ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Friday, October 23, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

’Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 22, Ciki Har Da Sojoji 4, Sun Ƙaƙaba Harajin ₦50m A Zamfara

by Sulaiman
2 weeks ago
Zamfara

Aƙalla mutane 22, ciki har da sojoji huɗu, ne aka kashe bayan ’yan bindiga sun yi wa wasu mutane kwanton ɓauna a hanyar Gwashi zuwa Nasarawa, a Ƙaramar Hukumar Bukkuyum ta Jihar Zamfara. Haka kuma, mazauna ƙauyuka uku a yankin Dansadau sun tsere daga matsugunansu sakamakon wasu hare-hare daban-daban.

Rahotanni sun ce maharan sun kuma ƙaƙaba wa al’ummomin yankin Dansadau harajin naira miliyan 50, bayan sun ƙona motoci 12 tare da fatattakar mazauna ƙauyuka uku.

Ɗan Majalisar Dokokin Jihar Zamfara mai wakiltar Bukkuyum, Hon. Hamisu Faru, ya tabbatar da faruwar harin, inda ya ce an kai wa waɗanda abin ya shafa hari ne ranar Lahadi, lokacin da sojojin ke bakin aiki a yankin.

ADVERTISEMENT

Ya ce har zuwa lokacin da ake haɗa wannan rahoto, ba a gano gawarwakin wasu daga cikin waɗanda aka kashe ba.

Jami’in Yaɗa Labarai na ‘Operation Fansan Yamma’, Laftanar Kanal Aliyu Danja, shi ma ya tabbatar wa jaridar LEADERSHIP da mutuwar sojojin a wata tattaunawa ta musamman da aka yi da shi a safiyar Litinin.

LABARAI MASU NASABA

Jama’ar Gari Sun Kashe ’Yan Bindiga Sama Da 30 A Wani Gumurzu A Zamfara

Yaƙin Neman Zaɓe: ’Yansanda Sun Hana Manyan Motoci Shiga Kaduna Gabanin Ziyarar Tinubu

A wani harin daban da aka kai a yankin Dansadau, rahotanni sun ce fiye da mazauna yankin 300 ne suka rasa matsugunansu bayan ’yan bindiga sun kai hare-hare kan ƙauyuka uku, sun ƙona motoci 12 tare da kakaba wa al’ummomin harajin ₦50m.

A wani ɓangare kuma, reshen jam’iyyar NDC na Jihar Zamfara ya yi Allah-wadai da hare-haren, yana mai bayyana cewa matsalar tsaro a jihar na ƙara taɓarɓarewa.

A cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Lahadi, wadda Sakataren Yaɗa Labarai na jam’iyyar, Kassim Almustapha Kayatawa, ya sanya wa hannu, jam’iyyar ta jajantawa iyalan waɗanda suka mutu, ciki har da sojojin da suka rasa rayukansu.

Zamfara
Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Gwamna Dauda Lawal Ya Rantsar Da Manyan Sakatarori Biyar
  • Sulaiman
    Ministan Harkokin Wajen Sin Ya Gana Da Takwaransa Na Djibouti
  • Sulaiman
    Ta Yaya Ake Ci Gaba Da Fitar Da Sabbin Kayayyaki A Yayin Baje Koli Na Canton Fair
  • Sulaiman
    Darasi Daga Zuhudun Manzon Allah (SAW)

MASU ALAKA

Jama’ar Gari Sun Kashe ’Yan Bindiga Sama Da 30 A Wani Gumurzu A Zamfara
Manyan Labarai

Jama’ar Gari Sun Kashe ’Yan Bindiga Sama Da 30 A Wani Gumurzu A Zamfara

October 23, 2026
Yaƙin Neman Zaɓe: ’Yansanda Sun Hana Manyan Motoci Shiga Kaduna Gabanin Ziyarar Tinubu
Manyan Labarai

Yaƙin Neman Zaɓe: ’Yansanda Sun Hana Manyan Motoci Shiga Kaduna Gabanin Ziyarar Tinubu

October 23, 2026
Sanata Abdul’aziz Yari Ya Ziyarci Sarkin Zazzau
Manyan Labarai

Sanata Abdul’aziz Yari Ya Ziyarci Sarkin Zazzau

October 23, 2026
Next Post
Tufka Da Warwarar INEC Kan Yiwuwar Zaben 2023

INEC Ta Ce Sanarwar Da Ake Yaɗawa Kan ’Yan Takarar Gwamnoni Kano Da Gombe Da Sauran Jihohi 3 Ƙarya Ce

LABARAI MASU NASABA

Real Madrid Na Tattaunawa Da Bellingham Don Tsawaita Kwantiraginsa

Real Madrid Na Tattaunawa Da Bellingham Don Tsawaita Kwantiraginsa

October 23, 2026
NLC Ta Gabatar Da Buƙatu 6 Tare Da Barazanar Yajin Aiki A Nijeriya Baki Ɗaya

NLC Ta Gabatar Da Buƙatu 6 Tare Da Barazanar Yajin Aiki A Nijeriya Baki Ɗaya

October 23, 2026
Jama’ar Gari Sun Kashe ’Yan Bindiga Sama Da 30 A Wani Gumurzu A Zamfara

Jama’ar Gari Sun Kashe ’Yan Bindiga Sama Da 30 A Wani Gumurzu A Zamfara

October 23, 2026
Sin Da Afirka Abokan Tafiya Ne Wajen Inganta Tsarin Jagorancin Duniya

Sin Da Afirka Abokan Tafiya Ne Wajen Inganta Tsarin Jagorancin Duniya

October 23, 2026

Shugabar Jaridar LEADERSHIP Ta Halarci Bikin Aza Harsashin Cibiyar Ƙirƙire-Ƙirƙire Tare Da Remi Tinubu A Abuja

October 23, 2026
Yaƙin Neman Zaɓe: ’Yansanda Sun Hana Manyan Motoci Shiga Kaduna Gabanin Ziyarar Tinubu

Yaƙin Neman Zaɓe: ’Yansanda Sun Hana Manyan Motoci Shiga Kaduna Gabanin Ziyarar Tinubu

October 23, 2026
An Kai Hare-Haren Makamai Masu Linzami Birnin Riyadh

An Kai Hare-Haren Makamai Masu Linzami Birnin Riyadh

October 23, 2026
Kakakin Majalisar Nasarawa Ya Raba Naira Miliyan 6 da Atamfofi 1,100 a Taron APC

Kakakin Majalisar Nasarawa Ya Raba Naira Miliyan 6 da Atamfofi 1,100 a Taron APC

October 23, 2026
Kamfanin Simintin Dangote Ya Ware Miliyoyi Don Tallafawa Karatun Al’ummar Gboko

Kamfanin Simintin Dangote Ya Ware Miliyoyi Don Tallafawa Karatun Al’ummar Gboko

October 23, 2026
Sanata Abdul’aziz Yari Ya Ziyarci Sarkin Zazzau

Sanata Abdul’aziz Yari Ya Ziyarci Sarkin Zazzau

October 23, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.