ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Karya Fure Take Ba Ta ‘Ya’ya: Mene Ne Ainihin Yanayin Kasar Sin?

by Sulaiman and CGTN Hausa
4 weeks ago
Karya

Kwanan nan, babban dan kasuwar Amurka, kana babban darektan kamfanin kera motocin lantarki na Tesla, Mr. Elon Musk, ya bayyana ta shafin sada zumunta na X cewa: “Sin tana da kyau sosai, ina matukar karfafa gwiwar kowa da kowa ya je ya gani.” Daga baya, mahaifiyarsa, Maye Musk, ta sake buga rubutunsa tare da cewa: “Kowane birni na Sin yana da nasa yanayin da ke janyo hankulan masu ziyara, akwai wuraren al’adu daban-daban da za a ziyarta. Gine-gine da tituna suna da tsafta, ana kula da su sosai. Mutane sun kasance masu ladabi da jajircewa, kuma suna mutunta juna.” Ta kuma jaddada: “Akwai tsaro a kasar, don haka ina jin dadin zuwa Sin.”

Lallai, kalaman na Musk da na mahaifiyarsa sun dace da wasu kalmomi masu alaka da kasar Sin da yanzu haka ke jan hankalin masu ziyartar shafukan sada zumunta na kasa da kasa, ciki har da “China Travel” da “China Cool”. A cikin ’yan shekarun nan, yayin da kasar Sin ke gaggauta inganta bude kofarta ga ketare, yawon shakatawa a kasar Sin na kara samun farin jini a fadin duniya. Alkaluman da aka samar sun shaida cewa, a farkon rabin shekarar bana, adadin baki da suka shigo Sin ya kai sama da miliyan 22 da dubu 910, adadin da ya karu da kashi 20.4% idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata, daga cikinsu kuma, yawan wadanda suka shigo ba tare da biza ba ya kai kashi 77.7%. Musamman ma a yayin da kasashe da dama ke fama da matsanancin zafi a bana, karin baki masu yawon bude ido na zuwa Sin, inda suke jin dadin yanayi a wasu sassa masu albarkatun sanyi da kuma na’urorin sanyaya daki da ake yawan samu a kasar, a sa’i daya kuma, fasahohin zamani da suka gani a kasar, irinsu jirgin kasa mai saurin gudu da biyan kudi ta wayar salula da mutum-mutumin inji da jirage marasa matuka sun burge su matuka.

Daga cikin bakin, akwai dan kasar Afirka ta Tsakiya mai suna Aime, yayin da yake ziyartar birnin Beijing, ya yi mamakin ganin mutum-mutumin inji masu siffofin dan adam da ke iya yin kofi da wasanni, kuma ya ce: “Fasahohin zamani na Sin, musamman na Beijing, suna da kayatarwa.” A Shenzhen da ke kudancin kasar Sin kuma, motoci marasa direba na Pony.ai suna zirga-zirga a sassan birnin, wadanda suka burge baki da yawa da suka zo birnin, har suka dauki “hawan mota mara direba” a matsayin abin da dole su gwada a birnin. A wuraren shakatawa, baki da yawa sun kuma gwada hidimomin isar da kaya ta jirage marasa matuka, fuskokinsu na cike da mamaki da farin ciki. Akwai kuma wasu masu shirya bidiyo da suka zo kasar Sin yawon shakatawa, wadanda suka dauki fita da dare a matsayin gwada “kasada”, amma sai suka gano cewa yanayin tsaro na Sin yana ba mace damar fita ita kadai ba tare da damuwa ba. Sai kuma wata mai shirya shirin bidiyo mai suna Josie ‘yar kasar Australiya, bayan da ta yi yawon bude ido a kasar Sin, ta gano cewa, a baya, ba ta san kasar Sin sosai ba, kuma masaniyarta game da kasar Sin bisa ga wasu rahotannin da aka samar a baya ba ta gaskiya ba ce.

ADVERTISEMENT

A hakika, jama’ar kasashen waje sun dade suna fahimtar kasar Sin bisa labarai da rahotanni da ba su dace ba da kafofin watsa labarai na kasashen yamma suka samar bisa son zuciyarsu, wadanda suka haifar da rashin fahimta da bahaguwar fahimta a kan ainihin yanayin kasar Sin. Duk da haka, karin baki na zuwa kasar Sin, inda suka gani da idonsu yadda kasar ta kasance, kana suka ga tituna masu tsaro har a cikin dare, da saukin rayuwa wadda kusan wayar salula ke iya biyan kusan dukkan bukatunka ta fannonin riguna da abinci da gidan kwana da kuma zirga-zirga, da yadda ake samar da na’urorin sanyaya daki a wuraren taruwar jama’a da kuma isasshiyar wutar lantarki, da kuma hadewar al’adun gargajiya da fasahohin zamani, kuma dukkan wadannan suka taimaka wa bakin gyara fahimtarsu da ba ta dace ba game da kasar Sin.

A daidai lokacin da Mr. Musk ya ba da shawarar ziyartar Sin, ofishin jakadancin kasar Amurka a kasar Sin ya sake fitar da abin da ake kira “gargadin balaguro zuwa Sin,” yana yada jita-jita marasa tushe kamar “rashin kwanciyar hankali a Sin, hadarin tafiya, da kama baki ba bisa ka’ida ba.”, gargadin da suke fitarwa a-kai-a-kai.

LABARAI MASU NASABA

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta

Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin

Amma kamar yadda Bahaushe kan ce, “karya fure take ba ta ‘ya’ya.” To shin mene ne ainihin yanayin kasar Sin? Sassaukar amsa ita ce gani ya kori ji, ma’ana abin sai wanda ya gani.

Bana ita ce shekarar cudanyar al’umma da musayar al’adu tsakanin Sin da Afirka, kuma tuni kasar Sin ta sanya hannu kan yarjejeniyoyin hadin gwiwar yawon shakatawa da kasashen Afirka sama da 30. Gani ya kori ji, muna fatan ‘yan uwanmu na kasashen Afirka ku yi amfani da wannan dama ku zo ku gani da idonku yadda Sin ta kasance. A nan kasar, akwai babbar ganuwa mai dadadden tarihi, akwai jirgin kasa mai saurin gudu. Kasa ce mai tsawon tarihi, kuma kasa ce da ke rungumar makomar ci gaban zamani, don haka, mene ne ainihin yanayin Sin? Jama’a, muna jiran amsoshinku.

Karya
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • Sulaiman
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • Sulaiman
    ‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna
  • Sulaiman
    Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi
Karya
CGTN Hausa
+ posts Bio
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

MASU ALAKA

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta
Ra'ayi Riga

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta

September 8, 2026
Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin
Ra'ayi Riga

Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin

September 4, 2026
Samun Rarar Kudin Ciniki Ba “Laifi” Ba Ne, Hadin Gwiwa Da Cin Moriya Tare Ita Ce Mafita Ga Kowa
Ra'ayi Riga

Samun Rarar Kudin Ciniki Ba “Laifi” Ba Ne, Hadin Gwiwa Da Cin Moriya Tare Ita Ce Mafita Ga Kowa

September 2, 2026
Next Post
Za A Yi Taron Dandalin Hadin Gwiwar Kafofin Watsa Labarai Na Sin Da Afirka Karo Na 7

Za A Yi Taron Dandalin Hadin Gwiwar Kafofin Watsa Labarai Na Sin Da Afirka Karo Na 7

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.