‘Yan bindiga sun kashe mutane biyu tare da jikkata wani mutum a wasu hare-hare da aka kai wa al’ummomin Berom a Jihar Filato.
Hare-haren sun faru ne a daren ranar Talata a Gwa-Wereng Rim, Kyeng da ke gundumar Bachi, Dorong da kuma Jol.
Ƙungiyar Berom Youth Moulders Association (BYM) ta ce an kashe Bulus Mwagwong, wanda aka fi sani da Dikko, a harin Gwa-Wereng Rim da misalin ƙarfe 9:30 na dare.
Ɗan uwansa, Yakubu, shi ma ya samu munanan raunuka.
A ƙauyen Kyeng kuma, an kashe Stephen Dachollom Kaze mai shekaru 47 da misalin ƙarfe 8:30 na dare.
A Dorong, ‘yan bindigar sun ƙone wasu gidaje, lamarin da ya tilasta mazauna yankin tserewa.
A Jol kuwa, sun yi musayar wuta da ‘yan sa-kai.
BYM ta yi Allah-wadai da hare-haren tare da yin kira ga jami’an tsaro da su ƙara yawan jami’ai a yankunan da ke fuskantar matsalolin tsaro tare da kama waɗanda suka aikata laifin.
Ƙungiyar ta kuma roƙi Gwamnatin Jihar da ta taimaka wa iyalan waɗanda aka kashe da kuma mutanen da suka rasa gidaje da dukiyoyinsu.














