakkyawan tsarin ɗan takararsu ga ƴan ƙasa. Ya yi nuni da cewa ADC na ƙoƙarin yaɗa farfagandar cewa tikitin NDC na aiki ne a madadin Jam’iyyar APC mai mulki ko kuma zai janye a minti na ƙarshe, yana mai gargaɗin magoya bayansu da su yi watsi da wannan ƙanzon-kurege da ke da nufin ruɗar da masu kaɗa ƙuri’a a jajiberin zaɓe.
Haka kuma, Kwankwaso ya ƙalubalanci kwamitin yaƙin neman zaɓen na ADC da ya mayar da hankali wajen amsa zarge-zargen da Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya yi wa Atiku Abubakar, maimakon ɓata lokaci wajen kai hare-hare a kan shi da Peter Obi. Ya ci gaba da caccakar gwamnati mai ci, inda ya bayyana cewa gwamnatin APC ta gaza wajen biya wa ƴan Nijeriya buƙatunsu, yayin da a gefe guda kuma jam’iyyar ADC ba ta da wani sabon tsari ko ingantacciyar mafita da za ta kawo wa ƙasar ci gaba.
A ƙarshe, Kwankwaso ya bayyana tikitin Obi da Kwankwaso a matsayin sahihiyar mafita ga ƴan Nijeriya, sakamakon ƙwarewarsu da kuma ɗimbin goyon bayan da suke da shi a sassan Arewaci da Kudancin Nijeriya domin haɗa kan al’umma.
Ya jaddada cewa Jam’iyyar NDC ce babbar jam’iyyar adawa mafi ƙarfi da kwarjini a ƙasar a halin yanzu da za ta iya magance ƙalubalen rashin tsaro, taɓarɓarewar ilimi, fannin noma, da tattalin arziƙi, tare da yin kira ga magoya bayansu da su ci gaba da jajircewa domin samun gagarumar nasara a zaɓen 2027.













